Chapter 12
Chapter 12
dama ma za su iya yin wata guda cur ba tare da an yi musu wankin ba don suna da wadatar suturar. Don haka ki tashi ki bar ƙofan gidan nan tun kafin na sauya miki halittan fuskanki". Na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo"don Allah a taimaka mini wallahi ina tsananin buƙatar aikin ne, ka ba ni dama na shiga na ga matar gidan wataƙila ba za a rasa wani aikin da za a maƙala ni a gurbin ba....". Kafin na rufe bakina na ji an ɗauke ni da wani gigitaccen mari sai da na zame na yi zaman dirshan a ƙasa sakamakon zafin da ya ratsa har cikin kwanyanta. "Yau na ga masifa ni Ahmadu. Za ki tashi ki bar nan wajen ko sai na shiga ciki na sincu miki karnuka na fito da su sun yayyaga ki". Yana rufe bakinsa na yi zumbur na yi miƙe jikina har yana rawa na bar wajen ban ƙara waiwayowa ba don daga yanayin furucinsa na tabbatar da cewar zai iya aikata duk abin da ya furta. Sai da na yi nisa na nema wani dakali na zauna ina mayar da numfashi. Na zabga tagumi da hannunwa bibbiyu tare da faɗa wa cikin kogin tunani, na daɗe zaune a wajen har rana ya iso inda nake ya soma duka na amma hakan bai sa na gusa daga wajen ba, sai da na ji jikina ya soma fitar da zuffa na gumi kafin na tashi na soma tafiya akan shimfiɗaɗɗan titin da yake wajen ya miƙe ɗoɗar, ina tafiya ina haɗa hanya tamkar ƴar maye ban yi aune ba na ji wani abu ya doke ni har sai da na faɗi a kan titin kaina ya bugu da ƙasa. Na runtse idanuna cikin wani irin mawuyacin hali na runtse idanuna. Dishi-dishi idanuna suke gano mini wata mace cikin shiga na alfarma a tsaya a kaina tana ta jeranta mini sannunku wani na bin wani sai dai na kasa amsa mata.Ta taimaka mini na tashi na zauna. "Baiwar Allah sannu. Ki na ji na kuwa?". Na yi ƙarfin halin gyaɗa kaina da hakan ya ba ta damar cewa"tashi mu je asibiti a duba ki". Take na watsake na buɗe idanuna tar na ce"a'a lafiyana ƙalau ba sai mun je wani asibiti ba". Na ƙare zancen ina ƙoƙarin tashi tsaye ta riƙe ni"ki koma ki zauna kin bugu fa". "Ban fa ji wani rauni ba zan iya tafiya. Don Allah ki bar ni na tafi ina da abin da ya fi zuwa asibitin nan muhimmanci". Na ƙare zancen cikin raunin da yake fitowa kai tsaye daga ƙasan ƙalbina. Na ɓaɓɓare hannunta daga jikina na soma tafiyata ko sauraron abin da take faɗa ban yi ba. Na ɗan yi nisa da tafiyan ina jan ƙafata da ƙyar saboda buguwan da na yi a gwiwan ƙafan. Na ji ana danna horn a bayana na matsa na yi gefe motan ya sha gabana, aka buɗe aka fito matar da ta buge ni ne ta fito, ina ganin ita ce na ƙara sauri cikin jan ƙafa zan bar wajen ta sha gabana tare da cafko hannuna ta riƙe tamau. "Baiwar Allah me yasa kike wasa da lafiyarki ne? Shin ba ki lura da yadda kike jan ƙafarki ba ne? Me yasa ba ki bari mu je asibiti a duba lafiyarki ba ko so kike yi wani abun ya same ki ina zaman zamana bakina alaikum ki ja min bala'i". "In dai don ta ni ne babu wani wanda zai zo ya same ki da batuna balle har a neme ki idan wani abu ya same ni sanadin hakan, don haka ki kwantar da hankali ba ni da kowa a garin nan". Ta yi sakeke tana kallo na ganin yadda na ƙare. "Ko ma mene ne ki bar ni na sauƙe wannan nauyin da ya rataya a wuyana, na kai ki asibiti a duba lafiyarki sannan na kai ki har gida". "Idan kika yi hakan za ki bar ni na yi tafiyata?". Ta gyaɗa mini kanta cikin tabbatar mini da abin da ta furta ta ce"in sha Allah". "Shikenan". Na furta a taƙaice ina juya wa na shiga motar ita ta zagayo ta shiga tare da figi motar muka bar wajen tun da muka fara tafiyar ban ce da ita uffan ba har muka isa asibiti. Ta lashe motar muka fito muka shiga ciki aka duba ni tare da yi mini dressing ɗin inda na kurkurje a gwiwana aka ba n wasu magunguna muka fito, sai da muka shiga cikin motar kana ta kallo ni ta furta"zan ɗan biya na yi siyayya ina mai ba ki haƙuri, na san zan ɓata miki lokaci amma ki yi haƙuri". Kaina kawai na gyaɗa mata kafin na ce"ba komai"? Ta ja motar muka bar cikin asibitin a bakin wani ƙaton shago ta tsaya da ake ta hada-hada a ƙofan shagon. Sai yanzu na yarda cewar garin jarafi babban gari ne na bugawa a jarida wanda ganinsa ya zarce jin sa. "Bari na shiga yanzu na fito". Kaina kawai na jinjina mata da hakan ya ba ta damar fita daga cikin motar ta fita, na zuba idanuna ta tagan ƙofan motan ina ƙarewa mutanen da suke wucewa kallo. Jin an buɗo ƙofar an shigo an zauna shi ya dawo da ni cikin hayyacina. Muka haɗa ido da ita ta sakar mini da murmushi ba tare da ta ce da ni komai ba. Sai da muka fara tafiya kafin ta kallo ni ta ce"ina muka nufa ne, ina ne gidanku?". Na rusunar da idanuna ƙasa kafin na ce"ki sauƙe ni a duk inda titin ya tsaya". "Ban gane ba?". "Ba za ki gane ba ko na yi miki bayani". "Kin yi min bayanin ta ko ya ya ne zan fahimce ki. Me yasa kika gararamba a kan titi a irin wannan shekarun nakin da ya dace a ce ki na makaranta ko kuma wajen koyan sana'ar da za ki dogara da kanki". Na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya kafin na ba ta amsa da faɗin"aiki na fito nema". "Wani irin kike nema?". "Ko wani irin aikin ƙarfi inna samu zan yi sa. Ko wankau ko raino". Ta ɗan yi shuru na wasu daƙiƙu kafin ta ce"za ki yi aikin cikin gidan kamar su shara, mopping da girki?". Na cije leɓena kana na ce"zan yi idan na samu sai dai an ce da ni samun irin wannan aikin da wuya don gidajen da suke da halin ɗaukar mai aiki yanzu Abuja suke zuwa su je kamfani a kawo musu duk kalar wacce suke so su zaɓa. Ba sa ɗaukar ya ku bayi irin mu". Ta saki dariya mai ƙarfi daidai lokacin da take karya kwana ta ce"waye ya gaya miki hakan? Tabbas akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu da suke da rajista da gwamnati da suke samowa mutane masu aiki, sai dai ba kowa ba ne yake da irin wannan ƙa'idar. Idan za ki iya yin aikin da na lissafa zan ɗauke ki aiki a gidana". Babu shiri na ɗago ido ina kallon ta"ranki ya daɗe don Allah da gaske kike wannan zancen?". "Me ye zai hana na yi miki wasa akan abin da na san kin ɗauke sa da muhimmanci. Da gaske na ke yi zan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98