Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sakat na yi faɗan na yi faɗan ba ta daina ba, har sai da na daina kula ta na daina yi magana na kusa a ƙalla wata guda kafin ta dawo cikin taitayinta, tun daga lokacin na fahimci Umma zuma ce dole a da wuta za a mu'amalance ta". Zan yi magana ta ɗaga mini hannu"mu bar wannan maganan, yanzu dai ba ni labarin ranar ki ta farko a wajen aiki, ya abin ya kasance?". Na ja numfashi mai nisan zango kana na fesar kafin na sama damar kwashe komai da ya faru na faɗa ba. Ta yi ɗan jim kafin can ta ce"ke kuma bayan faruwan hakan wani hukunci kika yanke?". "Wallahi na ji gabaɗaya aikin ya fita daga raina. Duk da ina son aikin amma ba na jin zan iya jure cin zarafi da wulaƙanci". Ta riƙo hannuna ta sanya cikin nata kafin ta soma magana cikin sigar ƙarfafa gwiwa. "Amatullah ki riƙe aikin nan ƙam. Kar ki bar damuwar wasu a cikin ranki. Ita ma wacce kike ba ni labarin ai ƴar aiki ce matsayinku ɗaya da ita don haka shafawa idanunki toka za ki yi ki karta mata rashin mutunci na rai da motsi, tun da daman an ce idan babba bai ji kunyar hawa jaki ba to jaki ba zai ji kunyar jefar da shi ba. Zake wa za ki yi ki ƙwaci ƴancin kanki da kanki kar ki yarda wata ƴar aiki da kuke matsayi ɗaya da ita ta taka ki". Na furzar da zazzafan iska daga bakina kafin na sama zarafin cewa"to ya ya kike so na yi? Shin kin san adadin shekarun da suka yi tare da ita da kike yin wannan maganar? Kuma daga dukkan alamo na yadda take cin karenta babu babbaka a cikin gidan akwai wani alaƙa a tsakaninsu. Kin ga yadda take yi kowa? Mulki take zuba wa ko matar gidan sai haka, ta na ba da umarni da cikakken izza ta na wani yatsina fuska". Na ƙare zancen ina kwaikwayon yadda Altine take magana. "Ai duk kar ki yi duba da waɗannan abubuwan, idan ta yi miki kan kara ki yi mata na rodi idan ta ɗaga miki ɗan ƴatsa ki tabbatar da cewa kin karya shi kafin ta sauƙe. Da zaran ta ce miki kule ki ce da ita cas. Ai ƴar aiki ba ta fi ƴar aiki ba, shi kuma wancan mutumin ki manna masa bajin hauka tun da ba shi ya ɗauke ki aiki ba ai ba shi da hurumin sallamarki". "To shikenan zan duba na ga abin da ya dace na yi". "Ya fiye miki dai kam kafin kwaɓar ta yi miki ruwa tsalalo". Taƙaitacce murmushi kawai na saka ba tare da na ce da ita komai ba, haka muka yi sallama da ita bayan mun yi wa juna a kwana lafiya. Na raka ta har ƙofa ta fita na rufe ƙofar. Na zo na kwana na runtse idanuna ina karanto karatun haddan da yake cikin kaina har bacci ya yi nasarar ɗauka ta. Washe gari da wuri na farka na yi alwala na yi salla ragowar ruwan da nake da shi na shiga banɗaki da shi zan watsa. Ina ƙoƙarin cire sutarar da yake jikina na ji an bankaɗo ƙofar banɗakin tamkar za a ɓalle ta. Cikin wani irin gigicewa da ya wuce a misalta shi na yi hanzarin mayar da rigana jikina. Wani gardeden ƙato ne daga shi sai gajeren wando ga tulelen ciki a gaba kamar randa. "Ki fita zan yi wanka". Firgicin da nake ciki na hana ni motsa wa balle samun kuzarin mayar masa da amsa illa kallonsa da na tsaya iya yi. Ya daka mini tsawan da ya sanya jikin rawa tamkar ana jona mini wutar lantarki. "Ki fita na ce ko ba kya jin Hausa ne?". Ya ƙare zancen yana sanya ƙafa ya yi bol da bokitin ruwan nawan, jikina yana ɓari na ɗauki da yake ta gangarawa na fice da hanzari ban tsaya a ko'ina ba sai cikin ɗakina har zuwa lokacin jikina bai daina rawan da yake yi ba. Na hijabina da ya karkace tare da ɗaura ɗan kwalina da ya faɗi, ragowar lemukan da Hajiya Muhibbat ta saya mini na ɗauko na sha na haɗa da biskit kafin na ɗauka makulli na fito na rufe ƙofan, ƙofar ɗakin su La'aniyatu a rufe ya ke don haka da makullin na tafi. A hankali nake tafiya kamar wacce take jin tausayin taka ƙasa, gabaɗaya ba na jin daɗin yanayin ƙarfi kawai nake yi nake ci gaba da tafiyan ina jan silifas ɗin da ya yi wa ƙafafuna yawa sosai. A gajiye tulus na isa ƙofar gidan na ƙwanƙwasa mai gadi ya fito ya buɗe mini na tsuguna har ƙasa na gaishe shi ya amsa mini fuskansa tamkar gonan auduga. Kaina a ƙasa na shiga cikin gidan ina tafiya a hankali ban yi aune ba na ji na yi karo da wani abu har sai da na yi baya kaman zan faɗi. Da sauri na ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan sa yana tsaye cikin shigar ƙananan kaya, irin na ƴan wasan ƙwallo sai dai na shi wandon dogo ne har ƙasa, ƙafafunsa ne sanye cikin takalmi sau ciki kansa da hula kamar na sanyi. Bai ce da ni komai ba ya juya ya ci gaba da tafiyansa na bi shi da kallo na ga ya shiga wani sashi wanda bai kai na Hajiya girma ba. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 5️⃣1️⃣ Na daɗe tsaye a wajen kafin na ja jikina na ƙarisa shiga cikin gidan, tun daga falo nake nake yin sallama amma ba a amsa mini ba, tamkar gidan babu mutane masu numfashi. A buɗe baki a karo na uku da nufin ƙara rangaɗa sallamar na ji yo muryar Altine a bayana. "Malama wannan sallama haka sai ka ce wacce kike bin mu bashi ko kuma tara. Idan kika yi ɗaya kika ji ba a amsa miki ba ai sai ki tsagaita". Na tsuguna akan gwiwoyina"na ga kamar ba kowa a gidan nan ashe ku na ciki. Ina kwana an tashi lafiya?". Ta galla mini wani uban harara kafin ta ce"da ban kwana ba za ki gan ni ne?, Ba na son kinibibi da iyayin banza da na wofi in za ki tashi ki kama aikin da ya kallafa akanki tun wuri ki tashi in kuma za ki ci gaba da zama anan ne to bismillah". Tana dire zancen ta juya ta shige kicin ta bar ni durƙushe a wajen, sai da na ja dogon numfashi mai nauyi na fesar kafin na sama zarafin miƙewa na bi bayanta na ɗauko tsintsiya da mopper na fito falon, na share ko'ina tsaf kana na soma yin mopping. Sai da na gama na shiga ɗakin su Aryan shi ma na gyara shi na fito na koma kicin ɗin. Tana tsaye tana soyar ƙosai da ƙamshinsa ya cika ko'ina, na zo gefenta na tsaya cike da girmamawa na furta"na gama sharan shi ne na ce bari na shigo na tambaya, ko akwai wani aikin da zan yi miki?". Kamar ba za ta amsa mini ba sai kuma can ta ce da ni"karɓin soyan ƙosan nan bari na haɗa kunun". Cikin sauri

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});