Chapter 81
Chapter 81
kafe shi da idanuna ina ganin tamkar mafarki nake yi ba a farke nake ba. "An ya ka san abin da bakinka yake furtawa kuwa? Ko kuwa dai ka mance wacce take tsaye a gabanka ne?". Ban jira amsar da zai ba ni ba na ci gaba da zancena cikin ƙonar zuciya da tafasan rai. "Idan ba ka gane ni na yi mata tuni ni ce fa Amatullah wannan ɗiyar da ka zargi tarbiyyarta. Wacce ta yi ciki ba tare da aure ba wacce ta tafi can uwa duniya ta yi rayuwa ba tare da tsawatarwan iyayen ba. Wacce ta yi zaman kanta a cikin tsakiyar gidan karuwai ta ci gashin kanta da kanta. Wannan yarinyar da ta mayar da ɗakin otel tamkar ɗakin kwananta, wannan yarinyar marar tarbiya da nutsuwa. Wannan yarinyar da kake shakku da kokonton kasancewar ta kusa da ahalinka". Na saki murmushin takaici kafin na ci gaba daga inda na tsaya. "Shin ko ka manta ku rayuwarku a tsaftace take? Ba ku da wani abun aibu a tattare da ku shin ka manta ikirarin da ka yi na cewar Allah a raba ku da kaidina?. Yadda kake mutumin ƙwarai kuma kamili ai da matar ƙwarai ka dace wacce ta fito daga gidan tarbiya da halin girma. Saifullah kar ka yaudari kanka da neman soyayyarta domin bayan rashin dacewan da muka yi da juna ba zan taɓa iya cusa sonka a cikin zuciyata da ka zama silar raunatata ba. Na roƙe ka idan ma ɓatan hanya ka yi ko kuma tuntuɓe harshe ka samu to kar ka ƙara zuwa ƙofar gidan nan, babu wani abun da ya rage tsakanina da ku". Na ƙare zancen cikin rauni ina haɗe hannayena wajen guda alamar, zai yi magana na katse masa hanzari. "Don Allah ka bar ƙofar gidan nan wallahi ba na ƙaunar ganinka. Ka yi wa girman Allah ka bar ƙofan gidan nan". "Na ji zan tafi amma don Allah ki ba ni ko da mintuna goma daga cikin lokacinki, ki saurare ni ki ji bayanin da zan yi miki. Ban zo wajen da nufin yaudara ko cutar da ke ba hasalima....". Na datse numfashinsa"ba zan taɓa sonka ba Saifullah, me yasa ba ka duba matsayina da na ka ba da suka yi hannun riga. Ƙwarya ta bi ƙwarya idan ta bi alwashi ai fashe wa za ta yi". "Na ji na yarda ba za ki so ni, amma ni dai ki ba ni dama ki saurare ni". Hannayena na saka na toshe kunnuwana da shi yayin da hawaye suke zuba daga idanuna kamar bakin indararo, ganin ba zan iya jimirin sauraron zantukansa da suke barazanar raba ni da nutsuwata ba, hakan ya tilasta mini juya wa na shige cikin gida da gudu. Na ci karo da Anty Sawwama ta na fito wa daga banɗakin ina jin ta tana tambayata ko lafiya na shigo gida da kuka, amma ban iya amsa mata ba. Kai tsaye ɗakin kwanana na nufa na kwanta ina kuka, babu irin tambayoyin da ba ta yi mini ba amma na dage ina ce mata babu komai ba don ta yarda ba haka ta haƙura ta ƙyale ni. Daren ranar ban iya runtsa wa sai da dare ta raba cikin baccin na ji ana ƙiran sunana na tashi na zauna ina ƙara kasa kunne na ji dai tabbas sunana ake ƙira a tsakar gidan. Zumbur na yi na miƙe ina murtsike idanuna na buɗe ƙofar ɗakin na fito waje inda nake jin sautin ƙiran yana tashi. Ina fito wa na ga tsakar gidan ya yi haske sosai tamkar ba dare ba, na kai dubana inda nake ji sautin yana tashi idanuna suka sauƙa akan fuskan Hajiya Babba. Take ilahirin jikina ya soma rawa tamkar ana jona mini wutan lantarki na nuna da yar manuniyar yatsana bakina ya na rawa na ce"Hajiya Babba ke ce ki ka biyo ni nan?". Lu na ji na yi baya na zube a ƙasa yayin da kaina ya bugu da dutse, tun idanuna suna gano mini fuskarta dishi-dishi har sai da suka rufe gabaɗaya, daga lokacin ban ƙara sanin inda kaina yake ba balle fahimtar abubuwan da suke wanzuwa. [12/24, 3:41 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________ Page 7️⃣8️⃣ A hankali na soma buɗe idanuna da suka yi mini nauyin gaske kaina ya yi dum tamkar wacce aka yi wa ajiya dutse, hankalina yana dawowa jikina abin da ya faru ya dawo mini cikin kwanyata tiryan-tiryan, take na zabure ina rafka salati tare da runtse idanuna da matuƙar ƙarfi ina ta batutuwa mara sa kan gado. "Hajiya Babba me ye na yi miki za ki biyo ni har cikin gidan nan? A zamana da ke ko da wasa ban cutar da ke ba don Allah ke ma kar ki cutar da ni ko da kwantankwacin misƙala zarratin ne". Ji da na yi an dafo kafaɗana shi ya dawo da ni cikin hyayancina na buɗe runtsatstsun idanuna na kafe Anty Sawwama da su da take zaune kusa da ni, ganinta kusa da ni ya sani ƙanƙame ta a jikina tsaf ina zubar da hawaye tamkar an kunna burɗaɗɗan fanfo. "Uwata ki nutsu ki kwantar da hankali, babu wani abun da zai faru face alkhairi da iznin Allah. Babu wanda ya isa ya cutar da ke duk abin da kika ga ya faru da ke to daman haka Allah ya ƙaddara zai faru". Luf na yi a jikinta ina mayar da numfashi tamkar wacce ta yi wani gagarumin aikin wahala, mun daɗe a haka kafin ta ɗago ni daga cikinta ta tambaye ni abin da yake faru na kwashe komai na sanar da ita, haƙiƙa na hangi tashin hankali da tsoro kwance a cikin ƙwayan idanunta sai dai ta dannan duk yanayin da take ciki. A cikin daren ta ƙira Yaya Alhassan ya zo ta sanar da shi komai, ina kwance na ɗaura kaina akan cinyarta yayin da na lumshe idanuna tamkar mai bacci sai dai a farke nake don ina sauraron dukkan abin da suke tattaunawa. Cike da tarin damuwan da yake tattare da furucin bakinta Anty Sawwama take faɗin"tsoro ɗaya kar wannan matar ta sabauta yarinyar nan, ina tsoron har ta juya mata hankalinta ko ma ta raba ta da shi gabaɗaya, don irin waɗannan matan ababen tsoro ne". "Umma in sha Allah babu abin da ta isa ta yi wa Amatullah, gobe idan Allah ya kai mu zan je har can garin Jafarin mu yi ta ni da ita, in ta kama ma har ƴan sanda zan saka cikin lamarin". Anty Sawwama ta yi hanzarin taran numfashinsa"kar ka sake ka aikata wannan kuskuren Alhassan. Wani hujja kake da shi da za ka je har cikin gidan ka tunkare ta da wannan zancen? Ka san girman irin wannan lamarin kuwa? Hmm! Addu'a ita kaɗai ce mafita a gare mu". Shuru Yaya Alhassan ya yi har ta kai aya bai ce komai ba sai can ya ce"to yanzu Umma mene ne abin yi? Me ya kamata mu yi?". Ta saki sakakken ajiyar zuciyan da har sai da na ji sautin fitarsa kafin ta sama damar furta abin da yake kwance a ƙasan ranta. "Ina tunanin idan Allah ya kai mu gobe mu ƙira Malamai su zo, a kewaye
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98