Chapter 25
Chapter 25
da dukkan abubuwan more rayuwa da ƙawata waje, komai na falon fari ne tun daga kan labulaye, kujeru, tayis da kuma kafet ɗin hatta abin da aka ɗaura tv a kai fari ne. Na cire hijabina na ɗaura a ƙuguna na soma tattare takardun da na gani a barbaze akan kujerar kan teburin kofi ne da goran ruwan da aka sha ba a ɗauke ba. Na tattare takardun na kimtsa su na saka a cikin jakar da na gani a gefe, na ɗauke kofi da goran ruwan na shiga ɗaya daga cikin ƙofofi biyu da na gani. Ƙofan farko da na shiga na ga kicin ne na ajiye kofi da goran, kicin babu ƙazanta a cikinsa amma komai a birkice yake komai ba ya muhallinsa. Ban san sa'ilin da na saki tsakin takaici ba ina kwakwayon muryarsa na ce"ni ko'ina a sashina a gyare ya ke ko wata macen ba za ta nuna mini tsafta ba". Na tattare kicin ɗin na share kana yi mopping na fito na shiga ɗayan ƙofan ɗaki ne mai ɗauke da kayan ɗaki tsaf sai dai da alama ba wanda yake kwana a cikinsa saboda yadda ya yi ƙora na karkaɗe na sauya zanin gadon na shiga banɗaki na wanke na fito na hau benin ya sada ni da wani ɗan madaidaicin falo nan komai a gyare yake sai ɗan abin da ba za a rasa ba, na kashe tvn da na gani a kunne kana na rufe tagogin da suke buɗe. Ƙofa ɗaya na gani na shiga na tarar da ɗakin kwana ne shi ma komai na cikinsa launin fari ne hatta zanin dake kan gadon. Sauya zanin gadon na fara yi na gyara gaban madubin da komai ya ke warwartse kana na wanke banɗaki. Na hango wani air freshener akan dirowar da ke jikin gadon na je da nufin ɗauka na feshe ɗakin da shi, sai dai mummunan ganin da na yi ya tursasa mini tsayawa cak na kasa motsawa na tsawon wasu dakiƙu. Jikina yana rawa tamkar mazari na kai hannu na ɗauko hoton da na gani ajiye a saman dirowar ina ƙara ware idanuna akan sa. In dai ba idanuna ba ne suka sama matsala tabbas hoton Muhammad Taufik da Saif na gani tare cikin shiga irin ɗaya kowa hannunsa riƙe da sallaya da alama masallaci za su je, ko kuma ranar bikin salla aka yi hoton. Duk su biyun fuskokinsu yana ɗauke da maɗaukakin annurin. "Muhammad Taufik". Na furta cikin rawan jiki da na murya yayin da wasu hawaye suke gangarowa daga idanuna suna wanke mini fuskana. Jin an turo ƙofan ɗakin an buɗe ya sani na firgita da har ban san lokacin da hoton ya zame daga hannuna zuwa ƙasa ba, gilashin dake jiki ya yi kwasa-kwasa. Runtse idanuna na yi ina kai hannayena dukka biyu na toshe kunnuwana da ƙaran fashewan gilashin da ya gigita ni har ya na barazanar juyar mini da ƙaramar curin ƙwaƙwalwata. "Me ye kike yi a nan?". Na yi muryarsa tamkar daga sama ban iya cewa da shi komai har ya iso inda nake tsaye daidai lokacin da nake buɗe lumshashshun idanuna har na gama buɗe su tar akan gilashin da ya tarwatse a wajen. Ina ɗago kaina muka haɗa ido da shi ya yi mini wani matsaiyacin kallo kafin ya tsuguna ya ɗauki frame ɗin bai ce da ni komai ba ya fita daga cikin ɗakin. Wani kuka ne mai ƙarfi ya kuɓuce mini na sulale ƙasa na yi zaman dirshan ina jin yadda dunduniyar ƙafana ya cashi gilashin yana fitar da jini amma ban damu ba na ci gaba da kukan da nake, tare da jefa wa kaina jerin gwanon tambayoyin da na gaza cimma amshoshinsu. Me ye alaƙar Saif da Muhammad Taukif da har na ga hotonsu tare? Shin da gaske yadda kunnuwana suka ji yo mini shi ne baƙon da zai zo cikin gidan nan da yammacin gobe?. Tagwayen ajiyan zuciya mai ƙarfi na ja na fesar kafin na yi ƙarfin halin tashi tsaye ina ɗan ɗingisa ƙafata na ɗauko tsintsiya na share wajen na fesa air freshener ɗin da na yi niyya kana na ja ƙofar ɗakin na fito. Babu kowa a falon saman amma an kunna sautin karatun alƙur'ani cikin wata muryar da na kasa tuna inda na taɓa jin ta, na sauƙo ƙasa na iske shi zaune a falon ƙasa yana zaune ya yi shuru kamar wanda yake nazarin wani abu. Na zo na durƙusa a gabansa. "Na ga ma duk wani gyaran da ya dace na yi. Shi ne na ce bari na tamnaya inda akwai abin da kake so a yi maka". Sai da na cire rai da samun amsa daga gare sa, don har da ƙafafuna suka gaji na ji kamar na ɗaura hannuna a ka na yi ta kurma ihu tsabar takaicin da ya ƙunsa mini, na tsani na yi wa mutum magana ya yi banza da ni wannan abun ci mini rai yake yi sosai da sosai. "Za ki iya tafiya kuma kar ki ƙara dawowa sashin nan don ba na buƙatarki a nan. Don haka ki san abin da za ki faɗa wa Anty". Yana gama zancen ya tashi ya ɗauki wayarsa da wasu makullan da suke kan teburin da yake gabansa ya zuba a cikin aljihunsa ya fita, ni ma tashi na yi na fita sanda na fito na gan shi har ya shiga motarsa Baba mai gadi ya buɗe masa gate zai fita na bi motar da kallo har sai da ya fice daidai lokacin da na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 5️⃣3️⃣ Ji na yi kamar na koma cikin sashin na binciko dalilin kasancewar hoton Muhammad Taufik a cikin ɗakinsa, gabaɗaya na rasa gane kaina balle fahimtar abin da yake yi mini daɗi. Na tsaya cak a wajen ina ta karatun wasiƙan jaki da saƙa da warwara cikin raina. Kamar daga sama na ji saurar dirin sauti a cikin kunnuwana da ya tursasa mini ɗago idona Ina duban Baba Mai gadi. "Ƴar nan lafiya? Tun ɗazu na hango ki kin fito kin tsaya a nan kin yi shuru. Ko dai akwai wani damuwar ne?". Na saki taƙaitaccen murmushin da iya kansa kan leɓena bai kar har cikin zuci ba. "Lafiya ƙalau Baba. Yanzu ma wajenka nake son na je in ba ka wani aikin ka soma koya mini ƙananun kalmomin yaren". Ya yalwata annurin fuskarsa kafin ya furta"ai kuwa ba na komai ina dai zaune ne kawai". Yana dasa aya a zancen ya juya na bi shi a baya har zuwa bakin gate ɗin ya zauna akan wani benci yayin da na zauna a kusa da shi. "To yanzu ta ina za mu fara?". Na duƙar da kaina ƙasa"ai Baba tun daga gaisuwa za a fara koya mini har a gangaro a zo kan ƙidaya da wasu kalmomin da suka kasance na amfanin kullum-kullum". Ya yi dara kafin ya ce"to kamata ya yi ki nema takarda da biro ina faɗa miki ki na rubutawa, tun da kin yi karatun zamani ai ko?". Na riƙe haɓa"na yi amma ban yi nisa ba". Kafin ya ce da ni wani abun Altine ta iso wajen kamar mai shirin zuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98