Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ratsawa. Ƙaran sauti da kiɗe-kiɗe suna daga cikin abubuwan da suke sautin kiɗima ni tare da saurin juya mini ƙwaƙwalwa da damalmala mini dukkan lissafi gami da hautsina mini hankali. Na kai hannuna na toshe kunnuwana tare da runtse idanuna da ƙarfi, duk ina daurewa har lamarin ya gagare ni wai cire wando ta kai. Ba tare da na buɗe idanuna ba na ce"don Allah ki yi haƙuri baiwar Allah ki tage ƙaran sautin nan". Ba ta tanka mini hakan ya sanya ni buɗe idanuna ina hango inda take na ga tana kwance a bisa katifarta tana ta sharara baccinta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ga sautin yana ta tashi a cikin ɗakin. Na tashi na ina jin hajijiya yana ɗeba na dafe gefen gini ina tafiyan a haka har na isa wajen da ta ajiye MP na kai hannu na ɗauka na kashe ta na mayar na ajiye. Ko barin wajen ban yi ba ta farka tamkar sautin MPn da baccin da take yi tare suke tafiya, ta murtsike idanunta tana kallona. "Bura uban can! Uban waye ne ya saki kashe min MP?". "Amma kin san ai ɗakin ba ke ɗaya ba ne, kin san da cewa da ƙaran sautin nan ki na shiga cikin hayyacina". Kamar na watsa mata tafasasshen ruwan zafi a jikinta ta miƙe zumbur ta tsaya akan ƙafafunta ta riƙe ƙugu. "Ke bari na fito miki a mutum kuɗi fa na cake na biya na kama ɗakin nan ba wai kyauta nake zaune ba ko kuma alfarma aka yi min ba. Kin gan ni nan ni ba na iya bacci ba tare da na kunna sauti ba, don haka tun wuri gwara ki saba". Tana dasa aya a nan ta kunna MP ɗin ta koma ta yi kwanciyarta tana kaɗai ƙafa, na kasa motsawa daga wajen balle na koma inda na taso duk da jirin da yake ɗauka ta. Sai da na saki dogon numfashi na fesar kafin na ja ƙafafuna na koma inda na taso na zauna na zabga wani uban tagumi tamkar wacce aka yi wa rasuwa ta wani babban makusancinta. Tun yana damuna har na zubar da komai na tashi na ɗauki buta na fita na je banɗaki na yi tsarki, na fito ina isowa tsakar gidan na yanke jiki na faɗi jirif kamar kayan wanki. Ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai buɗe idanuna na yi na gan ni kwance a cikin wani ɗakin da ban ga ne wajen ba, na yunƙura zan tashi na ji na kasa dole na komo na kwanta ina tunano abin da ya faru kafin faduwar hakan. "Sannu kin tashi ne?". Na tsinkayo wata baƙuwar murya ta sauƙa a kunnuwana na cira kai ina kallon matar ba tare da na ce komai ba. Zan tashi ta riƙe mini hannu"ki koma ki kwanta har yanzu jikinki babu ƙwari sosai". "Ina ne sannan wace ce ke?". Ta faɗaɗa annurin fuskarta kafin ta so daidai saitin kunnuna ta ce"sunana Zinariya". "Me ya kawo ni cikin ɗakin nan?". "Faɗo wa kika yi a tsakar gida babu wanda ya kula ki balle ya kawo miki ɗauki, haka na shigo na ganki yashe a ƙasa na ja shigo da ke cikin ɗakin na kwantar da ke. Shi ne tun ɗazun kike bacci sai yanzu kika tashi". Na buɗe baki zan yi magana kukan da ya kufce mini ya hana ni damar furzo da zancen da na yake kan harshena. Ta dafa kafaɗana"ki na jin wani ciwo a jikinki ne? Na girgiza kaina alamar a'a na tashi na zauna da ƙyar har zuwa lokacin hawayen suna zuba daga idanuna. "Don Allah zan sama ruwa na yi alwala?". Sai da ta bi ni da kallo kafin ta furta"a cikin wannan yanayin za ki yi salla?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta lasisin ci gaba da maganan cikin mamakin da ya bayyana har a cikin furucinta. "Ga buta ki ɗauka sai ki je ki yi alwalan". "Na gode". Na amsa da shi a taƙaice ina dirowa daga kan katifar na sauƙo ƙasa na mayar da ɗan kwalina da ya same kaina, na ɗauki butan na fita waje na je na yi alawan sanda na shigo na tarar da ita tana waya na ajiye wayar ba tare da na yi mata godiya ba. Ɗakina na wuce na tarar da ita har yanzu tana baccin ga sautin yana tashi sai dai amon bai kai na ɗazu tashi ba. Na ayi sallan na zauna a wajen ba tare da na tashi har sai da na yi sallan asr kana na fara yin wani irin yunwa yana ƙwalulan hancin cikina, na jawo ledar kayan nan na gama da ragowar sauran lemukan. Sai a lokacin da hankalina ya dawo jikina na tuna da cewar haka na fito daga gidan ba tare da na sanar da Hajiya Muhibbat halin da nake ciki ba. Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina jin har yanzu kunnuwana sun yi mini wani dum tamkar wacce aka ɗurawa wuta a ciki. Na tuna marin da cin mutuncin da Altine ta yi mini take na ji raina yana soyiwa tamkar yadda ake soya gyaɗa marau-marau a cikin toka. Na ja dogon gashin na fesar daga bakina ina jin wani hawaye suna ciko mini kurmin idaniyata tabbas na yarda rayuwa ba za ta yiyuwa a haka ba dole ni ma sai na tashi na soma nema wa kaina ƴanci, na fara tsaya wa kaina a cikin ko wani irin yanayi don tabbatar da zaman lafiya da jin daɗina. Dafo kafaɗana da na ji an yi shi ya dawo sa ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa, na ɗago kaina ina kallon La'aniyatu da take tsaye a kaina tana kallona. "Ki zo Hajiya tana ƙiranki". Kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na bi ta a baya har zuwa cikin ɗakin Hajiyar ta shige cikin uwar ɗaka yayin da ni kuma na zube a falo ina na iske Hajiya Babba da kuma Aminu zaune. Cikin girmamawa na gaishe da su sai dai cikin su babu wanda ya tanka mini illa bi na da kallo suke yi kamar yau suka fara tozali da ni. "Amatullah". "Na'am ranki ya daɗe". "Ɗaga idonki ki kalle ni da kyau kuma ki saurara abin da zan faɗa miki da kunnen basira". Na cira kaina a hankali ina kallon ta da hakan ya ba ta damar ci gaba da zancen da take yi. "Gidan nan da kike gani ba wajen sauƙan baƙi ba ne. Gidana gidan gudanar da kasuwanci ne da za ki iya gudanar da su ko kina daga kwance akan katifarki, ba zai yiyuwa ki zauna ki miƙe ƙafa da sunan ki na fita aikin bautan da sai wata ya ƙare kafin a ba ki kuɗi ba, don waɗannan kuɗaɗen ba za su ishe ki ɗaukar ɗawainiyyar kanki ba ma balle har ki biya kuɗin hayan ɗakin da kike zaune a cikinsa har ki yi sauran buƙatunki. Ki kama sana'ar da ƴan matan gidan nan suke yi ko kuma ki shirya barin cikin gidan nan. Tun da kika zo cikin gidan nan ba ki sauya ba kullum jiya i yau ko takalmin takawa ba ki da fitacce balle kuma suturar kirki". Tun da ta fara

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});