Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

filin yaƙi ta ja ta tsaya a gabanmu hannunta riƙe da wani baho ƙiran ghana must go ƙarami. "Amma kin san akwai aiki a cikin gidan kika zo nan kika tare ko?". Cike da mamaki na ɗaga ido ina kallonta da ta haɗe girarta na sama da na ƙasa. Ta murtuƙe fuska kamar magribar ɗinya. A hankali na ce"na wanke har kwanukan da aka ci abinci fa kafin Hajiya ta ce na je sashin can na gyara....". Tun kafin na gama ta tari numfashina"don kin wanke kwanuka kuma sai aka ce miki babu wani aikin ko? Ki tashi ki shiga ciki ki gyara ɗakin su Arya kafin na ce na kai saƙon nan na dawo, a fara shirin abincin rana". "To ki dawo lafiya". Na amsa da shi cikin sanyin murya ba ta amsa mini ba illa tsakin da ta tsirtar tamkar ta yi arba da ɗanyen kashi sakin yanzu-yanzu, ta ja bahon da ƙyar za ta bar wajen Baba mai gadi ya dakatar da ita ta hanyar faɗin"Hajiya Altine wannan kayan fa? Mene ne a ciki na ga ki na ja da ƙyar". Ta galla masa wani uban harara tamkar idanunta za su faɗo ƙasa"to ƴan sa ido masu zuwa lahira da cover shoe. Me ye naka a ciki? Ina ruwanka da ni balle kayan da zan fita da shi? Kowa ya tsaya a matsayinsa ka tsaya a matsayinka na mai gadi ni ma na tsaya a matsayina na ƴar aiki. Idan ba so kake yi mu ba wa hamata iska ba ni da kai". Jijjiga kansa ya yi a taƙaice ya furta"Allah ya kyauta". Ta yi wuf ta amshe zancen tamkar jira take yi"Amin in da gaske kake yi". Daga haka ta ja bahon ta fita da shi duk mu biyun muka bi ta da kallo har ta fice na sauƙe sakakken ajiyar zuciya mai matuƙar sauti. "Ɗiyata sai haƙuri fa zama da Altine ko na sakon ɗaya ne sai ka haɗa da haƙuri. Balle zaman awanni har ma ranaku da dama, kin gan ta nan tun farkon auren Hajiya aka kawo ta aiki a cikin gidan nan, Hajiya da mijinta har ma da ƙaninsa sun yarda da ita matuƙar yarda wanda har ya wuce kima sun yi imanin ba za ta a taɓa haɗa baki da ita a cutar da su ba balle ace ita da kanta ne za ta cutar da su. sai dai ba san cewa a cikin zaman da suke yi da ita cutar da su take yi su da ƴaƴansu ta ƙarƙashin ƙasa ba, ta yi musu illa sosai amma har yanzu ba su farga ba balle su gano fuska biyu gare ta". Tun da ya soma maganan na sake baki da hanci ina jin sa da kallo har ya kai aya kana na ja dogon numfashi na fesar kafin na zama lasisin faɗin"wani irin illa kenan Baba?". "Iloli masu yawan gaske ma kuwa, kin ga Altinen nan da kike ji da gani ta ƙi jinin ta ga wata ko wani ya raɓe jikin Hajiya mussamman in ta lura zai karu da wani abu, ka mamaye komai na cikin gidan nan duk wata ƴar aikin da za ka kawo da sunan ta zama mataimakiya a gare ta sai ta yi yadda ta yi ta yi kwance-kwance ta ƙulla mata tuggun da ba za ta iya fitar da kanta ba. A ƙarshe da kanta za ta zaɓa barin aikin akan ta ci gaba da zama. Ki na ganin Altine hatsabibiyar mace ce, akan ta na ƙara yarda da cewar ko sheiɗan dole ya ji tsoron kaidin mace balle mu kuma bil adama. Ki yi hankali da ita". "To wannan kayan da ta fita da shi ba ina za ta je da shi?". Ya saki taƙaitaccen murmushi kafin ya ce"a sannu a hankali idan Allah ya san zamanki a cikin gidan nan ya yi tsawon rai za ki fahimci inda take kai kayan". Ƙirjina ya buga da ƙarfin gaske cikin son ƙarin bayani na ce"ban gane idan zama na ya yi tsawon rai ba". "Duk wata mai ƴar aikin da ake kawo wa cikin gidan nan a ta wuce adadin makonnin huɗu take fita. Don haka ke ma ki yi taka tsantsan ki kuma san irin zaman da za ki yi a cikin gidan nan, mussamman kasancewar ki yariya mai ƙaranci shekaru". Jikin gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Na gaza cewa komai duk da tarin tambayoyin da suka yi mini tsayiwar ƙayan kifi a maƙoƙarona da ƙyar haɗiye miyau ɗin da ya taru mini a cikin baki. "Ƴarta ki kwantar da hankalinki ban sanar da ke hakan don na tayar miki da hankali, ko kuma don na kashe miki ƙwarin gwiwa ba. Ki ci gaba da aikinki sannan gefe guda ki dage da addu'a ki tabbatar da ba ki mu'amalance kowa da wani mummunan hali ba. Ki tashi ki shiga ciki kafin ta dawo ta same ki a nan ". "To Baba na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". "Amin Allah ya yi albarka". Ban iya amsa addu'ar cikin kalmomin baki ba sai a cikin zuciyana na amsa yayin da nake tashi daga wajen na nufi cikin gidan kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Wayam na iske falon babu kowa sai su Arya da Ayan suna kallon TV na bi shi su da kallo. Ban san me yasa haka kawai a duk lokacin da na ga yaran nake jin suna matuƙar burge ni. Na daɗe ban ga yara ƙananu masu irin shekarun da suke da kwatankwacin irin nutsuwarsu ba haka kawai na tsinci kaina cikin sakin murmushi, sai da na ƙare musu kallon tsaf kana na wuce kicin na ɗauko tsintsiya da mopper na dawo na nufi ɗakin su Ayan. Sai da na gyara musu gadon na sauya zanin gadon na saka wani na shara ɗakin na yi mopping kana na shiga banɗaki na wanke na feshe ko wani kusurwa da room freasher. Sai da na gama komai na fito jikina gabaɗaya babu gaɓar da ba ya yi mini ciwo. Ina ajiye tsintsiya da moppern na fito na wuce ɗakin Altine kamar kayan wanki na zube akan katifa ina mayar da numfashi kamar wacce ta yi aikin ɗaga ƙarfe, ko'ina a jikina ciwo yake yi mini har ba na ƙaunar motsawa, na lumshe idanuna a hankali ina jin wani mayataccen bacci yana fizgana ban san sa'ilin da na yi baccin ba sai jin sauƙan ruwan sanyi na yi a jikina. Figigi na tashi ina jan wani dogon numfashi na fesar da shi yayin da nake tantance inda nake don gabaɗaya ɗakin ya juya mini na kasa gane komai tamkar wacce aka yi wa dashen sabon curin ƙwaƙwalwa a cikin kanta. Kafin igiyar firgicin ya gama saki na na tsinkayo muryar Altine raɗau a masarrafar jina. "Kwanciyan me ye kike yi? Ai kwanciya bai kama ki tun da dai neman kuɗi kika fito yi. Ki tashi ki je ki share filin tsakar gidan nan tsaf". "Na gama duk wani aikin da ya kamata na yi shi yasa na zo nan na kwanta ina hutawa. Wallahi gabaɗaya gaɓobina ciwo yake yi mini.....". Kafin na gama zancen na ji ta sauƙe mini mari a gefen fuskana na

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});