Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 68

Chapter 68

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kika shiga lokaci guda fa kika fita daga cikin hayyacinki, babu wani wanda zai gan ki a wannan lokacin ya tsammata miki za ki ƙara yin numfashi ko da na sakon ɗaya ne a cikin wannan duniyar. Waɗannan mutanen da suka ikirarin cewar su ƴan uwanki ne su ne suka kawo ki asibiti tare da ni aka yi komai don jiya har sai dare kafin na bar cikin asibitin nan, don Likitotin sun ce babu wanda zai kwana a wajenki. Waɗannan mutane sun nuna miki ƙauna mai ƙarfi da ta amsa sunanta, a dai cikin wannan duniyar da muke rayuwa a cikinsa da mutanen kirki suka yi ƙaranci da wuya a sama masu kirki da tausayinsu. Daman ki na da ƴan uwa maza ne? Don a labarin da kika ba ni kin ce ke ce ɗiya ɗaya tal a wajen iyayenki?". Na furzar da iska mai zafi daga bakina kafin na soma ba ta amshoshin tambayoyinta. "Tabbas kam yadda suka ce su ɗin ƴan uwana ne, sai dai ba muharramaina ba ne. Mahaifiyarsu ce yayar mahaifina uwa ɗaya uba ɗaya. Mai farin kayan shi ne Yaya Alhassan wanda aka so haɗa ni aure da shi ɗayan kuma ƙaninsa ne Amir wanda yake bin bayansa, idan ba ki manta ba su ma na ba ki labarinsu". Cike da mamaki ta riƙe haɓa"yanzu Amatullah wannan zankaɗeɗen saurayin kika ƙi aura? Shi kuwa me ye laifinsa? Ga shi da kyau, ga ƙira da kuma kwarjini da ɗin da ɗawa ga kuma daɗin murya". Jinjina kawai na yi ba tare da na ce da ita uffan ba don na lura da yanayinta ko da na cewa wani abu, ba lalle ba ne ta fahimta balle har ta fahimci halin da zuciyata take ciki. "To yanzu me ye dalilin wannan zuwan da suka yi? Don fa sai da aka ɗeba ƴan kallo tsakaninsu da Hajiya Babba ta yi musu tijara mai wasali, wannan ƙaramin har sai da ya fusata ainun don har sai da ya yi yunƙurin kai mata mari Aminu ya amshe cikin faɗan. Nan ta tada tijarar sai an biya ta kuɗin hayan ɗakinta da kika zauna a cikin kaf, Aminu ya bijiro da na shi buƙatar sai da aka biya shi wai kuɗin ɗawainiyyar ciyar da ke da ya yi a lokutan baya. Take suka karɓa lamban asusunsu suka tura musu kuɗin, kafin Hajiya ta bari suka kawo ki wannan asibitin ta kuma gindaya musu sharaɗin yadda suka fita da ke a cikin gidan nan, to su tabbatar da cewar kin fita ke nan har abada ko kin dawo sai dai ki nema wani masauƙin amma dai ba cikin gidanta ba". Cike da damuwar da yake barazanar tarwatsa zuciyar da take kwance a cikin ƙirjina, na kai hannuna na dafe kaina da yake sarawa da ƙarfi. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Me yasa Hajiya kuwa za ta yi mini haka?". "Babu wani dalili illa na baƙin ciki da tsanar da ta yi miki tun farko, mussamman da kika ƙi bin layin da ragowar ƴan matanta suke bi. Ga ki da diri da kuma sura komai cif-cif kin ga kuwa ai da kin ba da kai bori ya hau ba ƙaramin harka za a buga da ke". "Ai kuwa in sha Allahu na bar cikin gidanta ke nan har abada". Zinariya ta yi hanzarin tarar numfashina"ban ga ne kin bar gidan har abada ba ina za ki koma ke nan?". Na kwashe duk yadda muka yi da su Yaya Alhassan na sanar da ita, ina gama ba ta bayanin kawai na ga ta fashe da kuka sosai lamarin da ni ma ya saka ni kuka muka rungume junanmu babu mai lallashin wani a cikinmu. Ni na fara yin ƙarfin halin tsagaita na wa kukan na ɗago kanta ina share mata hawayen fuskanta tare da faɗin"zan koma gida Zinariya Allah ya yanke mini wannan zaman ƙasƙanci da wulaƙancin. Ke ma ina mai ba ki shawara ki yi wa kanki karatun ta nutsu ki koma gida, na tabbatar da cewar iyayenki za su amshe ki". Cikin muryar kukan da ya gama galabaitar da ita ta ce da ni"Amatullah ba zai yiyu yanzu in ce zan koma gida ba in kuma na yi yunƙurin hakan to ina mai tabbatar miki da cewar sai dai a komar da gawata. Sa boda mun riga da mun shiga cikin ƙungiya mun kuma yarda za mu yi biyayya ga dukkan dokoki da sharaɗoɗinta duk wanda ya ce zai fita to ɗayan biyu ne ko dai ya haukace ko kuma ya bar cikin duniyar gabaɗaya. Ke ma da ba kya cikin ƙungiyar ina jiye miki tsoron abin da Hajiya Babba za ta iya yi a kanki mussamman yadda suka yi musayar yawu da ƴan uwanki". Gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau na kasa cewa komai har sai da ta ci gaba da maganar"ke dai Allah ya ƙaddara ba za ki saɓa masa ba ta hanyar keɓe wa da wani ɗa na mijin da ba halal ɗinki, ƙaddarar rayuwa a barikin ce kawai a kanki amma babu ƙaddarar saɓawa Ubangiji. Na taya ki murna da ba ki bari sheiɗan ya yi nasara akan yi ba haka nan ba ki taka rawa a lokacin da yake buga gangar sheɗancinsa ba, za ki koma gidan iyayenki cikin aminci da kuma mutunci Amatullah. Ga wannan wayar ki tafi da ita idan kin nutsu ki ba wa ƴan uwanki su saurari abin da yake ciki na san cewa za su fahimce ki". Tana gama maganan ta riƙo hannuna ta damƙa mini wayar yayin da ta fashe da wani kuka da ni ma ya tursasa hawaye kwaranya daga idanuna. Ban iya ce mata ko kanzil ba har zuwa lokacin da Yaya Alhassan suka dawo cikin ɗakin tare da Likitan ya duba ni ya kuma tabbatar da cewar jikina ya yi sauƙi ya rubuta mana sallama tare da wasu magungunan da ya ce lalle a saye su, kuma na fara amfani da su da gaggawa. Haka muka fito har cikin haraban asibitin hannuna saƙale cikin na Zinariya, da Yaya Alhassan yake ta yi mata nasihar ta tuba da koma zuwa ga Allah da ya kasance gafurul rahim. Kanta kawai take gyaɗa masa don da ni da ita mun an cewa akwai ɓoyayyan matsalan da bala'in da yake tattare da hakan. Ko da muka zo rabuwa da ita ji na yi tamkar raina zai bar gangar jikina. Haka muka sha kukanmu Amir ya din ga ba mu haƙuri da ƙyar muka saki hannun juna, haka muka rabu muka hau adaidaita muka nufi tasha, muna isa muka saka motar garinmu ba mu yi mintuna goma ba ta shiga muka soma tafiya. Tun da muka soma tafiya ƙirjina yake bugawa har muka isa cikin garin, ina fitowa daga cikin motar na ji gabana ya faɗi da har sai da na runtse idanuna, muka tara adaidaita muka shiga na lura har zuwa wanna lokacin Yaya Alhassan fushi yake yi da ni hatta magana ma sama-sama yake yi mini shi ma sai ya zama dole ne. Mu na iso ƙofar gidan Anty Sawwama na ji wani zazzafan zazzaɓi ya lulluɓe wajen gabaɗaya ya sauya miki tamkar wacce ta yi shekaru goma cur da barin cikin gidan, da ƙyar nake ɗaga ƙafata da na

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});