Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,212 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yi ƙoƙarin amsawa mata da kalmomin baka bakina zai ba ni haɗin kai waje aiwatar da hakan a aikatace. Na nufi kicin na ɗauko tsintsiya da faka na zo na share inda plate ɗin ta tarwatse na je na zubar, a hankali na dawo cikin falon ina tafiya a hankali don haka kawai na ji gabaɗaya ƙafafuna sun riƙe ta yadda da ƙyar nake ɗaga su ina sauƙewa. "To baƙon nakan yaushe zai zo sai mu fara shiri?". Na ɗago kai ina satan kallonsa na ga idanunsa suna kan plate ɗin ƙosan da yake gabansa sai dai ban ga sa'ilin da ya kai ko guda cikin bakinsa ba. "Gobe da yamma in sha Allah zai shigo garin nan tare da mahaifinsa". "Allah Sarki! Muhammad Taufik ina jin daɗin ganin yadda yake bayar da hankali wajen ba wa addini gudunmawa kamar yadda mahaifinsa yake yi, duk da irin yanayin aikinsa. Shi fa yanzu lokacin kansa ma bai da shi balle kuma na mace daga kai har shi ɗin shi yasa har yanzu kun kasa fito da matayen aure. Ga shi kullum ƙara girma kuke yi shekarunku suna ƙara tafiya". "Hajiya Antynmu ai komai lokaci ne, idan lokacin mu ya yi babu makawa za mu yi auren nan. Ko kika sa ni ma ba mu daga cikin wanda Allah ya ƙaddarawa za mu yi aure a cikin duniya". Ya ƙare zancen yana miƙe wa tsaye daidai sanda zan shige ɗaki na ji Hajiya Muhibbat tana tambayar sa ya ta ga ya tashi? Ya ce da ita ya ƙoshi ban san yanda suka ƙare ba na shige ɗakin. Ina shiga muka haɗa ido da Altine ta banko mini wata uwar harara tamkar wacce ta yi arba da kashi, na yi hanzarin janye idanuna ina ƙariso na zauna a ƙasa. Mun shafe a ƙalla mintuna talatin ni da ita babu wanda ya ce da wani ko kanzil ina waige-waigena na hango alƙur'ani ajiye a saman akwati. "Anty Altine don Allah ina ba damuwa zan yi amfani da alƙur'anin nan". Ta ɗago ido ta yi mini wani banzan kallo kafin ta ce"ai ba a kaina kika gan shi, da za ki ce sai kin jira na sauƙe kafin ki yi amfani da shi". Ban ce da ita komai ba na tashi na ɗauko alƙur'nin na soma karanta suratul Maryam cikin nutsuwa da fitar da haƙƙin ko wani harafi ɗaya bayan ɗaya. "Malama ki rage muryarki don bacci nake so na yi". Na yi mata wani kallo ta wutsiyar idona na ci gaba da karatun da nake yi ba tare da na bi ta kanta ba. Ban yi aune ba kawai na ji an zagbaw mini wani gigitaccen mari a kuncina babu shiri na dafe kuncina tare da ɗago idanuna na sauƙe shi akan fuskar Altine da take tsaye a kaina ta riƙe ƙugu tana huci tamkar saniyar da take shirin kai bugu. "Me ye na yi miki da za ki mare ni?". "Bari ki ji in gaya miki wani abun da ba ki sani ba shi ne duk wata ƴar aikin da aka kawo cikin gidan nan dole ta bi umarnina. Sannan wajibi ne a gare ta ta yi mini biyayya don a gaba nake da ita. Na lura tun ranar ki ta farko kanki yana rawa ki na ta wani ƙoƙarin shige wa jikin Hajiya da wani kinibibin jan su Aryan a jikinki, to billahillazi tun wuri gwara ki kama kanki kafin na haɗa miki sharri da tuggun da ba za ki iya fitar da kanki ba". Na ji zuciyata tana wani irin harzuƙa ta zo mini har wuya tabbas na yi sanyi don da zamani da nake gida ne ba ta isa ta ɗaga mini ƴatsa ban karya shi ba duk da kuwa ina da haƙuri matuƙa da kai zuciya nisa. Tsam na miƙe jikina har wani rawa yake yi kamar mazari haƙwarana suna karabɗiya da juna suna ba da wani sautin ɗas ɗas. Ta matso dab da ni ta ce"ko za ki rama ne na ga kin miƙe ina wani jijjiga?". Ta saki wani bushashshiyar dariyar da ba ta da haɗi da nishaɗi, jin daɗi ko kuma walwala kana na furta"ai ko dukana kika yi da itacen bishiya ba zan rama ba Anty, sa boda na ƙoshi da tarbiyya kuma an koyar da ni yadda zan girmama na gaba da ni ko da kuwa da sankan ɗaya ya riga ni zuwa duniya balle ke da kin kusa haifa ta. Bari na je na duba Hajiya ko sun gama na tattare kwanukan". Da alama ba ta ji daɗin zancena na ƙarshe ba don sakeke ta yi tana bi na da kallo tamkar ta sama majigi har na fice daga cikin ɗakin ba ta ce da ni komai ba. Da sallama na ƙariso ciki falon na ga har sun gama cin abincin sun koma kan kujeru sun zauna, na tsuguna na yi wa Hajiya sannu da hutawa kana na isa wajen dinning table ɗin na tattare kwanunkan na kai kicin na wanke su tas na mayar da su majiyarsu. Ina kicin ɗin Ayan ya shigo wai na zo in ji Umminsu, muka fito tare da shi na zauna a ƙasa cikin girmama wa na ce"Hajiya ga ni". "Jiya Saif ya kai ki gidan nakun?". Ƙirjina ya buga da ƙarfi na ɗago ido ina satan kallonsa na ga shi kam ko a jikinsa wai an muntsini kakkarauna yana zaune yana latsa wayar da yake hannunsa. Sai da na daidaita nutsuwata kafin na iya furta"e Hajiya ya kai ni". Ta mayar da dubanta gare shi"ka ga gidan na sun?". Ba tare da ya ɗago kansa ba ya ce"e Hajiya Antynmu ko yanzu ma in ki na so zan iya kai ki". "To alhamdulillah tun da ka ga gidan, ka ba ta makullin sashinka ta share maka kafin ka fita. Don ni yau sai around 5:pm zan fita". Sai a lokacin ya ɗago kansa daga latsa wayar da yake yi"Anty ni fa sashina a gyare yake. Ke ma kin san ko wata macen ba za ta nuna min tsafta ba balle kuma wannan". Ta murmusa kafin ta ce"ai duk tsaftan namiji Saif a bayan mace yale komai ƙanƙantan ta kuwa. Ka ba ta makullan kawai ta je ta gyara maka, kar wani gyara ka iya kai da yaushe ma ka zauna a cikin gidan". Kamar na yi magana na ce ta ita ta bar shi kawai tun da ba ya so sai kuma na yi shuru. Muryarsa a cushe ya ce"a buɗe yake". "To Amatullah tashi ki je sashin nasan ma a buɗe yake, ki gyara masa shi tsaf irin gyaran da shi da kanki sai ya sa an nemo ki gobe. Idan hakan ya faru kuma ni da kaina zan tsaya miki ki gara shi kamar ƙwallon ƙafa kafin ki je ki ƙara gyara masa". "To Hajiya". Na amsa da shi a taƙaice jikina gabaɗaya ya mutu murus, na tashi na fita zuwa sashin nasan ƙirjina yana tsananta bugu kamar zai fito waje. Sai da na isa ƙofar sashin na ja dogon numfashi na fesar kafin na turo ƙofar na shiga ciki na tsaya ina ƙarewa zubi da tsarin falon kallo. Ba shi da girma sosai don bai kai na Hajiya Muhibbat ba ya tsaru sosai

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});