Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 84

Chapter 84

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na yi shuru ɗaya ɓangaren ma aka yi shuru har sai da na yi zaton ƙiran ya katse kafin na ji an yi magana. "Na san ba ki gane mai magana ba ko?". "E". Na amsa da shi a taƙaice. "Saifullah ne". Ban san lokacin da na maimaita sunan cikin ɗaga sauti ba. "Saifullah kuma? A ina ka sama layina?". "Yayanki Amir ne ya ba ni layin. Ina fatan bai yi laifi ba?". Numfashi mai zafi na furzar daga bakina kafin na ce"sanar da ni dalilin ƙiran don ba ni da lokaci". Ina iya jiyo sakakken ajiyar zuciya da ya sauƙe kafin ya sama zarafin faɗin"kawai na ƙira na ne na ji yadda kika wuni". Wani bambarakwai na ji lamarin ya zo mini a bazata mamaki da al'ajabi ya hana ni cewa komai illa jujjuya zancen nasan da nake ta ci a can cikin ƙasan raina. Tamkar ya san abin da nake tunanin ya ce"ki na mamaki zantukana ko? Uhmm! Ni ma kaina idan na zauna mamakin kaina nake yi Amatullah ban taɓa tunanin zan iya furta irin waɗannan furucin da nake yi miki yanzu a kaf cikin rayuwa. Sa boda tun tasowa ta na tashi ni ban kasance mutum mai yawan magana ki shiga hayaniya ba, haka nan mata ba sa gabana harkan da ta sha min kai shi kaɗai nake mayar da hankalina a kansa". "Uhmm". Na amsa da shi a taƙaice ina ɗaukar wayar na kara a kunnena bayan na cire ta daga amsa-kuwwar ina ci gaba da sauraron abin da yake furta wa. "Amatullah ban zo gare ki da yaudara, mugunta ko kuma cutarwa ba. Hasalima zuciyata a wanke take babu wani mummunan abu a cikinta. Ba zan gaji da sanar da ke cewa ina sonki ba idan har kika ba ni dama babu abin da zai hana ni aurenki ko da kuwa duk mutanen duniya za su taru a kaina". Cike da ƙosawa da zancen nasan na kawar da zancen ta hanyar faɗin"ina su Aryan?". Sai da ya yi ɗan jim kafin can ya ce"suna nan lafiya, Amatullah ki ba ni dama na nuna miki irin soyayyar da nake yi miki". "Wai har yaushe ka fara son nawan ne? Da kake ta ikirarin soyayya haka?". Na jefa masa tambayar raina a ƙunzume ina jin wani ɓacin rai yana cika mini zuciyata taf. Sai da ya ɗauki mintuna a ƙalla uku kafin ya dawo mini da amsa. "Tun daga lokacin da na daina sanya ki a cikin idona, tun daga lokacin na fahimci sonki ya yi min mamaya a cikin zuciyata ba tare da na farga ba". Na yi luf tamkar wacce ruwa ya cinye ta. "Wataƙila ki ji zantukana tamkar waƙan shata ta yadda za su shiga ta kunnenki su fita ta ɗaya. Na riga da na sanar da ke iya gaskiyar abin da yake cikin zuciyata, ke ma ki je ki yi shawara da na ki zuciyarki da dul waɗannan kike ganin kin aminta da su, sannan abu mafi muhimmanci ki yi sallan istikara. Kar ki ji shakka, nauyi, ko tsoron sanar da ni duk abin da kuke ji a ranki a game da ni. Kin gan ni nan a cikin rayuwar nan babu wani abun da yake ba ni tsoro, sa boda duk abin da nake tsoron faruwarsa ya riga da ya faru da ni. Duk abin da nake tsoron rasawa na rasa su kuma na ci gaba da rayuwa. Duk waɗannan nake tsananin so da ƙauna sun tafi sun bar ni irin tafiyar da babu waiwaye balle dawowa, rayuwa ta koyar da ni haƙurin dole da kuma juriyan ɗaukan duk abin ya faru da ni walau na shirya masa ko kuma akasin hakan. Don haka duk abin da kike ji a ranki game da ni kar ki yi shakkan sanar da ni da tunanin wai za ki ɓata min rai ko kuma na yi fushi". Tabbas zantukan sun sama matsuguni a cikin kwanyata sun yi zaman dirsham, jikina ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka tsoma ta a cikin ruwan gishiri. Na ƙare matse wayar a kunnena yayin da wasu hawaye suke zuba daga gefe da gefen idanuna. Babu abin da yake yi mini yawo a cikin ƙwaƙwalwata face maganganun da muka yi da Muhammad Taufik ɗazu. "Ki na ji na kuwa?". Tambayar da ya yi mini shi ya dawo da ni cikin duniyar zahiri. "Ina jinka kuma ina so na roƙi wani alfarma a gare ta". Tun kafin na rufe bakina ya ce"faɗi dukkan abin da kike buƙata, matuƙar bai fi ƙarfina ba to tabbas kin riga da kin same shi". "Ina so ka ba ni lokaci na yi tunani kuma na yi addu'o'i, kai a naka ɓangaren ka gabatar da abubuwan da suka dace wanda addini ya sharraɗanta a yi yayin nema. Sannan ina so har zuwa lokacin da zan gama kar ka ƙara yi mini wani maganan da ya danganci soyayya". Haƙiƙa na fahimci zantukan sun yi masa nauyi don sai da ya ɗauki tsawon lokacin kafin ya dawo mini da amsa cikin sanyin jiki. "Ban yi zaton wannan alfarman za ku roƙo amma sai dai ba na fatan zuwan ranar da za ki nema wani abu a waje ki rasa. Don zan yi kamar yadda kika buƙata in sha Allah zan ba ki cikakken lokaci ki yi duk tunani da addu'o'inki, kuma ba zan ƙara yi miki maganar soyayyar ba har sai ke da kanki kin buƙata hakan. Sai dai ni ma zan roƙe ki alfarman". Jikina a sanyaye na ce"ina jinka". "Ina so kar ki hana ni ƙiranki, kar ki hana ni ganinki, kar ki hana ni zuwa inda kike. Sannan inna ƙira ki ko ba za ki ce komai ba". Ba tare da wani dogon tunani ba balle nazari na ce"na yarda". "To ina godiya ranki ya daɗe, bari na bar ki ki kwanta ki huta. Sai da safenmu a tashi lafiya". "Allah ya kai mu". "Amin ya hayyu ya ƙayyum". Daga haka na katse ƙiran na rumgume wayar a ƙirjina tare da lumshe idanuna, na daɗe a haka kafin na tashi na fito na yi alwala na koma na je na yi sallan raka'a biyu na ɗaga hannuna sama zan roƙi Allah sai dai na kasa magana, da zaran na buɗe baki kuka ne kawai yake fitowa haka na kifa kaina a wajen ina tilawan karatun haddan da yake kaina, a wajen baccin wahala ya ɗauke ni. [12/25, 6:59 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ____________________________________ Page 7️⃣9️⃣ Washe garin ranar da ƙyar na tashi sa boda wani azababben ciwon kan da ya addabe ni idanuna ma ba na don buɗe wa balle na ga gilawan haske komai ƙanƙantansa. Tun safe ban fito daga cikin ɗaki ba ina kwance har sai da Anty Zulaihatu ta zo ta kana na tashi daga kwanciyan da na yi, na gaishe ta yayin da idanuna suke a lumshe, ta amsa mini cike da kulawa sa'ilin da take kai hannunta saman goshina ta ji ya ɗauki zafi garau tamkar garwashin da ke ƙasan tukuban tsire. Cike da kulawa da ya gauraye da lallashi gami da lallama ta soma faɗin"Amatullah me ya yi zafi ne haka alhalin shi ba wuta ba? Me yasa kike so ki jefa

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});