Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 46

Chapter 46

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bakinta ba. Na rusuna na yi mata sannu ta amsa mini tare da cewa"ki dafa min shayi ba na jin daɗin jikina ba zan iya cin komai ba". "To ranki ya daɗe". Na amsa da shi a taƙaice cikin bin umarni da girmamawa. Na wuce cikin kicin ɗin na dafa mata shayin da ta buƙata babu ɓata lokaci na kammala na kawo mata. Tana zaune akan kujera ta jingina bayanta jikin kujerar tare da lumshe idanunta ta dafe goshinta da hannayenta da hakan ya taimaka wajen fito da damuwar da take cikinsa ƙarara. "Hajiya lafiya kuwa kike?". Sai a lokacin ta buɗe lumshashshun idanunta na kuma fahimci lumshe su da ta yi ashe kuka take yi. "Subhanallahi! Kuka ku ma Hajiya me ya yi zafi haka?". Ta kawar da guntun hawayen da suke idanunta ta kai hannu ta amshi kofin shayin da nake miƙa mata, ta kai bakina ta yi kurɓa ɗaya ta ajiye a gefenta. Cikina a sanyaye na furta"ban san me yake dsmunki a cikin zuciyarki don sanin sirrin dake taskace cikin tsokar zuciya haƙiƙa wannan sai mahaliccinta, amma don Allah ku yi ƙoƙarin ki cire komai daga cikin ranki in sha Allah watarana komai zai wuce har ma ya zama labari". Sai da ta ɗau lokaci ba ta tanka mini har na faɗa tunanin na tsallake iyakata ta hanyar faɗa cikin abin da bai shafe ni ba kuma bai kasance hurumina ba. Har na cire rai da samun amsa daga gare ta sai kuma can na ji ta ce"Amatullah". "Na'am". Na amsa da shi cikin nutsuwa da kulawa. "Kin taɓa yin soyayya? Kin taɓa son wani irin son da kike ji tamkar ba za iya yin rayuwa ba tare da shi ba? Kin taɓa tsintar kanki cikin ƙangin so mai dabaibayi? Kin taɓa ɗaukar so da ƙauna kacukam kika ɗaura akan wani ɗa na miji? Kin taɓa yin soyayya mai zurfi da sarƙarƙiya?". Sai da na sauƙe numfashi mai nauyi kana na sama zarafin cewa"Ranki ya daɗe duk abubuwan da kika lissafa babu ko guda ɗaya da ya taɓa faruwa da ni. Hasalima ban taɓa yin soyayya ba a cikin rayuwata". "In dai abin da kika faɗa haka ne tabbas ba za ki taɓa fahimtar duk abin da zan bayyana miki ba, Amatullah so wani mungun abu ne. Wallahi ko maƙiyina ba na masa fatan Allah ya jarabce shi da makauniyar soyayya". "Don ban taɓa yin soyayya ba ai ba hakan ne zai sa na kasa fahimtar halin da kike ciki ba, sai dai na Hajiya ni na san ban kai na ji damuwarki ba amma in sha Allah na yi miki alƙawarin zan taya ki da addu'ar Allah ya kawo miki mafita da sauƙin halin da kika tsinci kanki a ciki". Ina dasa a zancen nawan na tashi na tattare kwanunkan da su Ayan suka gama cin abincin na kai kicin na wanke su, duk da ina jin yunwar kuma ina buƙatar na saka wani abu a cikin cikina, amma na kasa cin abincin sa boda yadda na ga Hajiya tana zubar da hawaye. Duk da ban san takamammen abin da yake damuwanta tare da yi mata ƙaiƙayi a cikin ranta ba, amma na tabbatar da cewar abin azimun. A lokacin yarinyatata duk macen da na gani tana rayuwa a cikin babban gida, tana saka suturar da take so sannan ta hau manyan mota. Gani nake yi tamkar a duniya dai kam ba da ta wani matsala kuma sun gama dace wa a cikin duniya sai dai a yi fatan dace wa a gobe ƙiyama. Ashe kallon kitse nake yi wa dogo, sai yanzu da hankali ya ratsa jikina ma fahimci ko wani Bawa da irin na shi damuwar kuma mai ɗaki shi ya san inda yake yi masa yoyo. "Idan tunanin za ki tsaya zauna kina yi ai da kin ui zamanki a can gida ba zai kin zo nan ba". Muryar Altine shi ya dawo da ni cikin duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da nake yi, ban ɗaga ido na kalle ta ba balle na ce da ita wani abu na tashi na je na rufe abincin na wanke hannuna na fita. Har yanzu Hajiya tana nan zaune inda na bar ta ba gusa ba wnda a iya tsawon kwanakin da na yi a cikin gidan. Na lura ba ta cika sama a falon ƙasan ba rai da rai yana sama indai ba wani abun ba ne ya sauƙo da ita ƙasa shi ma tana gama wa take kowa wa sama. Har na yi gaba zan wuce sai na ji ta ƙira sunan na dawo da baya na zo na durƙusa a gabanta kaina a ƙasa ina sauraron zancen da take yi cikin amo mai rauni. "Amatullah ki ba ni shawara na rasa da yadda zan ɓutowa wannan lamarin gabaɗaya kaina ya kule. Tunanina ya tsaya a waje guda cak". "Ranki ya daɗe ai ban san abin da yake damunki ba balle har na yi tunanin shawaran da ya dace na ba ki". Ta ɗan yi jim ta ce"haƙiƙa Allah ya jarabce ni da tsananin son mijina. Hasalima ni na fara ganinsa na ce ina sonsa har kuma Allah ya ƙaddara za mu yi aure su haifa Ayan da Aryan. Su biyu iyayensu suka haifa daga shi sai ƙaninsa Saifullah da muke zaune tare da shi a cikin gidan, ba su da wani dangin kusa illa junansu hakan ya sanya suke matuƙar ƙaunar juna. Mun yi aure da Saddam amma sai bayan auren na fahimci ya aure ni kawai sa boda ya sama wacce za ta taya sa sanya ido akan ƙaninsa kasancewar sa ba mazauni ba, tun da muka yi aure da shi bai taɓa yin sati guda cur a cikin gidan nan ba. Ya yi wuta shi ne ya zo ya yi kwana biyar ya koma daga nan kuma sai ya sanda ya ƙara waiwayo mana. Soyayyar Saddam ta rufe min ido ta hanyar ba na iya ganin aibunsa kuma ba na ganin laifinsa akan komai duk da kuwa ni ma kaina na san yana cutar da ni". "Hajiya ba kya tunanin cewa kuma yanayin aikinsa ne yake hana sa samun lokacin da zai zo gida? Kin ga fa ya wadata ku da komai na buƙatar rayuwa bai bar ku da yunwa ba, bai bar ku da ƙishi ba haka nan bai bar ku cikin tsumma ba komai na buƙatar rayuwa yana yi muku". Ta saki wani sakakken murmushi kafin ta ce"ba za ki fahimta ba. Duk waɗannan abubuwan da kika lissafa ba su ne jin daɗin rayuwar duniya mussamman a cikin gidan aure. Aure ba na mutum ɗaya ba ne na mutane biyu da ake buƙatar ko wani ɓangare ya ba da na shi gudumawar, ban yi dogon karatun addini ba amma iya sanin da nake da shi na san cewa ƙissan rayuwar Sayyada Khadijatu da Ma'aiki sallallahu Alaihi Wasallama, ita ta fara ganinsa ta ce tana sonsa sa boda ta yarda da shi kuma ta yi na'am da kyawawan halaye da ɗabi'unsa. Shin ni na yi laifi don na yi koyi da macen da tarihi ya tabbatar da cewar ta hidimtawa addini da ƙarfinta kuma da dukiyarta? Mene ne lafina don na gan sa na ce ina son sa

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});