Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 59

Chapter 59

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wai sai Abba da yake sanye da fararen kaya tas ya riƙe mini hannuna. Ya jijjiga mini kansa alamar kar na je, haka na durƙushe a wajen ina kuka ta na ta aikin lallashina. Shewa da ihun da na ji an saka a filin tsakar gidan shi ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga nisan zangon da na yi a cikin kogin tunanin da na faɗa. Na kai hannuna na kawar da hawayen da suka ɓata mini fuskana na yunƙura zan tashi na ga an shigo da ledan kaya cikin ɗakin. "Ledar nan fa, na wane ne?". Sha'awanatu da ta shigo da akwatin ta washe baki ta na kallona, don tun bayar faruwar wancan abun tsakanina da ita ta shiga taitayinta ba ita kaɗai ba ma har wasu daga cikin matan gidan, silar da ya sa suke shakka ta kenan. Mun ɗinke ni da ita don ta zama cikakkiyar ƴar fadata mai lasisi. Duk wani jagwal da ta taro yake neman girmewa lissafin ƙwaƙwalwarta ni take tunkarowa na warware mata shi sala-sala. "Ai Zinariya ce ta dawo yanzu haka ma ta na tsakar gida". Ba ta rufe bakinta na daka tsalle na tsallake ledan da ta shigo da shi ɗin, na fito tsakar gidan. Muna ganin juna ni da Zinariya habawa! Sai murna muka rumgume juna ana yaushe gamo. Na ja hannunta suka cikin ɗaki na zaunar da ita a bakin katifar ina faɗin"ke kuma da muka yi da ke ba za ki wuce wasu kwanaki ba. Kika je kika share waje kika yi zamanki. Ki ka bar ni nan cikin fargaba da zulumi". Ta ɗan murmuss tare da sadda kanta ƙasa kafin ta ce"dalili ne mai girma ya kawo hakan Amatullah, yanzu dai ba n ruwa na yi wanka tukunna don wallahi duk wani gaɓa a cikin jikina ciwo yake min". Kaina kawai na jinjina mata na ɗauki bokati na fita waje, ɗakin duk wacce na yi niyya da ra'ayi na faɗa na kamfato ruwa na yi fito babu mai ce wa da ni uffan tambaya na ba'asi. Na kai mata ruwan banɗaki ta shiga wankan na dawo na kallafawa duk wata wanda ta yi girki sai ta kawo mini plate guda ɗakina Zinariya ta ci ta yi haniƙan. Babu mai cewa da ni ko kanzil don na isa har na yi yawa, Hajiya Babba ma sai dai ta ganni ta jijjiga kaina don na zame mata ƙadangaruwar bakin tulu a bar ni na ɓata ruwa, a kashe ni a yi asarar tulu. Dole ƙanwar naƙi ta na ji tana gani sai idanuna ta kawo ta zuba mini. Sai da na bari ta yi wankan ta ci abincin, ta je ɗakin Hajiya Babba ta gaishe ta sannan ta dawo ta kwanta. Na zo kusa da ita na zauna na ce"na ta ƙiran layinki kullum a rufe, ga shi kuma yanzu na ga kin dawo babu waya a hannunki. An ya lafiya kuwa wannan tafiyar?". Kamar wacce na tsikara mata allura ko kuma wacce na sosa mata inda yake mata ƙaiƙaiyi ta yi zumbur ta tashi ta zauna tana fuskana. "Kin gan ni nan tsabar rashin hankalin da na shiga har ma na manta da wani abu a duniyar nan wai shi waya. Tun da na ba ro ofishin ƴan sanda da aka ba ni wayar na kashe ta na jefa a cikin ledan har yanzu da nake yi miki wannan maganar, ban sama nutsuwar da zan ɗauko ta ba". Cike da mamakin da ya bayyana har a cikin furucina na ce"sanar da ni abin da yake faru wa cikin gaggawa kar ki bari zuciyata ta buga. Don fargaba". Ta ja dogon numfashi kana ta soma zayyano mini zancen daki-daki wani yana bin bayan wani. "Na isa masauƙina a cikin babban otel kuma mafi tsada da tsaruwa a cikin garin Abuja, na ci mai kyau na sha mai kyau sannan na kwanta na yi baccin huce gajiya. Washe gari na shiga hidimar tarban Ogana da zai biyo jirgin yamma daga ingila zuwa ƙasa Najeriya. Ƙarfe shidan yamma ya ƙira ni ya shaida min ya iso har ma ya ɗauki hanyar zuwa otel ɗin da nake. Tabbas na cika da murna da har sai da ya sa ni na tashi na taka rawar daɗin jin kalamansa a gare ni. Ya Kawo min tsarabobi masu yawan gaske mun faranta ran junanmu a wannan ranar, sa boda mun yi marmarin juna sosai muna kwance da rana kwatsam na ji ana mana buga mana ƙofa. Lokacin bai tashi daga bacci ma don haka na tashi na je na buɗe ƙofar ina buɗe wa na ga wani Saurayi tsaye. Muka yi kallon-kallo da shi kafin na ce da shi Bawan Allah lafiya za ka zo ka na buga mana ƙofa? Waye kake nema?. Bai amsa min ba sai da na ga yana ƙoƙarin shiga cikin ɗakin na ƙi ba shi dama muka soma hayaniya da shi, da hakan ya sanya Ogana tashi daga baccin da yake yi ya zo shi wajen a nan na fahimci sun san juna ƙarshen sanayyana ma saurayin ƙaninsa ne na jini da suka fito daga ciki ɗaya. An yi rigima sosai sun yi musayar yawu da shi ainun na fusata na ɗauki kwalbar giyan da ya sha a daren jiya na je da nufi rotsawa saurayin a kansa ya zame na sama Saddam a goshinsa, take kwalbar ta tarwatse jini ya soma malala daga goshinsa take a wajen ya yanke jiki ya faɗi ba ya ko motsawa. Na gigice na rasa abin da zan yi kawai na ɗaura hannu a ka ina rusa kuka, ma'aikatan otel ɗin suka shigo su suka ƙira ƴan sanda suka zo suka tafi da ni aka rufe ni ban ƙara sanin halin da Saddam yake ciki ba sai da na yi kwanaki biyar cur a ofishin ƴan sandan kafin Saurayin ya zo shi a bakinsa nake jin mummunan halin da matar shi Saddam ɗin take ciki. Kuma ita ta buƙaci a yi min afuwa ta ƙara cewa idan halina ne wataran zan kai kaina inda ba zan iya fita ba, haƙiƙa na ji tausayinta ainun kuma na jinjina halin girma da dattakunta, ba ni da wani wajen da zan je haka nan ba ni da kuɗin da zan dawo gida sa boda ATM ɗina yan can ɗakin otel ɗin. Haka nan ma wayata ban san duniyar da take ciki ba". Ta tsagaita kafin ta ci gaba da cewa"da ƙafata na yi dogon tafiya har na isa gidan wata ƙawata da na muka haɗu da ita sanadiyyar bariki. Sai dai ita ta tuba har Allah ya kawo mata miji ta yi aurenta. A gidanta na zauna ta ba ni mafaka sa boda lokacin mijinta bayan cikin garin, a cikin gidanta na yi waɗannan tsawon kwanakin ina ta fafutukar yadda zan yi welcome back ɗin layina ko don kuɗaɗena da suke kwance a cikin akawuna. Da ƙyar hakan ya yiyu a cikin azurkinta ta taimaka ta ba ni ƙaramar wayar da na saka layin, ana cikin hakan mijinta ya ƙira ta a waya yake sanar da ita cewar yana hanyar dawowa lamarin da ya fara haifar da matsala a tsakaninmu ke nan, ta dade akan sai dai na bar cikin gidan don mijinta ba zai

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});