Chapter 20
Chapter 20
ji a cikin maƙoƙarona tamkar an shayar da ni ruwan maɗaci. Ina zaune cikin wannan halin Aminu ya faɗo cikin ɗakin ban ji shigowarsa ba sai ji na yi an zubo mini wani irin hayaƙi a daidai saitin fuskana take tari ya sarƙafe ni na soma yin sa babu ƙaƙƙautawa, da ƙyar tarin ya tsaya wanda hakan ya ba ni damar bin sa da idanuna yayin da yake zama akan tabarman da nake zaune, yana busa tabar sigari cikin ƙwarewa hayaƙin yana fita ta baki da hancinsa. "Tunanin me ye kike haka ƴan mata?". Na yi masa wani kallo ta wutsiyar idona kana na ce"amma ka san bai dace ka faɗo mini cikin ɗaki haka ba tare da sallama ko neman izni ba ko?". Ya ƙura mini idanuna tamkar ba da yaren Hausa na yi zancen ba"ban gane ba me ye kike nufi da waɗannan kalaman nakin?". Idona a cikin nasa na ba sa amsa"ina nufi bai dace ta na shigo mini cikin ɗaki haka garangatsau ba, ko ba komai wani lokacin akwai yiyuwar ka same ni cikin wani hali". "Wani irin hali ke nan?". Na galla masa harara tare da ɗauke idona daga kansa ba tare da na ba shi amsar tambayar da ya yi mini ba. "Ɗazu na zo ba kya nan ina kike je?". A taƙaice na ce"wajen aiki". "Aiki?". Ya maimaita cikin sigar tambaya na gyaɗa masa kaina cike da tabbatarwa. "Ina mai tabbatar miki da cewan babu wani aikin da zai riƙe ki balle har ki ɗauki ɗauwaniyyan kanki da shi. Amatullah ki buɗe idanunki ki farka daga baccin da kike yi da yake haddasa miki yin wannan mafarkin mara gindi balle tushe, kin san me ye bariki kuwa balle yadda ake gudanar da rayuwa a cikinta? Kin san yadda zaman bariki yake kuwa? To billahillazi duk wanda kike ga yana zaman kansa ko zaman kanka a cikin duniyar bariki sai ya yi da gaske kafin yake ɗaukan dukkan ɗawainiyyansa, a namiji ma ke nan balle kuma ɗiya mace da take rauni a bayyane. Kin ga duniyar bariki ya wuce duk yadda kike tunani kallon kitse kike yi wa goro, tun wuri idan za ki zubar da makamanki ki kama gaskiya da hanyar da za ta miƙar da ke ɗoɗar ki yi kafin lokaci ya ƙure miki. Ban da toshewar basira ina ke ina wani zuwa aikatau aikin da sai kin saka ƙarfi kin sadaukar da lokacinki wajen yin sa, yadda kike da kyakykyawan suran nan da diri mai kyau da ɗaukar hankali aikin wahala bai kamace ki ba, kamata ya yi a ɗauke miki komai sai dai kawai a kama miki ɗaki a ciyar da ke a shayar da ke duk abin da kike so. Ki ci mai kyau ki sa mai kyau. Ki sha iskan AC ki kwanta ki bi lafiyar gado". "Na gwammace na yi ko wani irin aiki da na bi hanyar da kake so ka ɗaura ni a kai". Ya yi wata dariyar da na kasa gano manufar da yake ɓoye a tattare da shi kafin ya furta"ina nufin ki ba da kai kawai bori ya hau. Kawai manyan masu kuɗi hamshaƙai da suka ci suka ta da kai, akwai ƴan kasuwanni, akwai ma'aikatan gwamnati, akwai masu aikin ɗamara, akwai ƴan siyasa, akwai manyan malamai da suka yi shura da suna a duniya, akwai waɗanda su ba ma a cikin ƙasar nan suke ba. Waɗannan su ne waɗannan ba su da matsala su hotunan wasu sassan jikinki kawai za ki ɗauka a hoto ki ki dinga tura musu yayin da su kuma za su dinga jiƙa miki account ɗinki da wasu mahaukatan kuɗaɗe masu nauyin gaske. Akwai hanyoyi da yawa da za ki bi don rufa wa kanki asiri ba tare da kin yi aikin wahala ba". Na kai hannuwana na toshe kunnuwana saboda yadda kalamansa suka jirkita mini tunanina har sun barazanar juyar mini da kaina. "Ba zan duk abubuwan da ka lissafa ba. Don na yi wa kaina alƙawarin ba zan ƙara aikata wani saɓon Allah a ciki sanina ba, sai dai wataƙila ba na cikin hayyacina amma da hankalina dai kam ba zan iya wannan abun ba". Ya sake baki da hanci yana kallona"hoton jikinki ne fa kawai za ki ɗauka ki na zauna daga cikin ɗakinki akan wannan tabarman ki turo, babu wanda ya san kin yi wani abu. Wannan ake yi wa kirari da cewar ka yi kyauta da damanka ba tare da hagunka ya sani ko ya ji labari ba". "Kar ka canza ma'anar maganar nan domin sam ba haka yake ba. Kuma ina so ka sani ba ka da wasu kalaman da za ka yi mini zai sa na karya alƙawarin da na yi wa kaina". A fusace ya miƙe yana jefa da guntun sigarin da ya gama zuƙa ya take ta kafin ya furta"shikenan ki yi yadda kike so. Daman Hausawa sun ce mai rabon shan duka ai ba ya jin bari, don haka ga fili ga mai doki sai ki yi sukuwarki yadda kike so". Tana dasa aya a nan ya fice daga cikin ɗakin na bi shi da kallo kamar idanuna za su faɗo a ƙasa, yana fita La'aniyatu tana shigo wa cikin ɗakin kamar zai bangaje ta ya ƙarisa ficewa cikin ɓacin rai. "Lafiya na ga wannan ya fita cikin ɓakin rai kamar zai duki bango?". Ta jefa mini tambayar yayin da take zauna kusa da ni. Sai da na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kana na furta"ba komai kawai dai abin da aka saba ne wanda kin riga da kin san shi". Ta jinjina kanta"Allah ya kyauta". "Amin, na ga ɗazu kaman ranki a ɓace me yake faruwa ne?". Ta ɗan yi jim kafin ta ce"wallahi Ummata ce ta yi mungun ɓata min rai, sai da na ji kamar na ɗaura hannu akaina na yi rafza kuka tsabar tsagwaron baƙin cikin da ta ƙunsa min". Cike da mamaki game da buƙatan ƙarin bayanin da ta yi mini a dunƙule na ce"me ye ta yi miki haka?". "Wai fa baƙi ta yi ta san da cewa ina cikin ɗaki ina saka kayana ta shigo da su. Wallahi na ji haushi sosai ta yadda ban ma san lokacin da na rufe ta da masifa ba". Cike da maɗaukakiyar mamaki na waro idanuna waje"Umman nakin kika rufe da masifa?". "To mene ne?". "Ai ita ɗin mahaifiya ce ko me ye ta yi miki bai dace ki rufe ɗaga mata murya ba balle har ki rufe ta da faɗa. Iyaye fa suna fa su na da wani irin daraja da kima wanda ba kowa yake da makamancinsa ba, mussamman uwa wanda sai Annabi ya ambace ta sau uku kafin ya ƙira uba sau ɗaya saboda girman haƙƙin da take da shi akan ɗa". Ta ɗan yi shuru kamar abin da na faɗa ya ratsa ta sai dai kuma kalamanta suka sani tabbatar da cewa duk abin da na faɗa ya shiga ta kunnenta na gefen dama ne ya fita ta gefen hagu. "Ummanta dole sai ana yi mata haka, dole sai mutum ya zama jan wuya mai iya ƙwacen haƙƙinta kafin ya iya zama da ita. Akwai wani lokaci da ta tsiri kawo maza cikin ɗakinmu su hana n
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98