Chapter 65
Chapter 65
rayuwar mahaifinki? Mahaifiyarki kuma ta sallamaki ga duniya?". Ta watsa miji tambayoyin a dunƙule kuma a lokaci guda, sai da na ja dogon numfashi mai nisan zangon kafin na sama zarafin warware mata tsakanin zare da abawa, babu abin da na ɓoye mata game da gurɓataccen tarihin rayuwata na sanar da ita komai ba tare da na rufe wani abun ko na kwaskware shi ba. Tun da na soma ba ta labarin take zubar da hawaye har na kai aya ina ƙarewa da faɗin"to yau dai kin sauraru tarihin rayuwata kin san wace ce ni...". Ba ta bar ni na ƙarisa ba ta rumgume ni duk mu biyu muka tuntsire da wani irin kuka mai matuƙar cin rai da azabtar da ruhi. "Tabbas bakin uwa masifa ne ga ƴaƴanta abin da da yawa-yawan iyaye matan wannan zamanin ba su fahimta ba ke nan. Kaifin harshen Ummanki akan ki shi ne abin da yake bibiyar rayuwarki Amatullah, shi yasa ake ce wa DAFIN HARSHE ya zarce dafin maciji cutar wa da gurɓata duk wani abun da ya soma baki a ciki". Ban iya amsa mata da kalmomin da baki kan iya furtawa ba sa boda nauyin da bakina ya yi mini, harshena ya cika mini bakina da hakan ya taka rawar ganin wajen hana maganata fita. Deeno ne ke ta ba mu haƙuri har muka tsagaita da kukan da muke yi lokacin har ƙarfe biyar ɗin asubahi ya yi har an fara haramar ƙiran sallan asubahi. Na tashi na shiga cikin banɗakin da take cikin ɗakin na yi alwala na zo na gabatar da sallan a zaune sa boda gabaɗaya jikina babu ƙwari, ba na zato da tunanin ƙafafuna za su iya jure ɗaukar nauyin gangar jikina. Ko da na iddar da sallan na yi dogon addu'an kafin na tashi daga wajen lokacin kusan ƙarfe shida saura, muka fara haramar tafiya Deeno ya kawo mana face mask ya ce mu saka haka kuwa muka yi muka saka kafin muka fito muka yi sallama da Deeno muka hau adaidaita zuwa gida, tun da muka shiga ban ce komai ba illa lumshe idanuna da na yi ji na nake yi tamkar majinyanci don ba na iya aikawatar da komai. Ko da muka iso gida sai da Zinariya ta taɓo kafaɗuna kafin na ankare da cewar mun iso na sauƙa, ta miƙa masa kuɗinsa ya ja napep ɗinsa ya bar wajen, Zinariya ta kallo ni tare da cewa"wannan damuwar duk na mene ne Amatullah? Na yi tunanin tun da yanzu kam kin cika burinki ai komai ya zo ƙarshe babu abin da ya dace da ke face farin ciki da kuma murna cikar muradinki". "Ni ma kaina hakan na yi tsammani sai dai ban san dalilin da ya sa na tsinci kaina cikin wannan damuwar ba". Cike da ƙarfafawa ta ce"mu shiga ciki ki huta, da yardan Allah yanzu kam komai ya zo ƙarshe". Ta riƙo hannuna muka shiga ciki kai tsaye ɗakinta muka nufo ta buɗe mana ƙofar muka shiga ciki, a nan ɗin ma kwanciya na yi na rufe jikina ruf sa boda yadda nake jin wani sanyi yana ratsa jini da gaɓoɓin jikina. Ina kwance na ji Zinariya na magana. "Ki tashi mu je wajen Hajiya Babba ki yi mata wannan babban albishiri ɗin, ina da tabbacin ita da kanta ma sai ta sara miki balle kuma fadawan natan". Furucinta ya tilasta mini yaye bangon da na lulluɓe har kaina da shi sai a lokacin na ga har rana ta fito ta dalle ko'ina da haskenta. Na yi miƙa haɗe da faɗin"wai har gari ya waye haka?". "Tun yaushe kuwa, yanzu fa kusan ƙarfe goma ake nema ba". Na waro idanuna waje cike da mamaki na tashi daga kan katifar ta miƙo mini wayar na amsa muka nufi ɗakin Hajiya Babba tare. Tana kishingiɗe muka iske ta muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu yabo babu fallasa. Kafin mu ce komai ta tare mu da faɗin"ina fatan dai ki na lissafin ragowar kwanakin da suka rage miki ko?" Na kaɗa ina murmushi kana na furta"ai in sha Allah ma daga yanzu duk wani lissafi ya ƙare, yau na zo gabanki da cikakkun shaidun da za su tabbatar miki da cewar duk wani alwashin da na yi na cika sa tsaf". Na lallasa wayar na shiga fegin hotunan da muka yi na miƙa wayar ta sa hannu ta amsa tana kallo sai da ta kalle su tsaf kafin ta ce"amma ai satan ɗaukar hoton aka yi tun da gashi ma kwance yake yana bacci, aka yi hoton". "Hajiya idan kin tuna a cikin yarjejeniyarmu ba ki gindaya mini sharaɗin cewar sai na farke zan yi hoto da shi ba, don haka ko yanzu aka tashi tabbas ni na ci wannan wasan". Ta ɗan yi shuru ta na ta ƙare wa hoton kallo kafin ta ce"wannan hoton anya kuwa ba haɗa wa aka yi ba?". "Hajiya ki dai ƙara duba wa sa kyau". Zinariya ta ba ta amsa, wayarta ta ɗauka ta ƙira Aminu ta ce duk inda yake ya zo yanzu ta na son ganinsa, ya kuma amsa mata da cewar ga shi tafe daman ba nisa ya yi ba. Cikin ƙasa da mintuna ashirin ya bayyana a cikin ɗakin ta miƙa masa wayar ta na faɗin"karɓi ka duba hoton nan ka gane min haɗa wa aka yi ko kuma na gaske ne". Na amshi wayar yana kallon hoton tare da yin zooming ɗinsa ciki da waje, sai da ya gama ƙure basirarsa kafin ya ce"billahillazi Hajiya wannan hoton na gaske ne ba haɗa wa aka yi ba, sannan ba aikin AI ba ne wannan na'urar zamani mai ƙwaƙwalwar nan. Wannan hoton na gaske ne". Ya mayar da idanunsa kaina. "Tabbas kin cika mai cika duk wata maganar da ta furta kin kuma cancanci a jinjina miki bisa wannan na mijin ƙoƙarin da kika yi, yanzu kam ai sai ki kama harka babu kama hannun yaro ko?". Na ɗan murmusa kafin na ce"ina buƙatan lokaci na yi tunani akan hakan, kafin na fara aiwatar da komai". "Duk yadda kika ce haka za a yi ranki ya daɗe. Amatullahi mai abin mamaki ga sani fal ga kuma shagala". Duk mu ukun muka yi dariya ban da Hajiya Babba ta da murtuƙe fuskarta tamkar magribar ɗinya ta soma faɗin"akwai wasu maza biyu da suka zo neman ki jiya cikin gidan nan in taƙaice miki bayani a jiyan kawai sai da suka zo sau kusa biyar. Na shaida musu cewar ba za ki kwana a gida ba jiya ki na can otel don haka su dawo yau da misalin ƙarfe biyu na rana, don haka sai ki shirya tabar baƙi. Duk da ma dai na ga ba wani tsiyar ba ne a tare da su". Ban kawo komai a cikin raina ba don na ɗauki zantukan natan kamar ƙidan shata don haka na ce"Allah ya kawo su lafiya ina nan ina jiran su". Da haka muka yi mata sallama muka koma ɗakinmu Zinariya ta yi mana girki muka ci na kwanta bayan na sha maganin zazzaɓi da na ciwon kai take bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ni ba ni na tashi ba har sai da aka yi sallan zuhur, Zinariya ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98