Chapter 38
Chapter 38
da farko gida na yi niyyan wucewa amma yadda na ga Altine ta ɗaura idonta a kaina ya sa ni sauya shawara, na je wajen Baba Mai gadi na zauna. Ta fi mintuna goma sha biyar a tsaye a wajen ita ba ta yi gaba balle baya tana ta aikin banko mini harara tamkar ƙwayoyin idanunta za su faɗo ƙasa. "Lafiya kuwa yau me ye yake faruwa tsakaninki da uwar-gijiyartakin?". Furucin Baba Mai gadi ya dawo da ni izuwa cikin duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na afka na wucen gadin. "Babu komai Baba, daman wajenka na zo neman wani taimako". Ya gyara zamansa yana fuskantana da kyau da hakan ya ba ni ƙarfin gwiwa da karsashin ci gaba da zancen. "Akwai wani babban malamin addini da ya yi shura a gefensa kuma sunansa ya ɗaukaka ya zagaye ko'ina a cikin ƙasar nan har ma da kewayenta." Tun kafin na dire zancen ya katse mini hanzari ta hanyar faɗin"wannan ba kowa kike magana a kansa ba fa ce baƙin Balarabe". "Anya kuwa shi ne? Wannan ɗin fa sunansa Sheikh Dawood aka yi masa kirari da gaskiya dokin ƙarfe". Ya murmusa kafin ya furta"ai mu a nan cikin jarafi an fi sanin sa da sunan baƙin Balarabe. Yana zuwa tafsirin alƙur'ani sosai a cikin garin nan. Ina tunanin babu garin da ya tara masoya fiye da wannan garin namun indan ya zo hatta mai martaba Sarki dakatar da komai yake yi ya je ya saurari wa'azinsa, kusancin da yake da shi da mai martaba ya sa shi ba shi auran ƙanwarsa ƴar autarsu ya aure ta sai dai ta rasu shekaru biyu da suka wuce, mutum ne mai tarin ilmin addini har ma da na zamani don na taɓa jin an ce yana shugabanci a wata jami'a". "Don Allah Baba kaman da wani irin lokaci yake zuwa garin nan ɗin? Sannan in ya zo yana yin kamar kwana nawa kafin ya tafi?". Sai da ya kalle ni kafin ya ce"yana iya zuwa a ko wani lokaci sai dai ta fi zuwa a lokacin sanyi kamar irin yanayin da muke ciki yanzu. Sannan idan ya zo yana gabatar da wa'azi a wurare daban-daban kuma a mabanbantan lokuta hatta wa'azin mata yana gabatarwa a masallacin Sarki". Na ɗan yi jim kafin can na ce"shin ko yana da wani alaƙa ne tsakanin shi da wannan baƙon da ya zo cikin gidan nan?". "Wai Sultan?". "Sultan kuma?". "Ƙwarai da gaske sunansa Sultan don tun sanin da na yi masa haka ake ƙiransa da shi. Amma asalin sunansa Muhammad". Mamakin zantukansa suka gana ni samun damar cewa komai illa sadda kaina ƙasa da na yi ina tufka da warwara a cikin raina. Ta ya ya Muhammad Taufik ɗin da na sani zai ya rikiɗe ya koma amsa sunan Sultan?. Sannan me ye haƙiƙanin alaƙarsa da Sheik Dawood da har na ga hoton su tare? Hoto ne da aka yi shi cikin lokacin zallan farin ciki da annashuwa da har ya bayyana akan fuskokinsu. Kuma a cikin gida aka yi sa balle ma na ce a wajen gabatar da wa'azi suka haɗu aka yi hoton. "Amma ƴar nan lafiya kike ta yi min wannan tambayoyin?". "Lafiya ƙalau Baba, tun ranar da na ga wannan baƙon ne na ga suna kama da shi Sheikh ɗin to shi ne nake ta tunanin ko sun haɗa jini da shi ne. Ko wani dangantaka ta kusa ko ta nisa?". Na ƙarƙare zancen cikin sigar jefa masa tambaya a faƙaice. "Ban ma taɓa lura da kaman da suke yi ba sai yanzu da kika furta nake zumo kamar a idanuna. Sultan dai kam abokin Saifullahi tun na ƙuruciya wani sa'ilin ma a nan cikin gidan suke ƙarar da hutun makaranta, ban taɓa jin labarin akwai alaƙa tsakaninsa da Sheikhi ta kusa ko ta nisa ba. Na san dai Sheikhi yana da azurki ƴaƴa sai da mafi yawansu mata ne ɗansa na miji ɗaya ne tal kuma bai cika bayyana fuskarsa ba". "To shi Sultan bayan abokan da yake tsakaninsu da Saif su na da wani alaƙa da masu gidan nan ne?". Kallon da ya watsa mini ya sani tabbatar wa kaina cewar na kwafsa kuma na wuce gona da iri har ina ƙoƙarin tsallake iyaka ba tare da na farga ko na ankare ba. "Wannan irin tambayoyin ƴar nan sai ka ce ina gaban alkali". Na murmusa kafin na ce"yi haƙuri Baba kawai na ga kamar ta sun ne ta yi tsananin yawa shi yasa nake tambaya". "Ba laifi kika yi don kin tambayi abin da ya shige miki duhu ko ya jefa ki cikin shakku ba, ai magabata sun ce tambaya mabuɗin ilmi ce. Sai dai a wannan gaɓar zan iya ce miki ba ni da amsar ko guda ɗaya daga cikin tambayoyin da kika yi min hasalima yadda kike gan sa a cikin gidan nan ya zo, ni ma haka nake ganinsa tun yana yaro ban taɓa damuwa da na san mene ne alaƙarsa da masu gidan ba don wannan ba hurumina ba ne kuma bai shafe ni ba". Na jinjina kaina cike da gamsuwa da zantukansa da dukkan suke kan gwadaben gaskiya. "Haka ne kam Baba to Allah ya kyauta". "Amin ya Allah". "Zan nem takarda da biro na zo ana ɗaura mini darasi. Ko gaisuwa ya kamata na koya daga cikin yaren nan tun da ban iya furta ko kalma guda a ciki ba". Ya dara sosai kafin ya ce"ba girin-girin ba dai ta yi maiƙo, kullum haka kike ce har na gaji da gafara sa ba tare da na ga ƙaho ba". Kafin na kai ga cewa wani abu Aryan ya iso wajen. "Wai ki zo in ji Umminmu". Haka kawai na ji gabana ya faɗi zuciyata ta buga da ƙarfi. Jikina a sanyaye na ce"lafiya?". Ya ɗage mini kafaɗunsa alamar bai sa ni ba daga haka ya dura da gudu ya koma ciki. "Tashi ki je ƴar nan kar ki yi sanya don ba a bori da sanyin jiki". Kaina kawai na gyaɗa masa na tashi na nufi cikin gidan ba tare da na san abin da zan je na tarar a ciki ba. Ina doso cikin falon idanuna suka soma sauƙa aka fuskar Altine da take zaune kusa da ƙafafun Hajiya Muhibbat gefe guda kuma Aryan da Ayan ne suke wasan mota. Na durƙusa kana na ce"Barka da hutawa Hajiya, ga ni an ce ki na nema na". Ta ɗau lokacin kafin ta ce"me ya kai ki wajen mai gadi?". "Hajiya gaisawa kawai muke yi da shi, sai kuma yaren kanuranci da na roƙi ya dinga koya mini kasance yarena ne kuma nan yi ba". Ta ɗan yi shiru kafin ta ce"to ba na son na ƙara ganin kin ce wajensa ko da wasa ne kuwa, ki yi aikinki shi ma ya yi nasa". "In sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa za a kiyaye". "Good". Ta amsa da shi a taƙaice, jikina ya yi sanyi ƙalau don na kasa gano inda maganganun natan suka dosa da kuma abin da take nufi da kar na ƙara zuwa wajensa ko da kuwa da wasa ne. "Hajiya rana tana yi me ye za a girka ne?". Furucin da Altine ta yi kenan da ya tilasta mini
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98