Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 72

Chapter 72

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba ta zauna da kowa zaman lafiya a cikin gidan nan ba. Ni ce kawai ta zame min dole ni ma ɗin kuma na fara gajiya tun da daman Ubangijinmu ne ai kawai ya ba ya gajiya da mu Bayinsa". Ji na yi kaina ya yi mini dum jikina gabaɗaya ya ƙara sake wa, wani baƙin duhu da babu ko da ɗigon haske a cikinsa ya gilma ta cikin idanuna. Duk da idan zaune ji na yi kamar ina shirin faɗuwa ƙasa, hakan ya sanya ni yin zaman ƴar bori dirshan a ƙasa. Na juyo da kaina ina kallon fuskar Umma da tun da Umman Amira ta soma zancen ta yi ƙasa da idanunta hawaye su na ci gaba da zuba daga gare su. "Umma me yasa kika zauna haka har jinyar nan ta yi nisa, ba tare da kin nema maganinta ba"?". Kafin ta ba ni amsa Umma Amira ta yi caraf ta amshe zancen cikin faɗin"to ke kuwa Amatullah jinya ba dole sai da kuɗi ba, to haka kawai ake tashi a nema maganin ba tare da ko sisi ba?. Ko wancan aikin yanke ƙafan da aka yi Alhassan ɗan Gwaggonki da yake su ma ƴaƴan kirki ne irin albarka da suka kwankwaɗi tarbiyya a cikin kofin girmamawa shi ne ya yi ƙundunbala ya biya kuɗin aikin da na magungunan da aka rubuta haka nan ya yi mata siyayyar kayan abinci ya kawo, shi nake ɗan tsakura ina dafa mata har zuwa wannan lokacin da kika zo kika iske ta tana numfashi". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Na furta cikin wani iriyar muryar mai tattare da tarin rauni saka kaina tsakanin tafukan hannayena tare da rushewa da wani matsanancin kuka mai tsanani. "Ba kuka za ki yi mata ba Amatullah addu'a za ki yi mata Allah ya kawo mata sauƙi da mafitan halin da take ciki. Idan kuma wannan jinyar ba na tashi ba ne to Allah ya sauƙaƙa mata tafiyar ya sa can ya fi mata nan kasancewa alkhairi a gare ta. Ki tashi ki fito waje ki ɗan sha iska don warin cikin ɗakin nan babu makawa sai ya kumbura miki ciki, ko kuma ya haifar miki da wani cutar mai zaman kanta". Umma Amira ta yi zancen ta na kai hannunta ta rufe hancinta tare da juya wa ta fice daga cikin ɗakin. Na tsinkayo amon Anty Zulaihatu cikin rarrashi ta na cewa"ba kuka za ki yi ba Amatullah addu'a za ki yi mata, sannan kuma a fara neman mafitan nema mata lafiya. Wanda daman akan hakan ki ka zo ki ka same mu, akwai wasu gidauniyar da suke ɗaukan nauyin majinya mussamman masu irin lalurarta a yi musu aiki kyauta, magani ma kuma kyauta. Tunin Yaya Alhassan ya saka sunanta kuma in sha Allah akwai cikakken yaƙinin cewar za a dace don haka ki kwantar da hankali komai ya yi farko zai yi ƙarshe da iznin Allah". Ban iya cewa da ita komai sa boda kukan da ya gama galabaitar da ni ainun, rurin da wayarta ya yi shi ya tilasta mata tashi ta fita daga cikin ɗakin don ta amsa ƙiran, ban ga laifinta don ta fita ba don tabbas zama ciki ɗakin sai ka kai zuciyarka nisa kuma sai hakan ya zama dole a gare ka watau ba ka da wani zaɓi. "Amatullah". Umma ta ƙira sunana da hakan ya sanya ni ɗaga kai ina kallon fuskarta, ta riƙo hannuna ta sanya cikin na ta. Hawaye suna gudu a bisa kuncinta ta ce"Amatullah kin ga yadda rayuwa ta yi da ni ko? Tun bayan rasuwar Manniru nake ta haɗuwa da jarabawa kala-kala daga wannan sai wannan kamar wacce aka saka wa hannu a cikin lamarin. A da na yi zaton barin sa cikin duniya zai ba ni wani dama ne da zan ci duniyata da tsinke sakace ta yadda zan sakata na kuma wala sai dai ashe kallon tsire nake yi wa rogo, na wofantar da ke sosai na ƙunsawa dangin Manniru ƙunci da baƙin ciki ba wai don ba na ƙaunar ki ba. Duk abin da na yi na yi sa da nufin ƙuntatawa Sawwama da kuma ƴaƴanta sai dai ban sani ba ashe wuƙa na ɗauka na daɓa wa kaina ba tare da na sani ba rashin Manniru ya sa ni fahimci komai isa, izza da taƙamar mace dole ta na buƙatar jagorancin na miji a cikin rayuwarta. Rashin Manniru ya sa ni na fahimci dole akwai wasu buƙatun da komai gata da azurkinki a cikin duniya ba za ki taɓa iya biya wa kanki su ba, rashin Manniru ya sa ni na fahimci duk macen da take zaune ba tare da wani tsayayyen na miji a cikin rayuwarta ba walau uba, miji ko kuma ƴaƴa to ita da hanyar Zamfara ɗaya suke a ɓangaren rashin tsaro. Amatullahi tun da wannan jinyar ta same ni babu ranar da garin Allah zai waye ba tare da na yi kukan rashinki ba lokuta da yawa na kan zauna na yi tunanin a wani irin hali na jefa rayuwarki a cikin yanzu? Tabbas Manniru ya yi gaskiya da ya ce DAFIN HARSHE ya fi dafin da ke tattare da bakin maciji da duk wani dabba mai cutarwa ga lafiyan ɗan Adam, mussamman kuwa bakin uwa don kamar yadda duk addu'ar da ta yi wa ƴaƴanta Allah yake amsar sa haka nan idan ta furta mummunan kalma gare su, sai hakan ya yi tasiri akan su ko ba daɗe ko ba jima ƙarshe kuwa ita za a bari da cizon ɗan yatsa. Kowa ya juya min baya a cikin gidan sai dai daidai da rana ɗaya ban taɓa ganin laifinsu bisa hakan ba tun da ni ma a lokutan baya ban rangwanta musu. Idan na ga yadda ƴaƴansu suke yi musu hidima ko da kowa hidimar aikace-aikacen cikin gida ne sai na ji hawaye su na zubo wa daga cikin idanuna tunaninki da na halin da na je da rayuwarki a ciki sai ya dawo min sabo dal a cikin raina". Dole ta tsagaita sa boda tari mai ƙarfi da ya sarƙafe ta, lokaci guda ya fitar da ita daga cikin hayyacinta. Na ɗauki kofin da yake na zaba ma da gudu waje da nufin ɗebo mata ruwa, har na buɗe rangan zan ɗebo ruwan na ji an riƙe mini hannuna. "Kar ki sake ki haramta min ruwan da nake sha kuma nake ibada da shi, ta hanyar soma min wannan ƙazamin kofin marar tsafta da ya fito daga cikin ɗakin wulaƙantacciyar matan can da ba ta san mutuncin ɗan Adam ba". Cak! Na tsaya ina bin matar da kallo don a tsawon zamana a cikin gidan ban taɓa ganin fuskarta a cikin gidan ba, ko da kuwa a zuwan baƙunta ne. Muryata ta na rawa na ce"don Allah ki yi haƙuri ki ba ni ruwan nan ko kaɗan ne, na kai mata ta sha tari ya sarƙafe ta ga shi nan ma ki na jin sautinta". Na ƙare zancen wasu hawayen su na gudu a fuskana. Tsaki ta buga mini tare da sa dukkannin ƙarfinta ta ture ni Allah ya rufa mini asiri ban kai ƙasa ba ta rufe rangan kirif, ta tsaya a wajen tare da riƙe ƙugu tana jijiigawa. Numfashi mai

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});