Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Chapter 57

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mu'amalar da aka ƙulla komai ƙarko da daɗewansa. Sai da na yi nisa na nema ƙasan wani bishiya na zauna na ci kuka na yi kuka na zubda ƙwalla tamkar raina zai fita. Komai ya fita daga cikin kaina na rasa inda zan nufa na ji daɗi da sanyi a cikin raina. Duniyar da abubuwan da suke cikinta gabaɗayansu suka daina burge ni balle su ba ni sha'awa. Ba don ilmin addini da nake da shi wanda ya yi matuƙar tasiri a gare ni har yake bayyana kansa cikin aikina ba, da kuma hukunci da azabar da na san Ubangiji ya tanada ga duk Bawan da ya kashe kansa ba da babu abin da hana ni shan guba ko kuma na rataye kaina, na huta ba. Zafin ranar da yake duka na shi ya tursasa mini tashi daga wajen ba domin na gaji da kukan da nake yi ɗin ba. A tashi na ci gaba da tafiya ina tafe ina haɗa hanya tamkar ƴar mayen ta sha abubuwan gusar da hankali ta bugu ta yi tatil. Ikon Allah ne kawai ya kawo ni gida ba domin na san inda kaina yake ba, balle ina nake cilla ƙafata a buɗe na tarar da ƙofar ɗakin da hakan ya tabbatar mini da cewar Sha'awanatu tana ciki, ina shiga na gan ta zaune tana latsa waya ta kuna kiɗa tamkar za ta ɗaga ɗakin, mu na haɗa ido da ita ta kashe kiɗa ta soma bi na da kallo har na je kwanta akan tabarmata. Na dafe kaina ina ta murtsukuku sa boda tsananin azabar ciwon kan da ya rufe ni lokaci guda ko buɗe idona ba na ƙaunar yi balle na ga haske, ina jin Sha'awanatu na tambayata ko lafiya na yi banza da ita ba tare da na tanka mata ba har ta yi ta gaji ta koma ta ci gaba da harkokinta. A daddafe na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da sallan zuhur ina shafa addu'ar da na yi na tsinkayo muryar Zinariya ta na faman ɗura ashariya a tsakar gidan, wanda ban zan da wanda take yi ba. Na yi wuf na tashi na fito daidai lokacin da ta buɗe ƙofar ɗakinta ta shiga na bi bayanta, ta waigo tana kallona. "Har kin dawo ke nan yau da wuri haka?". Maimakon na ba ta amsa sai kawai na tuntsire da kuka har jikina yana rawa. Ta saki ledodin siyayyar da ta yi a kasuwa suka faɗi ƙasa ta riƙo hannuna muka zauna. "Kukan me ye kike yi Amatullah? Sanar da ni abin da yake faruwa?". Ban yi ƙasa a gwiwa ba na kwashe duk abin da ya faru na sanar da ita. Sai dai ban fayyace mata cewar Hajiya Muhibbat ita ce matar Saddam wanda take yi wa take da Oganta ba. "Kan bala'i bura uban can. Yau ina ga ni wani zallan rainin wayo da ɗiban albarka. Kuma ke sai kika tsaya kika zuba musu ido su na jifanki da waɗannan kalaman? Ai fito na fito za ki yi da su ki nuna musu ainihin kalar taki salon barikin. Na rantse sai na dira a cikin gidan matar nan tamkar sauƙar aradu na yi wasan kura da ita sai na nuna mata cewar lalle da ruwa ake dafa shayi kuma bakin rijiya bai kasance wajen wasan makaho ba, tashi mu je ki kai ni gidan". Ta yi zancen yayin da take miƙe wa tsaye. "A'a Zinariya ba za a yi haka na ƙudurce a cikin raina cewar ba zan ƙara wuce wa ko da ta ƙofar gidan ba ne balle na shiga cikinsa. Na ri ga na yi musu bayannin komai". A kufule ta ce"waya gaya miki yanzu bayani yana tasiri ga mutane? Ai duk yadda kika ƙware wajen iya tsara kalaman da gogewarki wajen furta su daki-daki, wasu mutanen ba sa fahimta sai kin haɗa musu da akuyanci a cikin lamarin. Ki yi wa girman Allah ki tashi mu je gidan matar nan na ƙaddamar mata". Na tashi tsayi na riƙo hannunta"don Allah ki taushi zuciyarki ki yayyafa mata ruwan sanyi, mu bar maganar nan ta wuce. Na sanar da ke kawai don na ji sanyi a ciki raina ba don wani abun ba". Ba ta ce da ni komai ba illa zare hannunta da ta yi daga cikin na wa ta koma mazauninta ta zauna, ta yi ƙwafa kana ta ce"billahillazi don kawai zan yi tafiya ne shi yasa zan lafa bayan hakan ban dalilin da za ki ce kin bar wannan maganar ba". Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya tare da faɗin"gobe za ki tafi Abujan ko?". "Da sassafe ma kuma Ogana kuma jibi da yamma zai diro najeriya, a ƙalla za mu iya yin sati guda tare". Na waro idanuna waje"kika ce hutun ƙarshen mako kawai za ku yi tare ki dawo?". Ta yi fari da idanunta"e amma yanzu lissafin ta sauya kai tsaye ba zan iya ce miki ga ranar dawowa ta ba, sai dai ranar da Allah ya nufa kawai za ki ganni. Zan bar miki makulin ɗakina akwai ragowar kayan abinci ki yi amfani da su. Sannan don Allah ina son kafin na dawo ki sauya daga wannan Amatullah ɗin da take zaune a gabana yanzu, ina son duk wanda ya ɗaga miki ƴatsa ki tabbatar kafin ya sauƙe ta kin karya ɗan tsayan, kin ga harkar bariki fa babu wanda zai zo don ya taimake, ya kawo miki agaji ko kuma ya ƙwata miki haƙƙinki. Yaƙi ne da babu wanda zai tallafa miki ke za ki tashi ki yi wa kanki yaƙin neman ƴancin kai". "In sha Allah ba zan dawwama a haka ba ni ma, dole akwai lokaci ya na zuwa wanda zan sauya". Ta murmusawa"yauwa ƴar gari yanzu na ji batu". Daga haka ta ɗauki ledodin siyayyar da ta yi ta soma nuna mini, magungunan mata ne da na matsi birjik iya ganin mai gani. Daga na turare sai na tsuguna da na sha da kuma na ci da kaza. Ta sayo mini wasu dogayen riguna da mayafai ta ba ni, bakina har kunne na din ga doka mata godiya tamkar zan yi aron baki. A nan ɗakinta na yi sallan isha'i muka ci abinci, ita take gulmata mini cewar Hajiya Babba ta tura La'aniyatu can ƙasar nijer wajen wata aminiyarta don a ba ta horo a kuma koyar da ita kwasa-kwasan bariki don a cewarta so take yi ta gaje ta ta ɗaura daga inda ta ja birki. Ba kaɗan ba lamarin ya taɓa ni tausayin La'aniyatu ya mamaye zuciyata ni shaida ce akan cewar ba ta ƙaunar irin rayuwar da mahaifiyata take yi, balle daidai da rana guda ta ji sha'awarsa a cikin ranta. Ba ni na baro ɗakin Zinariya ba sai ƙarfe sha ɗaya dare, lokacin ta gama haɗa kayanta tsaf domin tafiyar gobe. Ta rako ni har ƙofar ɗakinmu muka yi sallama don ta tabbatar mini da cewar ƙarfe ukun dare za a zo ɗaukarta za su wuce garin Kano inda daga nan za ta kai jirgin safe da zai tashi daga cikin filin tashin jiragen sama na cikin jihar Kano zuwa garin Abuja, ta ɗauki makulin ɗakin ta damƙa mini na yi mata fatan sauƙa lafiya kana na shige ɗakin.

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});