Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yanayinki ya sauya?". Kalaman La'aniyatu ya dawo da ni cikin hayyacina. "Babu komai kawai wani abun na tuna. Na gode da kulawarki a gare ni, mu tashi lafiya". Murmushi kawai ta sakar mini ba tare da ta ce da ni komai ta tashi ta fice. Na zauna na yi jigum ina ta tunanin abin duniya, wasu hawayen masu zafi suka ciko mini kurmin idaniyata, na tuna Umma lokacin da ta yi watsi da ni ta ƙi ba ni ko wani irin ƙofar da zan yi mata bayyana balle har ta fahimce ni. Na daɗe zaune ina tunanin na ji an bankaɗo labulen ɗakin an shigo na cira kai ina kallon Aminu har ya shigo ya zauna. "Na ga saƙo na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Ya ɗago ya kalle ni"in ce dai ki na lissa adadin kwanakin da kika yi a cikin gidan nan yanzu ko?". Na bi shi da kallon mamaki sai dai na danne mamakin da kalamansa suka shayar da ni na ce"ina sake da yawan kwanakin. Kuma in sha Allah kwanan nan zan nema aikin da zan dinga ɗaukan ɗawainiyya kaina da shi". Ya yi ƙuri yana kallona"wani irin aiki ke nan?". "Wankau ko kuma aikatau". Cikin maɗaukakin mamaki ya ce"da kuɗin wankau da aikatau ɗin za ki ɗauki nauyin kanki?". "In sha Allah". Na amsa da shi cike da dukkanin ƙwarin gwiwa. "Kar ki yaudari kanki Amatullah babu ta inda sana'ar wankau zai riƙe. Yadda kiken nan mace iya mace sura iya sura diri iya diri, ki na da kyawun sura ta yadda duk wani lafiyayyen namijin da ya yi ido huɗu da ke dole sha'awarsa ta motsa. Idan kin iya allonki to tabbas za ki yi moriyar bariki za ki ja zarenki shekaru aru-aru, don yanzu haka ma akwai hamshaƙan mazan da suke ganin gilmawarki a cikin gidan nan kuma sun yaba za su saki baki aljihu matuƙar kika ba su dama". Na runtse idanuna"ba zan taɓa aikata zina ba a cikin rayuwata". Ya yi saurin taran numfashina"ba ki shirya aikata zina ba kika shigo bariki". Ya miƙe tsaye ya tsaya"ki yi wa kanki karatun ta nutsu. Don tallafina gare ki na sati guda ne kuma yau an ci kwana biyu saura kwanaki biyar". Yana dasa aya a nan ya cika bujensa da iska ya fice ya bar ni zaune na kasa ƙwaƙwƙwaran motsi. Na ja dogon numfashi na fesar ina yi wa zantukansa tankaɗe da rairaya. Na cije leɓansa saboda bugawan da ƙirjina yake yi. Dole ne zai na yi zina kafin na sama abin da zan ɗauki nauyin kaina da shi? Tambayar da na jefawa kaina ke nan da tsawon daren na gaza samun amsarsa. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 4️⃣4️⃣ Haka na ƙarar da dukkan tsawon daren ina tunanin ina saƙa da warwara a cikin raina. Tabbas dole na tashi na nema na kaina in bay haka kuma na ji ana yi, sai dai ta ina zan fara wai ƙoƙarin cire wando ta kai. Ina zaune a inda na iddar da sallan asubahi ina ƙarewa ɗakin kallo cikin dubu, haƙiƙa ina buƙatar wasu abubuwan buƙatan rayuwa kamar kayan sawa, abinci da wasu ƙananun abubuwan. ban yi aune ba na ji wasu hawaye suna zubo miji daga idanuna wanda ban san dalilin zubar su ba, ban goge su ba kamar yadda ban yi wani yuƙurin haka su zuba ba. "Anty Sawwama ku yafe ni na san ba jefa ku cikin tashin hankali na rashina. Na san na shayar da ruhinku ɗacin baƙin ciki, sai dai na yi muku alƙawarin ba zan taɓa sauƙa daga turban da kuka ɗaura ni a kai ba zan ci gaba da kare mutumcina da tsayawa akan gwadaben da na taso a kai". Ina rufe bakina na kai hannu ina goge fuskana tare da miƙe wa tsaye na ci ragowar abin da na bari jiya. Sai da gari ya yi haske na fito waje so nake yi na yi wanka amma ba ni da abubuwa da yawa da za su taimaka mini wajen gudanar da hakan, sai na tsaya ruwa, na nema bokiti, soso da kuma sabulu uwa uba kayan da zan sauya idan na yi wankan. Ina dab da fitowa daga cikin ɗakin muka yi kiciɓus da La'aniyatu tana shigo wa na matsa mata ta shigo, muka tsaya muna kallon juna ina da ita kafin ta ce"ina za ki je kuma da safiyar nan? Na yi tunanin ma zan zo na samu ba ki tashi daga bacci ba". "Ina so na fita ne na je neman aiki don na ga rayuwar ba za ta yiyu a haka ba". Ta yi ƙuri tana kallona"kin dade dai sai kin nema aikin nan?". "To ya ya kike so na yi, Aminu ya shaida mini cewar ɗawainiyyar ciyar da ni na tsawon sati guda kawai zai yi wanda yanzu haka ya rage kwanaki huɗu rak, idan ban fita na nema ba ya ya kike so na yi da raina a lokacin da ya janye tallafinsa a gare ni". Na yi maganar ina ƙoƙarin ficewa ta riƙo hannuna"ki bi a hankali dai mutanen unguwan nan ba ababen yarda ba ne". Kaina kawai na jinjina mata na yi ficewa ta na bar ta a cikin ɗakin, sai da na fito ƙofar gidan na sauƙe numfashi mai zafi ina ƙarewa gabar da yamma kudu da arewa kallo. "Ya Zuljalali wal ikram ga baiwarka nan". Na yi furucin a bayyane cikin sanyin jiki haɗe da na murya, na salwantar da aƙalla mintuna uku a tsaye kafin na ja ƙafafuna na bar ƙofan gidan na yi dogon tafiya kafin na iso bakin wani tankamemen gidan da aka ƙawata da shukayen koren fure. Na ƙarar da mintuna ina kallon gidan kafin na isa na ƙwanƙwasa gate ɗin wani mutum ya fito ya buɗe ƙaramin ƙofan gidan gare ɗin yana jefa na da wani irin kallo. Na tsuguna har ƙasa na gaishe shi sai dai maimakon ya amsa mini sai ya jefo mini wats tambayar cikin zafin rai. "Ke me ye kike yi a nan wajen?". "Na zo neman aiki ne?". Ya watsa mini wani ƙazamin kallo"ce miki aka yi ana neman masu aiki a gidan nan? To su masu aikinsu tun daga Abuja ake kawo musu kamfani suke zuwa su cike takarda su zayyana irin wacce suke so a kawo musu su zaɓa, ki tashi ki bar ƙofar gidan nan tun kafin na ɓata miki rai". Na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo"don Allah ka taimaka mini na shiga cikin gidan na yi musu magana da kaina, wallahi ina tsananin buƙatar aikin nan ne". "Ke zan haɗa da Allah ai ki taimake ni ki tashi daga nan wajen tun kafin masu gidan su fito. Don idan suka fito da ni da ke duk ba za mu ji daɗi ba". Yana rufe bakinsa aka buɗo ƙofar gidan yana faɗin"wai ina ka shiga ne ina ta ƙiranka?". Cikin rawar jiki ya ce"Allah ya huce zuciyarka ranka ya daɗe ka daɗe ka yi shekaru irin na dabino, na ɗan fito waje ne amma ban yi nisa ba". "Ka zo ka buɗe min gate zan fita amma ba zan daɗe ba zan dawo". "To ranka ya daɗe a dawo lafiya". Har sun juya

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});