Chapter 2
Chapter 2
ƙanwar uwata ba ta dawo da ni cikin hayyacina. Na dafe cikina da hancina suke kukan yunwa na waigo da nufi ɗauko ledar da Aminu ya kawo mini na ga waje wayam babu shi babu alamarsa. Ta yi zumbur na miƙe ina ta waige-waige amma ban ga komai ba hatta pure water guda ɗayan da na ajiye ban gani ba. Na durƙushe akan gwiwoyina ina shararo kuka da dukan ƙarfina, ga wani yunwan da nake fama da shi kamar ƴaƴan hanjin cikina za su tsintsinke, tun ina durƙushe sai da na kwanta a ƙasa na dinga juyi riƙe da cikina da yake murɗawa. Na kasa yin bacci tsabar yunwan da yake nuƙurƙusata take wani zazzaɓi mai zafi da ratsa jiki ya rufe ni na koma sauƙe numfshi da ƙyar. Da wani irin kuzari Anty Sawwama ta wayi gari ranar ta fito waje ta soma kici-kicin haɗa wuta domin ɗaura abin kari, tana cikin aikin Umar a fito ya iske ta ya durƙusa har ƙasa ya gaishe ta ta amsa fuskarta ɗauke da walwala, tare Yaya Alhassan da Amir ma suka fito suka tsuguna suka gaishe ta ta amsa tare da sanya musu albakar da addu'ar Allah ya datar da su a cikin wunin wannan ranar. "Umma ke da kanki za ki yi girkin ba za ki ba ri Asma'un ta zo ta taya ki ba". "Har yaushe zan jira zuwan Asma'u ita ma da sai ta gamo aikin gidansu kafin ta zo. Ina so yau na yi girki na musamman ga Amatullah don tun gabannin faruwar wannan lamarin babu wani abin da take ci na kirki". Ta ja dogon gashin ta fesar kafin ta ci gaba"wallahi yanzu ba ni da wani burin da ya wuce ganin Amatullah cikin farin ciki. Ba ni da wani sauran buri da ya zarce na ga rayuwarta ta gyaru wanda ya aikata mata wannan aika-aikan kuma a hukunta shi daidai da abin da ya aikata". Cikin jimami Amir ya furta"ai wallahi da zan ga wannan mutumin sai na yi masa lakanin da ko uwar da yi naƙudarsa, idan ta gan shi ba za ta shaida sa ba". "Babu wannan maganar Amir amma tabbas doka za ta yi aiki akan sa. Ba ma shi kaɗai ba hatta matar da aka yi abun a cikin gidanta sai ta ɗanɗana kuɗanta". "Hakan shi ne daidai, Allah ya datar da mu". Anty Sawwama ta yi furucin da duk suka amsa da amin, tare suka yi aikin don daman ta sabar da su akan hakan, sai da suka gama haɗa komai aka tattare wajen Umar ya shimfiɗa tabarma aka jera kayan karin kumallo. "Bari na je na taso ta". Anty Sawwama ta yi zancen tana tashi ta nufi ɗaki wayam ta tarar da ɗakin babu kowa, take ta dafe ƙirjinta cikin tsananin tashin hankali ta dudduba ɗakin hatta katifa sai da ta ɗaga. A fito jikinta yana ta rawa su Yaya Alhassan duk suka taso suna tambayar lafiya. "Ba ta ciki ban ga Amatullah ba ta cikin ɗakin". "Ba ta ciki kuma Umma?". Yaya Alhassan ya yi zancen yana faɗawa cikin ɗakin, shi ma babu inda bai duba ba amma wayam babu ko alama haka ya fito jikinsa a sanyaye aka karaɗe ko'ina a cikin gidan. Banɗaki, kicin, ɗakin ajiya babu inda ba duba ba. Suka tsaya cirko-cirko kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa. "To Umma ko ta fita ne ba mu sani ba?". "Amir ina za taje? Wani gida ta sani a cikin unguwan nan? Wajen waye za ta fita ta je ta?". Cikin damuwa Yaya Alhassan ya ce"Umma ki kwantar da hankalinki in Sha Allah babu wani abun da zai faru, bari mu fita mu duba. Da yarda Allah Amatullah za ta dawo cikin aminci". Ya juya yana kallon Umar"ka zauna tare da ita bari mu je da Amir". Yana gama faɗin haka suka fita, haka suka karaɗe cikin gari duk inda suke tunanin za a dace sai da suka je amma ba yi dace ba. Bayan sallan asr lilis suka dawo gida. Anty Sawwama tana ganin shigowan su ta miƙe"ya na gan ku haka ina ita Amatullah ɗin?". Ba su amsa mata ba sai da suka ƙariso suka zauna suna. Duk su biyun suka kasa cewa komai illa kallon juna da suke yi. "Alhassan ka buɗe baki ka yi min magana mana. Ina Amatullah take?". "Umma babu inda ba mu duba ba amma ba mu same ta ba. Duk inda muke tunanin da a dace mun je, kaina gabaɗaya ya kulle ina Amatullah za ta je wanda ba za ta iya sanar da ɗaya daga cikinmu ba?". Da hanzari Amir ya ce"to ko wajen Ummanta ta je?". Anty Sawwama ta jijjiga kanta alamar a'a"ba ta je wajen mahaifiyarta ba don wannan ƙawar tatan da suke gida ɗaya Amira ta zo nan gidan wajen ta. Wanda hakan yake nuni da cewar ba ta je can ba, kuma na ƙira Zulaihatu ma ta ce ba ta je wajen ta". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! To ina Amatullah ta shiga?". Haka suka zauna jimgum-jimgum kamar masu karɓan gaisuwar mutuwa, babu abin da Yaya Alhassan yake yi face ƙiran wayan dangi yana tambayar su ko suna tare da Amatullah. Amma duk wanda ya ƙira ba a dacewa. Ya sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya yana zare wayan daga kunnensa tare da faɗin"Umma ba a dace ba, ba ta je wajen su ba". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Umar ɗauko min hijabina na fita neman yarinyar nan don zama bai kama kama ni ba". Da sauri Yaya Alhassan ya riƙo hannunta ya zaunar da ita"don Allah Umma ki kwantar da hankalinki kin san fa kina da hawan jini. Bai kamata ki fita ba a wannan halin da kike ciki, ki bari mu mu je mu nemo ta a duk inda ta shiga". Ta kafe shi da ido"Alhassan jiya cikinku akwai wanda ya yi magana da ita ne?". Ya sadda kansa ƙasa"ni ne na yi magana da ita ƙarshe". "Wani magana suka tattaunawa da ita?". "Umma maganar da muka yi da ke ne. Kuma ban mata dole ba na ba ta daman ta je ta yi tunani kafin ta yanke ko wani irin hukunci". Ta ɗan jim kafin ta ce"Allah ya sa ba abin da nake tunani ba ne ya faru". "Umma me ye kike tunani?". "Wataƙila ta gujewa aurenka ne Alhassan". Ya waro idanunsa waje"me ye zai sa Amatullah gujewa aurena? Umma shin ina da wani aibun ne?". Ta dafa kansa"ba ta da wani aibu Alhassan amma wannan hashashe ne kawai na zuciyata wanda ba na fatan hakan ya kasance". A sanyaye ya furta"to Umma bari mu je mu ƙara duba. Amma don Allah ki kwantar da hankalinki". Murmushi kawai ta sakar masa suka tashi suka fita ba su dawo ba sai bayan sallan isha'i suka shigo cikin gidan cikin mutuwar jiki. "Ba a gan ta ba ko?". Anty Sawwama ta furta yayin da suke shigowa cikin gidan. Sai da suka zauna kana Amir ya yi ƙarfin halin faɗin"Umma ba a dace ba". Ta sauƙe tagwayen ajiyar zuciya kafin ta ce"Amatullah amana ce a gare ni ba zan so duk abin da zai cutar da ita. Yanzu ban san halin da take ciki ba". "Umma ni babu abin da nake tunani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98