Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 41

Chapter 41

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na kwanta sa boda sarawan da kaina yake yi mini tamkar ana buga mini guduma. Ban yi nisa a cikin baccin ba na ji sauƙar ruwa mai sanyi a fuskana babu shiri na tashi sai dai duk da firgitan da na yi hakan bai hana ni kamo sunayen mahaliccina guda ɗari babu ɗaya ba cikin bakina. Na cira kai ina duban Altine da take tsaye a kaina babu alamar ranƙwafawa tamkar wacce ta haɗiye taɓarya. Raina ya tuntsura yana tafasa tamkar talgen da yake bisa wuta yana ɓararraka. "Kin fi kowa sanin cewar ai ba bacci ne ya kawo ki ba, da za ki zo ki yada baki ki na baccin asara wanda babu gaira babu dalili". Tsam na miƙe akan ƙafafuna"na lura duk yadda na kai ga ƙoƙarin ganin na ba ki girmanki na kuma mutunta ki ba kya ganin hakan. To gwara na fito miki a mutum na fito miki a yadda kike so, Ina so ki sani ni fa baiwarki ba ne a cikin gidan nan hasalima matsayinmu ɗaya. Ki riƙe girmanki ni ma zan tabbatar da cewar na yi miki biyyaya a matsayinki da wacce kike gaba da ni amma idan kika zubar da mutuncinki babu abin da zai hana ni sanya ƙafa na take sa, ai daman idan malam bai ji kunyar hawa jaki ba to jaki ba zai ji kunyar jefar da shi ba". Ina rufe bakina kawai na ga ta ɗaga hannu da nufin zabga mini mari na yi caraf na riƙe hannunta. "Kar ki kuskura ki ƙara yin gangancin ɗaura hannunki a jikina da sunan mari. Don duk ranar da kika ƙara maimaita haka zan yi miki abin da tarihin rayuwarki ba zai taɓa cika idan babu shi". Ina dire zancen nawan na sakar mata hannunta na juya ɗauki hoton na ƙulle a gefen hijabina na fice daga cikin ɗakin, kai tsaye kicin na nufa na iske har ta fara aikin girkin abincin ranan, na nema waje tsaya tare da naɗe hannayena a ƙirjina ban taɓa komai ba har ta shigo cikin kicin ɗin tana ta faman harare-harare. Cikinmu babu wanda ya ce da wani ko kanzil. Haka nan ban motsa daga inda nake ba balle na yi wani aikin har ta gama girkin ta sauƙar ta ɗauko kula za ta zuba a ciki, ni ma na ɗauko plate na ajiye mata ta ɗago ido ta kalle ni kamar za ta yi magana sai kuma ta yi shuru. Ganin ba ta da alamar zuba mini ina ganin ta gama zuba wa a kulan na ɗauki kudayin na zuba wa kaina na ɗauko na koma gefe, na soma ci. Ina ganin ta ta gefen idona sai banko mini harara take yi kamar idanunta za su faɗo ƙasa. Ina gama cin abincin na wanke plate ɗin na koma ɗaki na yi alwala na gabatar da sallan asr, ina zaune kan sallayan ta shigo ko sallama babu ni ma ban damu don ko ɗaga kai ban yi ba balle na gan ta. Haka kawai na ji gabaɗaya zaman gidan ya fita akaina, don haka na tashi na fito falo ina fito wa na tarar da Hajiya tana sauƙo wa daga beni yayin da su Aryan suke biye da ita a baya. Muka sakar wa juna murmushi ni da ita yayin da muka haɗa ido kafin na yi mata sannu da fito wa ta amsa mini cikin sakin fuska. Da hakan ya ba ni damar amayar da roƙona. "Hajiya daman ina so na je gida ne idan babu damuwa". "Za ki iya zuwa Amatullah ai na ga babu wani aikin ma da ya rage, mun yi waya da Saif ba za su dawo yanzu ba. Ni ma kuma yanzu zan fita shago ne akwai kayan da zamu haɗa su Aryan muka zan ajiye su a wajen Hajiyarmu. A taƙaice dai dawowarmu mu ma zai iya kai wa dare, mu je na sauƙe ki a hanya". Cike da jin daɗi na ce"ina godiya Hajiya". Na riƙo hannun Ayan muka fita zuwa wajen motar muka shiga, ta ja motar muka fita a hanya ta sauƙe ni yayin da su kuma suka wuce. Ban yi tafiya mai nisa ba na iso gida ina shigowa na hango Zinariya a ƙofan ɗakinta tana girki. Muka sakarwa juna murmushi kafin ta ce"kin dawo kenan? Ɗazu na leƙa ai ba kya nan?". Na gyaɗa mata kaina yayin da nake zama akan dakalin ƙofar ɗakinta. "Yau gidan shuru lafiya kuwa?". "Kin san yamma ta yi ai yanzu kowacce ta shirya ta tafi waje kwastomanta". Na jinjina kaina ina girmama lamarin a cikin raina, haka ta yi ta ja na da hira har izuwa lokacin da wayarta da take cikin ɗaki ta soma ruri. "Taimaka ki ɗauko min wayata a cikin ɗaki. Kin fi kusa da ƙofar". Kaina kawai na gyaɗa mata yayin da nake tashi na shiga cikin ɗakin ina ɗaukar wayar ƙiran yana tsinkewa. Hoton fuskar wayar ya bayyana idanuna suka kai kansa. Take na ji ƙirjina ya harbawa tabbas indai ba ƙarya idanuna suke yi mini ba hoton Abbinsu Aryan ne tare da Zinariya a fuskar wayar kamar za su rumgume juna tsabar kusanci da jikinta ya yi da shi. Jikina ya ɗauki rawa ina ƙara ware idanuna don tabbatar da sahihancin abin da suke nuna mini. [12/4, 7:36 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 6️⃣1️⃣ Jikina gabaɗaya ya ɗauki rawa tamkar wacce aka jona wa wutar lantarki, na kasa yin komai illa idanuna da na ci gaba da ƙurawa hoton fuskar wayar. "Ba ki sa ma wayar ba ne?". Tambayar da Zinariya ta jefo mini daga waje shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na afka. A lokacin aka ƙara ƙiran wayar a karo na biyu na juya da nufin zan kai mata muka yi kiciɓus da ita a ƙofar ɗakin tana shigowa, na miƙa mata wayar yayin da ni kuma na fice waje. Na zauna akan kujerar da ta tashi tare da zabga tagumi tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar wani shaƙiƙinta. Ina zaune a wajen har Zinariya ta gama wayar ta fito ta ja kujera ta zauna, na bi ta da kallo ganin yadda fara'arta ya ƙaro sam bakinta ya kasa rufuwa sai washe haƙwara take yi tamkar wacce aka yi wa wani gagarumin kyautar a zo a gani. "Yau ina cikin alkhairi dumu-dumu, tun da na wayi gari na ke cin karo da alkhairi". Ta yi zancen cikin maɗaukakin farin cikin da ya bayyana har a cikin furucinta. "Me ya faru haka? Na ga gabaɗaya fara'arki ta ƙaru". "Alhajina ne ya ƙira ni yanzu muna gama wayar na ga alert miliyan guda a cikin asusun ajiyata". Na bi ta da kallo kana na ce"miliyan guda? Wannan maƙudan kuɗaɗen na mene ne haka?". Ta yi fari da idanunta kafin ta furta"kyauta ce kawai daga masoyi zuwa masoyiyarsa, ranar Alhamis zai aiko mota a ɗauke ni zuwa can garin Abuja ranar juma'a na ƙara kimtsa kaina na jira dawowarsa a yammacin ranar don ba ya ma ƙasa gabaɗaya. Ya yi mini alƙawarin tare da ni zai yi hutun ƙarshen mako kuma sa boda ni mussamman ya baro duk abin da yake yi ya zo shi". "Irin wannan hidima haka

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});