Chapter 45
Chapter 45
tsaya na ji amsar da za ta ba ni ba na yi ficewa ta daga cikin ɗakin na bar ta tsaye a wajen tana cizon ƴatsa. Na iske Hajiya Muhibbat zaune a cikin falon tare da Saif da alama wata muhimmiyar tattaunawa suke yi ganin yadda gabaɗayan su suka tattara hankulansu waje guda. "Anty lokaci ya yi fa za mu gaya wa Yaya gaskiya abin da yake yi sam bai dace ba. Ta ya ya mutum mai iyali sai tafi can wata uwa duniya ya tare shi kaɗai har ya shafe tsawon wani lokaci mai tsayi ba tare da ys waiwayi amanar da yake kansa ba balle har ya yi ƙoƙarin sauƙe nauyin da Ubangiji ya ɗaura masa ba. Anty idan ma har yanzu wannan abun da ya faru ne a cikin ransa ai ina tunanin za ki ci albarkacin waɗannan ƴaƴan da kika haifa masa ya sauƙo. Ya rumgumi ƙaddara kamar yadda ke ma kika manta da duk abin da ya afku kika amshi a matsayin miji a gare ki kuma uba ga tagwayen ƴaƴanki". Cike da gajiya da sauraronsa Hajiya ta ɗaga masa hannu muryarta tana rawa ta ce"Saifullah ya isa haka ba na son ana tuna min da abin da ya riga ya wuce hakan ya kan jefa ni cikin wani irin hali. Ina yi wa Saddam uzuri akan komai da yake aikata ba wai don ba na jin zafin abin da yake aikata wa sai don kawai ɗaurewar zaman lafiya a tsakaninmu da shi tun da ka fi kowa sanin halaye da ɗab'iun ɗan uwanka. Babu abin da Saddam zai aikata a gare ni da hakan zai sauya matsayin da yake da shi a cikin zuciyata". "Anty wai har sai yaushe ne za ki daina yi wa Yaya Saddam uzuri akan rashin adalcin da yake yi a gare ki? Na yarda ki na son mijinki amma don Allah na roƙe ki kar ki ba fi wannan soyayyar ta rufe miki ido, ta ki kasa faɗa masa gaskiya idan ya aikata ba daidai ba. Shi fa zaman aure na mutum biyu ba na mutum ɗaya ba dole sai kowa ya ba da na shi gudumawar kafin abubuwa su tafi yadda ya kamata. Anty ba ni da kowa a duniyar nan da ya rage min face Yaya Saddam shi ne komai na wa, shin ki na tunanin ba na jin zafin abin da yake aikata wa ne? Waɗannan fa ƴaƴansa ne ke kuma matarsa ce wacce ta sadaukar da komai sa bosa shi, ki zaɓi shi sama da kowa. Ki zaɓi ki yi rayuwa da shi har izuwa lokacin da numfashi zai yi bankwana da gangar jikinki". "Ya isa haka Saif na ce ya isa haka". Hajiya ta yi zancen cikin ɗaga sauti tana sa hannayenta ta toshe kunnuwanta da su. "Ka tashi ka fita ka ba ni waje ko kuma ka yi wata maganar amma ba wannan ba. Don ba zan iya juran hakan ba". Miƙewa tsaye ya yi jikinsa gabaɗaya ya mutu murus kamar wanda aka zare wa laka. A hankali yake motsa leɓansa yana faɗin"shi kenan Anty ba zan ƙara yi miki wannan maganar ba. Daman na shigo na sanar da ke cewar ɗazu na kai Muhammad Sultan filin jirgi, mun zo tare zai yi miki sallama kuma na ga ba ku buɗe ƙofa na ƙira wayarki ba ki ɗaga ba, ya ce a yi miki godiyar irin ɗawainiyyar da kuka yi da shi a tsawon kwanakin da ya yi a cikin wannan gidan". Yana dasa aya a zancen ya juya ya fice daga cikin falon, da hakan ya sanya Hajiya dafe kanta cike da damuwar da ya gauraye da tsananin tashin hankali. Saɗal-saɗal na ja ƙafafuna na bar cikin falon na wuce cikin kicin na tarar da babu wani alamar an ɗaura girki, na nema waje na tsaya na rumgume hannayena a ƙirjina kafin na soma safa da marwa a cikin kicin ɗin. "Saddam". Na maimaita sunan a bayyane ina sauƙe wani gwauron ajiyar zuciya mai nauyin kilo ɗari da ɗoriya da ƴan kai. In dai ta tabbata cewar wanda na ga a fuskar wayar Zinariya shi ne Saddam mijin Hajiya Muhibbat ya yi wa Zinariya alƙawarin durowa cikin ƙasar nan a yammacin ranar juma'a. "Kai kawon me ye kike yi? Ba ki fara haramar ɗauka abin kari ba?". Na tsinkayo muryar Altine ya sauƙa a cikin ƙofofin kunnuwana tamkar sauƙar aradu. A ɗaga kai ina dubanta cike da son ƙarin bayyani, fahimtar abin da nake nufi ya sanya ta faɗin"ƙwarai ai kin ji abin da na faɗa, da can waye kike ajiye da kike tunanin zai ɗaura miki girkin ki zo ki ɗiba ki je ki baje akan katifa?". Ban ce da ita komai ba na wuce na soma kici-kicin ɗaura girkin, ɗan wake na yi mai rai da motsi. Na yanda kabeji, tumatur da kokanba na soya mai ya soyu rafai. Na haɗa komai na jere su akan dinning table kana na zo na durƙusa a gaban Hajiya. "Hajiya ga abin karin kumallo a gama". "Amatullah ba na jin zan iya cin komai, ba na jin sha'awar cin dankalin nan a dai kawo min ruwan shayin na sha kawai". "Ba dankali ba ne ranki ya daɗe, ɗan wanke ne". "Ɗan wake?". Ta maimaita na gyaɗa mata kaina alamar e. "Ai kuwa na kwana biyu ban ci ɗan wake ba. Tun wani lokacin da muka je gidan Hajiyata ta sa aka yi mana rabona da cin ɗan wake. Kawo min nan mu ci tare da su Ayan sai ki kai wa Saif na shi don na san yanayin da ya bar nan ba lalle ya shigo yanzu ba". "To". Na amsa da shi a taƙaice tare da tashi na je na kawo mata komai gabanta, na haɗa na Saif kamar yadda ya faɗa na fita zan kai masa, ina ta jeranta sallama a ƙofar falon amma ba a amsa ba kamar yadda ba a fito an buɗe ƙofar ba. Sai can aka zo aka buɗe ƙofar na tura ƙofar na shiga cikin bakina ɗauke da guntun sallama. Yana kwance akan doguwar kujerar zaman mutum uku ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman ƙirjinsa yayin da hannu ɗayan ya dafe goshinsa da shi, idanunsa suna lumshe amma na tabbatar da cewar ba bacci yake yi ba. Na ajiye tray ɗin abincin akan teburin da yake gabansa na juya zan fita. [12/6, 1:28 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 6️⃣3️⃣ Har na kai ƙofar ficewa daga cikin falon na tsinkayo muryarsa a dake yana faɗin"dawo ki ɗauke abin da ya kika ajiye". "Me yasa?". Ya yi banza da ni ba tare da ya ce da ni ci kanki ba, shurun sa bai hana ni ƙarisa zancen da na ɗauko ba"Hajiya ce ta ce a kawo maka idan ba za ka ci ba ita ya kamata ka ƙira ka sanar da ita, faɗa nata ne ni kuma ci kawa nawa". Ina dasa aya anan na juya na fita daga cikin falon a hankali nake taka ƙasa ina ɗaga ƙafafuna da ƙyar na koma cikin sashin Hajiya suna zaune tare da su Ayan suna cin abinci sai dai ita juya cokalin kawai take yi ban ga ta kai ko da loma guda cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98