Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 82

Chapter 82

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mana ƙur'ani a cikin gidan nan, sannan mu riƙi addu'o'i da azkar don shi ne kawai mafita". Cike da gamsuwa ya ce"in sha Allah yadda kika ce Umma hakan za a yi, bari na je na kwanta Allah ya tashe mu lafiya". "Amin". Ta amsa da shi da hakan ya ba shi damar tashi ya fita, ni kam dole ta sanya Anty Sawwama kwanan a nan tare da ni sa boda yadda duk bayan mintuna nake firgita har sai an riƙe ni. Washe gari da sassafe Yaya Alhassan ya nemo Malamai suka zo suka yi sauƙan alƙur'ani a cikin domin kariya da kuma fin ƙarfin duk wani aljanni ko iska har ma da wani mai mungun nufi, da mummunan ƙuduri. Kwana biyu na jera a jere ba na samun bacci duk da kuwa yadda aka zage da addu'a da roƙon Allah, Yaya Alhassan har yanka ya sa aka yi mini kafi lamarin ya lafa sai dai cikin ɗan kwanaki na rame sosai na fita daga cikin hayyacina. A ranar wani labara ina kwance a ɗaki ina karanta littafin ƁOYAYYEN MANUFA, labarin zazzafan soyayyar Aishatu da Abdulhamid da ya karo da ƙaddarar da ta yi silar tarwatsa dukkan gini da tubalin da suka gina soyyayarsu a kai, Amir ya shigo ya kawo mini sabuwan waya ƙarama har da layi a cikinta, ya kuma shaida mini cewar Yaya Alhassan ne ya ce ya kawo min don ba son ina amfani da wannan wayar da na zo na ita ya kuma ce ma na ba ta ita. Ban yi musu ba na tashi na ɗauka wayar daman ko layi babu a cikin ta, memory ne kuma shi ma tunin na cire sa tun lokacin da Yaya Alhassan ya umarce ni da na goge wannan sautin muryar, na naɗe sa a cikin takarda na sanya a cikin jaka yayin na ɓoye sa a can ƙasan kayana. Tare da shi muka fito falo ta juya wayar a hannuna yayin da nake ba shi saƙon godiya ya isarwa Yaya Alhassan kafin ya dawo gidan na yi masa na mussamman, turus muka yi ganin baƙi a cikin falon tare da Anty Sawwama. Muhammad Taufik ne tare da Saifullah da suke gaishe da Anty Sawwama ciki girmamawa ta na amsawa fuskarta kamar gonar auduga. Juya ciki na yi don ko mayafi babu a jikina na fito na zauna a bakin katifa yayin da na faɗa cakwakiyar tunanin dalilin zuwan su gidan a wannan lokacin. Ban yi nisa cikin tunanin ba Amir ya ɗago labulen ɗakin fuskarsa a sake ya ce"ki fito ku gaisa". Na murtuƙe fuskana"Mu gaisa kuma Yaya Amir? Ni fa ina tunanin lokaci ya yi da za du dakatar da mutanen nan daga zuwa cikin gidan nan". Jijjiga kansa ya yi yana ɗan murmushi ya ce"yanzu dai ki yi haƙuri ki fito ku gaisa". Ya na dasa aya a zancen ya saki labulen ya juya ya fita, ina ta ƙunƙunai na ɗauko hijabi na saka na fito falon lokacin da na fito na iske Anty Sawwama ma ta tashi daga cikin falon. Can gefe na zauna kaina a ƙasa na gaishe su suka haɗa baki wajen amsawa kafin shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe. Har sai da na ƙosa da zaman kafin na tsinkayo muryar Muhammad Taufik yana faɗin"Amatullah mun zo gaisuwa ne tare da neman iri, na san ba ki manta zancen da Saifullah ya zo miki da shi ba kwanakin baya ya sanar da ni cewar har yanzu ba ki ba shi amsa ba hasalima ba ki saurare shi ba. Ina mai tabbatar miki da cewar Saif mutumin kirki ne duk inda ake neman mutum na ƙwara to ya kai wannan matakin a iya tsawon zamana da shi ban taɓa jin ya buɗe baki ya furta yana son wata mace har ya yi burin aurenta ba sai ke, ke ce mace ta farko a cikin labarin rayuwarsa ke ce mace ta farko da ta fara karya alƙadarinsa. Don Allah ki ba shi dama ko da sau ɗaya ne ki ba shi damar ya yi yaƙi domin tabbatar miki da ƙarfin soyyaya da ƙaunar da yake gwada miki". Tun da ya soma zancen nake kallonsa da wutsiyar idanuna ina jin wani abu yana tasowa tun daga cikin zuciyata yana tokare mini ƙirjina. Take! Ranar kuwa fara ganin lokacin zan tafi islamiyya ya soma dawo mini cikin kwanyata, na yi saurin tare da hawayen da suke shirin ɓalle mini. "Mun yi tunanin ko akwai wanda kike magana da shi ko kuma an riga da an yi miki miji shi yasa ba ki saurare shi, amma yanzu da muka zuwa Anty da maganan ta tabbatar babu ko ɗaya, kuma ta ba shi damar ya nema amincewanki idan har kin amince shi kenan". Ban san dalili ba haka kawai tun ya ci gaba da maganan na ji hawayen da nake ta ƙoƙarin riƙe wa sun ɓalle suka fara kwaranya. "Ka ga ne Sultan ba ri na je waje ba zan iya jure ganin zuban hawaye daga idanunta ba". Saif ya yi furucin cikin sanyin jiki da na murya bai jira amsar da zai ba shi ba ya tashi ya fita. Daga ni har Muhammad Taufik muka yi shuru na tsawon mintuna kafin can ya kawar da shurun ta hnayar cewa"Amatullah in dai ba ni damuwa kuma ba za ki takura ba. Don Allah ki ba wa Saifullah dama ina yaƙinin ba za ki taɓa yin dana sanin zaɓinsa ba, ba zai taɓa yin gangancin jefa ki a cikin wani halin da za ki yi tir da kasancewarki da shi a cikin inuwa ɗaya ba". "Me yasa ka gaza fahimtar cewa ban dace da shi? Ba na so na gurɓata masa tarihi ta hanyar haɗa jini da shi. Na yarda aure bautar Ubangiji sai Allah bai kallabafawa Bawansa yin sa dole ba hasalima akwai hanyoyin neman aljanna bila adadin. Zan rayu kuma na tsayu akan hanyar bautar Allah da neman yardansa ba dole sai na yi aure ba". "Ko da kuwa aure bai kasance dole ba amma shi ne cikar mutunci da kimar duk wata mace. Aure rufin asiri ne ga ƴaƴan mata, ko ba Saifullah ba ina tabbatar miki da in lokaci ya yi dole ne ki yi aure". A sanyaye ya ƙare zancen muryarsa har ta na riƙe wa, alamar akwai wani abun a ƙunshe a ƙasan zuciyarsa da yake ɓoye wa. "Me yasa kake yin duk wannan ƙoƙarin akan kawai na amince da Abokinka?". Kamar jira yake yi na yi masa tambayar ya yi hanzarin ba ni amsa. "Sa boda na tabbatar da soyayyar da yake yi miki babu yaudara a cikinta, kuma zai riƙe ki amana tare da ƙoƙarin faranta miki har ƙarshen rayuwarsa". Na jinjina kaina tare da ƙarfin halin cilla ƙwayoyin idanuna cikin na sa kafin na furta"ka na nufin ke nan kai ba so na kake yi ba?". Babu shiri ya ɗago idanunsa da suke bayyanar da maɗaukakin mamaki ya kafe ni da su. Hakan ya ba ni ƙarfin gwiwan ci gaba da furzo da magana"kar ka musa abin da ya riga ya bayyana a cikin idanunka. Muhammad tun ranar da Allah ya haɗa mu kana so ka ce mini ba sona kake yi ba? Idan ba so na kake yi

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});