Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________________ Page 4️⃣1️⃣ Na daɗe ina kukan har sai da na gaji don kaina na tashi na share hawayena, so nake yi na je na yi alwala na gabatar da salla amma ban san ta inda zan fara ba ga shi ina son shiga banɗaki na tsaftace jikina kafin na yi sallan. Ganin wankin hula yana neman ya kai ni dare ya sani tashi na fito waje, cike gidan yake da mutane jinsin maza da mata kowa yana harkan gabansa daga matan har mazan babu wani shigar arziki balle ta mutunci. Mafi yawan matan zani ne a jikinsu ɗaurin ƙirji mazan kuwa gajeren wando da ya tsaya daidai gwiwansu masu kunya daga ciki suka ƙara da singileti. Na fi mintuna biyar a tsaye a ƙofar ɗakin na kasa gaba na kasa baya illa bin kowa da nake yi da ido. "Madam lafiya kin yi tsaye sai ƙare mana kallo kike yi in ce dai lafiya ko?". Na yi an yi zancen a zafafe kamar za a rufe ni da duka, da sauri na waiga don ganin wanda ya yi furucin. Wata matashiyar budurwa ce tsaye ta riƙe ƙunta tana ƙare mi kallon tsaf kamar yadda ni ma nake bin ta da kallo. Kafin na ce wani abu ta daura mini mari na yi saurin dafe kuncina don ba ƙarya marin ya shige ni sosai har sai da na ji idanuna sun kawo ƙwalla. "Ke waye da har ina yi miki magana za ki tsaya kina kallona maimakon ki ba ni amsa? Yau sai kin faɗa min uban da ya tsaya miki a cikin gidan nan da har ya ba ki damar da za ki yi min wannan ɗiban albarkan". "Me na yi miki za ki mare ni?". Na yi zancen har izuwa lokacin ina dafe da kuncina, da alama tambayar ta fusata ta don sai da ta riƙe haɓa kafin ta furzo zancen. "Kan uban can! Lalle ba ki san da wacce kike magana da ita ba ne shi yasa kika tsaya a gabana ina faɗa ki na mayar mini da martani. To yau zan nuna miki ƙarshen barikinki da iya shegen da kike ji da shi". Ta kacumo wuyan hijabina ta riƙe tamau har sai na soma tari, duk cikin dandazon jama'ar tsakar gidan babu wanda ya taso balle ya kawo mini ɗauki. Kowa ya mayar da hankali kan abin da yake yi. "Me ye nake gani haka Baraka? Kashe ta za ki yi ko kuwa? Sakar ta na ce". Hajiya Babba ta yi zancen yayin da take fitowa daga ɗakinta ta fincike hannun Baraka daga jikina. "Baraka na sha gaya miki cewar ba na son rigima a cikin gidan nan. Babu wanda nake ajiye kara ya tsallake shi face ke don hakan ba za ka tara min ciwon kai ba. Yanzu ba sai an jima ba ki shiga ki haɗo duk abin da yake mallakinki ne ki fice ki bar min cikin gida, tun da ba kuɗi muka haɗa muka gina gidan tare da ke ba". Take jikin Baraka ya soma rawa ta zube a ƙasa ta na magiya. "Don girman Allah Hajiya ki rufa min asiri kar ki bari na tozarta na kunyata a idanun maƙiya. Kin san yanzu ƙiris ake jira ya faru a soma yamaɗiɗi da kai. Hajiya ki rufa min asiri wannan shi ne na farko kuma na ƙarshe". Cikin zafin rai Hajiya ta soma cewa"sanin kanki ne Baraka ni ba na yafiya kuma ba na sauƙa daga kan maganar da na riga na furta. Don haka ki shiga ki haɗo kayanki ki bar min cikin gidan, daman na sama wanda suke son ɗakin kuma har na dafe ƴan sulallana". Tana dasa aya a nan ta waigo kaina. "Ke kuma me ye kike buƙata?". Na yi ƙasa da kaina kafin na ce"banɗaki zan shiga, sai kuma ina so na yi alwala". Ta nuno ni da ƴar manuniyar ƴatsarta kafin ta furta"zan ɗaga miki ƙafa ne kawai saboda ke baƙuwa ce kuma Aminu ya kawo ki to za ki ci albarkacinsa. Zan ba ki ruwa da buta da bargon kwanciya wanda za ki yi amfani da shi, amma ina so ki sani kuma ki sa a cikin kanki cewa a gidan komai na sayarwa ne komai da kike ji da gani ke za ki nemawa kanki hatta ruwan wanke ido kin ji ni ko?". Jikina yana ɓari na ce"e na ji na gode sosai". Ba ta tanka mini ba ta shige ɗaki babu jimawa ta fito, ta ba ni bango, buta sabuwa sai kuma pure water guda uku. Na karɓa na durƙusa har ƙasa ina yi mata godiya, ba ta bi ta kaina ba ta yi shigewarta cikin ɗakinta bayan ta gama gindawaya Baraka gargaɗin kar ta kuma fitowa ta iske ta ba ta bar cikin gidan ba. Na shiga ciki na ajiye bangon na zuba ruwan guda biyu a butan na bar ɗaga na sha, na fito na rasa gane ina ne banɗakin don haka na isa wajen wasu mata na yi musu sallama. Maimakon su amsa sai na ga duk sun kafe ni da idanuna kamar wacce ta zo da wani sabon abu. "Don Allah ni baƙuwa ce a gidan nan yau na zo. Banɗaki nake nema ina so na shiga". Duk su ukun suka fashe da dariya har da tafa hannu suka mayar da ni kamar magiji da sun kalle ni sai su tuntsire da dariya. Haka na gaji da tsayiwa na bar wajen na koma can gefe na tsaya. "Ki na neman wani abun ne?". Na ji an furta a kusa da ni. Na ɗaga kaina ina ƙarewa wacce ta yi zancen kallo sanye take da hijabi fari irin wanda ake ƙira da sunan half sunna. Na ja dogon numfashi na fesar kafin na ce"ni baƙuwa ce banɗaki nake nema". Ta yalwata annurin fuskarta kafin ta ce"mu je mana to na nuna miki". Ta yi gaba ina bin ta a baya har muka isa bakin banɗakin ta yi mini ishara da hannunta alamar na shiga. Na sakeke na tsaya ganin mutane tsaye cirko-cirko a ƙofar banɗakin suna lamarin gabansa babu abin da ya sha musu kai. Fahimtar abin da nake nufi da abin da yake yi mini yawo cikin raina ya sa ta faɗin"kar ki damu ki shiga abin ki, zan tsaya miki a wajen babu wanda zai shigo kanki". Na waro idanuna waje cikin firgici na ce"a shigo kaina kuma?". "Kaɗan ne daga cikin abubuwan da mutanen cikin gidan nan za su iya aikata. Don haka ki shiga abin ki ina tsaye a nan babu wanda zai shigo". Na jinjina kaina ba don na gamsu da abin da ta ce da ni ba, na shiga banɗakin na yi abin da zan yi na fito sai dai duk a firgici nake. Na yi alwala muka dawo ciki na yi mata godiya sosai ta nuna mini babu komai na shige ɗakin da aka kai ni. A bisa tabarman na yi sallan magrib da isha'i ko da na shafa addu'ar da na yi na zauna, na zabga tagumi ina tunanin makomar rayuwata da yadda lamura suke sauyawa. Na daɗe a zaune har sau da dare ta yi nisa, kafin yunwa da ba kasancewa

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});