Chapter 9
Chapter 9
Ina cikin tafiya takalmin ya tsinke na ji kamar na ɗaura hannu a ka na ta zabga ihu ko zan ji sauƙi halin da nake ciki. Haka na riƙo takalmin a hannu ga rana ga yunwar da take ƙwaƙular ƴaƴan hanjina na dawo gida, na sama ƙofar ɗakin a kulle da makulin na san La'aniyatu ce ta rufe ɗakin don ita na bari a cikinsa. Kafin na shiga ɗakinsu ta fito kamar ta san abin da zan tambaye ta ta miƙo mini ɗan makullina, na karɓa ba tare da na ce da ita komai ba na buɗe ɗakin na shiga na zube akan tabarma kamar kayan wanki ina sakin wani irin kuka mai ratsa zuciyar mai saurare. "Wai me ya faru ne kin fita kuma kin dawo ki na kuka?". Ban iya cewa da ita komai ba saboda yadda kukan ya gama galabaitar da ni. Ta ɗago ni tare da kwantar da kaina a bisa cinyoyinta tana ƙara maimata mini tambayar a karo na biyu. "Wai me yake faruwa ne Amatullah?". "Me yasa mutane ba su da tausayi ne? Me yasa masu kuɗi ba sa tausayi na ƙasa da su? Me yasa masu kuɗi ba sa tausayin masu rauni? Wani irin al'umma ce muke rayuwa a cikin da babu tausayi balle jin ƙai?. Kowa babu Allah a cikin zuciyarsa kowa saɓon Allah da kaucewa koyarwa Annabinmu Muhammadu kawai aka saka a gaba. Ta ina za a sama yadda ake so? Me yasa masifo da bala'i ba za su baibaiye al'umma ba?". Shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe na tsawon mintuna kafin ta kawar da shi ta hanyar faɗin"wai me ya faru ne?". Na kwashe komai tiryan-tiryan na sanar da ita ta daɗe ba ta yi magana kafin can ta ce"kin ga hakan kaɗai ya isa ya tabbatar miki da cewar sauran matan da kika gani a cikin gidan nan su ma dole ce ya sanya su aikata abin da suke aikatawa na haramci ba wai don son zuciyoyinsu ba". Na tashi na zaune"babu wani uzuri cikin aikata saɓon Allah. In sha Allah zan ci gaba da nema har na dace da na ƙwarai". Ta yunƙura za ta yi magana na dakatar da ita"ki taya ni da addu'a kawai". Ta ja numfashi ta fesar kafin ta ce"shikenan Allah ya sa ki dace". "Amin". Na amsa da shi, ta tashi ta fita ta bar ni a cikin ɗakin, na kwanta ina tunanin mafita ga bahaguwar rayuwata. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 4️⃣5️⃣ Tun da na shiga cikin ɗakin ban fito sai alwalan da na fito na yi na koma ciki na zauna, a nan na yi sallan zuhur, na yi asr har magrib. Yunwa ya dinga ƙwaƙulan kayan cikina na dafe cikina ta faman murtsukuku a wajen kamar zan mutu, ina mayar da wani irin numfashi da ƙarfi da ƙarfi da ƙyar na iya tashi na zauna ina salati tare da karanto dukkanin wani addu'ar da ya fara zuwa bakina. Ganin yunwa yana neman raba ni da numfashina idanuna har wani dishi-dishi yake yi mini ga wani irin nauyin da kaina ya yi mini na bala'in gaske. Da rarrabe na fito ƙofar ɗaki na dinga warara amai tamkar zan amayar da dukkan kayan cikina sosai nake aman har jikina yana rawa kamar ana jona mini wutar lantarki. "Sannu Amatullah ba ki da lafiya ne?". Na tsinkayo muryar La'aniyatu a bisa cikin kwanyata, na kasa ba ta amsa da kalmomin baki ila gyaɗa mata kaina da na yi alamar e ta taimaka mini na tashi tsaye sai dai ƙafafuna sun kasa ɗaukar nauyina. Muka koma ciki na kwanta lamau kamar ruwa na kasa tashi balle na ɗaga ko da ƴatsan hannuna. "Wai me yake damunki ne?". Na yi jarumtar faɗin"yunwa nake ji wallahi ji nake yi kamar numfashina zai tsaya cak". "Bari na kawo miki abinci sai ki ci". Ta ƙare zancen tare da tashi ta fita babu jimawa ta kawo mini biredi da ruwan shayi da babu ko madara a cikinsa, na tashi jikina yana rawa na amsa na ɓula ledar na soma zuƙa ina turawa da biredin sai da na ci ya fi rabin biredin kana na ƙarisa zuƙe ruwan shayin na koma na kwanta ina mayar da numfarfashi. "Sannu! Ya jikin na kin?". "Yunwar ce fa kawai". Cike da tausaya wa ta ce"ba ki ci abinci ba ne tun safe?". Hawaye suka ziraro mini daga gefe da gefen idanuna kana na ce"ban ci ba Aminun yau gabaɗaya bai shigo ba". Ta sauƙe numfashi mai ƙarfi da har sai da na jiyo sautin fitar sa"na ji fa Ummanta suna waya da shi yana cewa ya yi tafiya can wani gari, kuma ina tabbatar miki da cewar da wata matar zai dawo ya kawo ta cikin gidan nan". "Yanzu haka zan zauna kenan babu ci babu sha har sai ya dawo daga tafiyar da ya yi ke nan?. Dole na tashi na nema yadda zan taimaki kaina, ki riƙe ni na tashi na zauna na yi salla". Na wangale baki da ido tana duba na"salla kuma? Ba ki da lafiyan ma ba za ki huta ba? Ban taɓa ganin macen da take girmama ibada sama da ke ba. Tun da kika zo gidan nan ban taɓa ganin kin yi fashin salla ba". Cike da matsanancin mamaki nake bin ta da kallo na gaza cewa komai har ta gama zancen ta ƙare. "Salla kam ai ko da lafiya ko akasin hakan dole ce akan dukkan wani musulmi mai hankali kuma balagagge. Matuƙar kana cikin hankalinka dole ka yi salla ka bautawa Ubangijinka". Ta sauƙe numfashi kafin ta ce"tirƙashi! Ni dai na tashi ne kawai a matsayin musulma amma duk wasu abubuwan da suke cikin musulunci ban san su ba kuma ba na aikata su. Sallar ce kawai ita kuma bai fi a sati na yi sau biyu ba shi ma sai na ga dama, tun da nake Mahaifiyata ba ta taɓa nuna min cewa salla dole ne a kaina ba balle ta koyar da ni sauran wasu abubuwan addini". "Ko ba ta koyar da ke ba ke ya dace ki tashi ki nema ilmi ki nema ilmin addininki domin inganta rayuwarki ta gidan duniya da kuma na lahira. Kin ga hatta wannan sunan da ake ƙiranki La'aniyatu ba shi da gurbi a cikin addinin musulunci, domin fassara Annabinmu ya koyar da mu cewa mu sanya wa ƴaƴanmu sunane masu kyau da ma'ana domin suna linzami shi yasa ake so a dinga sanya wa ƴaƴa sunayen salihan bayi, masu imani da zuciyar tausayi waɗanda suka yi wa addinin musluncin hidima da ƙarfinsu, lokacinsu da kuma dukiyansu". "To me ye fassaran sunan nawan?". "Kalmar La'aniyatu kalmar labarci ne da yake nufin tsinanniya ko kuma wani abun da aka kwashe masa albarka". Ta dafe ƙirji"tsinanniya kuma?". Na gyaɗa mata kaina"ƙwarai kuwa a duk lokacin da aka ƙira sunanki hakan na nufin ana ƙiran ki da tsinanniya ne". Ta yi shuru na lura gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jifa da ruwan gishiri, na dafa kafadunta cikin sigar ƙafafa gwiwa na ce"kar ki wani damu fa, ai har yanzu lokaci bai ƙure ba. Za ki iya sauya sunan zuwa duk sunan da kike so mai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98