Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ɗakin sanye da fararen kaya ya taɓo kafaɗana na ɗago kaina ina kallonsa yayin da hawaye yake zuba daga idanuna. Fuskarsa ɗauke da yalwataccen annurin yake share mini hawayen da ya ɓata mini fuska. Bai ce da ni komai ba haka ni ma Allah bai ba ni ikon yi masa magana a cikin mafarkin ba har na farka. Sai da na sauƙe dogon numfashi kafin na tashi na fito sai a lokaci na tuna ko ruwan alwala ba ni da da shi balle wanda zan wanke fuskana da shi. Duk abin duniya ya taru ya yi mini yawa, na tsaya a ƙofar ɗakin ina tunanin mafita. Ina tsaye La'aniyatu ta fito muka sakarwa juna murmushi ni da ita kafin ta ce"ɗazu na zo ai na ga ba ki buɗe ƙofar ba ya ya jikin nakin?". "Da sauƙi". "Kamar wani abun kike buƙata ko?". Na sauƙe numfashi kafin na ce"wallahi kin ga na tashi ne ba ni da ko ruwan da zan yi alwala da shi". "To bari na kawo miki mana". Har za ta juya na dakatar da ita"a'a indai akwai inda ake ɗebowa ki kwantata mini kawai. Ai ba zan dawwama kullum sai an ɗauka an ba ni ba, gwara tun yanzu na fara taimakawa kaina". "Da nisa fa kuma kin ga har yanzu gari bai gama yin haske ba. Ƙarfe biyar ne da wasu ƴan mintuna". Cikin ƙosawa da sauraron zancenta na ce"ni dai don Allah ki taimaka mini ki kwantata mini wajen sai kuma ki ba ni bokitin da zan ɗebo a ciki". Ba ta yi musu ba ta koma ciki ta ɗauko mini bokitin ta ba ni ta yi mini kwantancen wajen na yi mata godiya, duk yadda ta so ta raka ni ƙin yarda na yi duk da ba wani gane kwantancen natan na yi sosai, amma na gwammace na fita na nema da kaina. Sharau kan layin babu kowa sai kukan karnuka da ƙwaɗuna, haka na dinga tafiya har sai da na fice daga layin na shiga wani na yi ɗan tafiya kaɗan. Na tsaya ina ta rarraba idanu don ta ce da ni a farkon layin zan hangin fanfon jikin wani masallaci. Hamdala na yi yayin da na hango fanfon na ƙara sauri na isa wajen na buɗe na wanke fuskana, na kurkure bakina kana na yi alwala. Na cire ɗan kwalin kaina na shimfiɗa da niyyan yin sallan a kai, na ga an miƙo mini sallaya. Na tsorita sosai don ban ga mutum ba sai kawai gani na yi an miƙo mini abu. "Karɓi ki yi sallan a kai". Na ji an furta tare da ajiye mini sallayan a kan ɗan kwalin da na shimfiɗa, bai jira abin da zan ce ba ya nufi masallacin da saurin don lokacin har an shiga sallan. Na shimfiɗa sallayan na tada kabbara, a nutsu na gabatar da sallan har na iddar don jam'i na b masalallacin. Ban yi wani dogon addu'a ba na tashi don sa'ilin har an fara fitowa daga cikin masallacin. Na ɗeba ruwa a bokitin na ninke sallayar na riƙe a hannuna. Ina ta rarraba ido ganin ta inda mutumin zai fito amma shuru har aka gama fitowa sannan na ga ya fito. Ya na sanye ne da jallabiya doguwa kalan ruwan ƙasa sai wani ƙaramin hula a kansa fara sol ban ga fuskarsa da kyau ba abu ɗaya zan iya cewa na gani a fuskar sa shi ne sajen da ya kewaye fuskar. Yana isowa na miƙa masa sallayar bai karɓa ba ya tsaya kallona har sai da na zargu da kaina na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. Sai da ya gama yin sa ya sa hannu ya karɓa sallayan bai ce da ni komai ba ya juya ya tafi. Na daɗa gammo da ɗan kwalina na ɗaura bokitin a kaina na bar wajen. Ina isa gida na zuba ruwa a butan da Aminu ya kawo mini na ajiye shi domin yin alwala. Ragowar na shiga banɗaki na watsa a jikina saboda tun da na zo ban ga ruwa ba. Kayan jikina na mayar na fito. Ina zaune ina tunanin ta inda zan fara La'aniyatu ta shigo ta ajiye mini biredi a gabana na cira kai ina kallon ta"wannan fa?". "Na ki ne mana". "Wai ke Ummanki ba ta yi miki faɗa ne na yadda kike ɗauko abubuwa ki na ba ni. Bayan na san cewa kowa shi yake ci da kansa a cikin gidan da samar wa kansu dukkan wasu ababen buƙata". "Ai ba ta sani zan da nake ɗauko miki". Na waro idanuna waje"to ai kuwa ba zan ƙara amsa ba, don haka wannan ma ki ɗauka ki mayar da shi inda kika ɗauko. Daman ba yunwa nake ji ba kuma fita ma zan yi". Ina dire zancen ma tashi na ɗauko mata bokatin da ta ba ni na bata tare da godiya. Duk yadda ta so na karɓa biredin na tubure akan cewa ba na ji yunwa dole ta haƙura ta bar ni, muka fito tare da ita daga ɗakin na kulle ƙofar na ba ta ajiyar makullin. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 4️⃣6️⃣ Na daɗe tsaye a ƙofar gidan ina ta tunani da nazarin inda zan nufa, ban san sa'ilin da hawaye suka fara kwaranya daga koramar idanuna ba. Tunawa da na yi irin rayuwar da na yi a baya da kuma Abba sai dai har yanzu ba na dana-sani balle nadamar barin gida da na yi. Na yi imanin tun da uwar da ta ɗauki nauyin cikina tsawon wata tara da wasu kwanaki a jikinta, ta yi wahalar nishin naƙudana, ta shayar da ni daga jikinta na tsawon shekaru biyu, ta raine ni har na girma na yi wayo na zama mutum. Ta iya fito ɓaro-ɓaro ta bayyanawa duniya ba ta buƙatata ba ta ƙaunar ganina ta sallama ni a duniya to babu wanda zai iya jure zama da ni. Komai alaƙa, dangantaka da kuma ƙarfin igiyoyin zumucnin da suke tsakani. Na ja dogon numfashi na fesar daga bakina ina kawar da hawayen da suke gudu a bisa dandamalin fuskana, tafiya na soma yi har sai da na bar cikin layin ban yi gigin komawa layin gidajen da na je jiya ba. Sai da na kusa barin cikin unguwan, ƙafafuna sun yi futu-futu da ƙura na gama gajiya tilis sai da na nema waje na zauna na huta kafin na tashi na ci gaba da tafiyan na iso baki gate ɗin wani gida na ƙwanƙwasa ƙirjina yana tsananta bugu. Mai gadi ya buɗe ƙaramin ƙofan jikin gate ɗin bai ce da ni komai ba ya tsaya tsawon mintuna yana ƙare mini kallo. Na durƙusa har ƙasa na gaishe shi bai amsa ba ya soma zazzage mini buhun bala'i mini kamar zai cinye ni ɗanya. "Baiwar Allah lafiya za ki zo gidan mutane ki na yi musu irin wannan bugun kamar wanda kike bi fashi ko tara. Wace ce ke kuma daga ina kike?". "Baba aiki nake nema ko na wankau ko raino". "To kin ga gidan nan matar gidan ma ba mazauniya ba ce. Aiki take fita daga safe har yamma, sannan kuma ba ta ƴaƴa. Wanki kuwa suna da mai yi musu har da goga idan sun ga

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});