Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mutum ne don duk faɗin garin nan babu inda zan shiga ba a san sunansa ko an san shi a fuska ba. Rimi-rimi ya aiko aka ɗauke ta zuwa otel yarinyar nan ta burma masa wuƙa a cikinsa ta ji ajalinsa har lahira ta kwashe masa maƙudan kudaɗe ta tsallake boda, ta bar ni a cikin masifa da ha'ula'i aka yi mini rufgudu na yi trending a cikin garin nan. Da ƙyar aka same ta a can yankin sudan aka cafke ta kafin na sama salama, ke ma na lura wannan simi-simin da kike yi tsabar tsagwaron munafurci da iya ƙulla luggu". Ilahirin jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin cikin rauni na furta"Hajiya har cikin raina na yanke wannan hukuncin". Ta ɗan yi jim tana bi na da kallo kafin can cikin wani irin dakakkiyar murya ta ce da ni"ke yarinya sa idonki a cikin nawa ni ɗin nan da kike gani wargi ce daidai ƙugun ko wacce ƴar bariki da take jin karanta ya kai tsaiko". A hankali na cira kai na sanya idanuna a cikin nata sai dai na kasa jurar jimirin haɗa ido da ita babu shiri na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa ina sauraran zancen da ta ɗaura da shi. "Ina fatan abin da kika furta su kasance gaskiya don ina mai tabbatar miki da cewar duk abin da kika jangalo a kanki zai ƙare don duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka. Akwai sharruɗa da nake gindayawa duk wata yarinyar da take cikin gidan nan, duk wani namijin da kuka yi mu'amala da shi ina da kaso ɗaya cikin uku na abin da ya sallame ki ina fatan ki na saurarana?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta damar cewa"ki na da mutane a ƙasa ko kuma mu nema miki duk yadda kike da suran nan babu wanda zai gan ki ya ji ba ki burge shi ba balle har ya kau da kai". "Babu wasu a ƙasa". Na amsa mata muryata can ƙasa kamar an dannen kwaɓo a cikin ruwan zafi. "To ku shirya da dare bayan misalin ƙarfe takwas za ki yi baƙo". Kaina kawai na jin wani irin abu yana tasowa tun daga ɗan yatsana yana bin dukkan sassan jikina, na tashi cikin rashin kuzari da ƙwarin jiki zan fita na ji an ƙira sunana da hakan ya tilasta mini tsaya wa ba tare da na waigo ba. "Ke kuma La'aniyatu me ye ya fito da ke daga cikin ɗakin? Ke da kika ce ba ki da lafiya kanki yana yi miki ciwo". "Umma ni fa na warke. Sai ki yi ta garƙame ni a ɗaki kamar wata ƙaramar yarinya kuma na daɗe da gane manufarki akan hakan. Harkar da kike jawo ƴaƴan wasu cikinta ne ni ba kya so na bi wannan layin, ai an ce duk abin da ka shuka Umma shi za ka girba". Tsam Hajiya Babba ta miƙe"ke La'aniyatu ki san irin maganan da za ki na furta domin ni ɗin uwarki ce. Kuma duk lalacewa ta ba za ki sauya ni a matsayin mahaifiyarki ba kamar yadda duk lalacewar tuwo ba a sauya masa suna". "Ni ban ce zan sauya ki a matsayinki ba amma ina gaya miki abin da yake zahiri ne wanda ko ba ji ma ko ba daɗe ko kuma raye ko ba ma ciki rayayyu, babu makawa sai hakan ya faru....". Ba ta ƙarishe zancen ba Hajiya Babba ta zuga mata mari mai matuƙar sauri har sai da hancin cikina ya kaɗa. "Tsinanniya wacce ba ta san haƙƙin uwa ba, in sha Allahu ke kam ba za ki gama da wannan duniyar salin ƙalin ba. Da ba a cikin ɗakin nan na haife ki ba sai na ce sauya min ke aka yi a asibiti, duk ƙoƙarin da nake yi wajen inganta rayuwarki da ganin ba ki nema komai kin rasa ba La'aniyatu ba kya gani?" Ta ƙarƙare zancen cikin sanyin amon. Kasa motsawa na yi daga inda nake tsaye munanan kalaman Hajiya Babba suka jirkita mini tunanina, na tuna da Ummanta a lokacin da take jifa na da makamantan irin waɗannan kalaman wanda ina da yaƙinin su suka yi tasiri a kaina har na tsinci kai a cikin gidan karuwai da ƴan daudu. Ji na yi an ja hannun aka fizgo ni muka fice daga cikin ɗakin ba mu tsaya a ko'ina ba sai cikin ɗakina. Na fizge hannuna daga cikin riƙon da ta yi mini. "La'aniyatu me ye haka kike yi?". A zafafe ta mayar min da tambaya"me ye kika ga na yi?". Na watsa mata wani kallo don ban taɓa raina wayo, hankali da hangen nisanta ba irin na yau. "Hajiya fa mahaifiyarki ce ko me ye take aikatawa hakan ba shi zai ba ki damar da za ki na faɗa mata duk wani abun da ya zo bakinki, ba tare da kin tauna kalaman ba". "Ni yanzu ba wannan ba shin da gaske kike za ki bi hanyar da suke so?". Na harare ta da wutsiyar idanuna kafin na ce"ƙwarai kuwa". Ina dasa aya na wuce zan zauna ta jayo gefen hijabina. "Me yasa za ki aminci bayan kin yi wa kanki alƙawarin ba za ki aikata ɓarna ba? Ke ma kenan za ki zama ba ki da bambamci da ragowar matan gidan nan? Kin san yadda suke yin wulaƙantaccen ƙarshe kuwa? Wasun su su kamo da jinyar da za ta yi ajalinsu, wasu shaye-shaye ya haukatar da su yayin da wasu kuma tsufa yake cim musu duk waɗanda suke mu'amala da shi su yi ɓatan gado su gudu ko sama ko ƙasa. Idan ba ki yi sa'a ba kuma har da kuzurin cuta za ta jajiɓowa kansu wasu kuma su haifa shegu waɗanda ba su da uba, haka rayuwarsu da ta yaran za ta faɗa garari su zama abin wulaƙantawa da tozarwa a tsakanin al'umma". Na cire hannunta daga jikina na je na yi zamana ina cire hijabin da yake kaina"duk na san da hakan, me ye zan zauna na yi bayan ga abin da ya kawo ni nan ban yi shi ba. La'aniyatu duk matan cikin gidan nan ƙaryan bariki suke yi yanzu ne zan nuna musu ainihin abin da kalmar ta ƙunsa, domin zan warware musu zare da abawa. Ke dai kawai ki zuba mini ido ki kuma bi ni da fatan alkhairi". "Mata da yawa da haka suke fara har su zarje su zama jan wuya. Amatullah ina jiye miki tsoron abin da kike shirin aikatawa zai haifar miki a nan gaba, kin ga muranen nan ba su da tausayi balle imami da zarar sun fara nannaɗa garɗin mace to ba sa barin ta haka banza wallahi har malamai da bokaye suna bi, don wasu ba a cin kuɗinsu a zauna lafiya". Taƙaitaccen murmushi na yi kafin na ce da ita"ni kuwa zan ci kuɗin kuma lafiya sumul". "Amatullah". Ta ƙira sunana cikin wani irin yanayi da ya fi kama da na zallan mamakin da ba sirka shi da komai. Na ɗage mata idona guda alamar lafiya? Ta zo ta zauna a kusa da ni tare da riƙo hannuna za ta yi magana na dakatar da ita. "Ki zuba

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});