Chapter 39
Chapter 39
cira kai na yi mata kallo guda tare da janye idanuna daga gare ta. "Fita ni zan yi zuwa anjima can da yamma. Ku dafa abin da za ku ji don ba na jin ma su Saif za su dawo nan kusa". Tana dasa aya ta tashi ta bar cikin falon sa boda ƙirar wyarta da aka yi ta hau sama zuwa ɗakin da kallo na raka ta har ta ɓace wa ganina daidai lokacin da sautin Altine ya sauƙa a masarrafar naɗar sautina. "Idan kunne ya ji jiki ya tsira". Duk yanayin da nake ciki hakan bai hana ni sakar mata da murmushin ba duk da kuwa bai kai har cikin ƙasan zuciyata ba. Ta tashi ta bar ni a gantale a cikin falon ba tare da ta sanar da ni abin da zan yi ba, zafafan iska na fesar daga bakina ina ɗan lumshe idanuna da nake jin har wani zafi-zafi suke yi mini. Jin an fado kafaɗuna ya sa ni buɗe lumshashshun idanuna ina tsayar da su akan Ayan da yake tsaye a gabana yana rungume da dokin wasa a hannunsa. "Kuka kike yi?". Na girgiza masa kaina ina kai hannuna ina share hawayena da ya zubo daga idanunta don ban san lokacin da suka zubo ba. "Ummi ce ta yi miki faɗa shi ne kike kuka ko?". Na riƙo hannuna ina jinjina kaifin tunanin yaron na furta"Ummi ai duk ta fi mu shi yasa idan muka yi ba daidai ba za yi mana faɗa, sa boda rayuwarmu ta gyaru ba don ba ta son mu ba". Kallon da ya tsare ni da shi ya sa ni fahimtar kalaman da na yi amfani da su sun yi girme wa shekarun da har ya hana sa fahimtar saƙon da nake son a isar masa a cikin zancen. Na kai hannuna na shafo sumar kansa"ba faɗa Ummi ta yi mini ba ka ji?" Ya gyaɗa mini kansa alamar ya ji, daidai lokacin da Aryan ya iso wajen ya zo ya tsaya kawai yana kallona. Na ƙirƙiro murmushin dole na dasa a bisa fuskana kafin na kai ga furta"lafiya ka tsaya haka?". Ya yi rau-rau da ido yana ta faman dube-dube ya matso saitin kunnena kamar mai raɗa ya ce"Anti don Allah ki yi mana wanka jikinmu gabaɗaya ƙaiƙayi yake yi mana". "Wanka kuma? Ba a yi muku ba ne?". Da sauri Ayan ya janye Aryan daga kusa da ni yana faɗin"Aryan Uncle Saif ba ya hana ka yawan magana ba, ka zo mu yi wasan mu". Na cafko hannayensu gabaɗayan su ina kallon Ayan da gaba ɗaya ya bi ya firgice na lura ya fi Ayan tsoro nisa ba kusa ba. "Me yasa za ka ce ya yi shuru?". "Uncle Saif ya ce babu kyau yawan suturu". Ya ba ni amsa ba tare da ya yarda mun haɗa ido da shi ba. "Ba irin wannan maganar yake nufi ba. Yanzu dai ku zo mu je na yi muku wankan sai ku dawo ku yi wasan". "A'a yanka mu za ta yi". Ayan ya yi zancen hawaye suna ciko masa idanunsa ga jikinsa da ya soma rawa sosai. Cikin mamaki na ce"waye? Waye zai yanka ku kuma?". Duk su biyun suka sadda kawunansu ƙasa ba tare da sun ba ni amsa ba. Take na ji kifiyar tausayinsu ta ratsa zuciyata tare yin pieces da ita, jikina ya yi la'asar na rasa ta inda zan fara shawo kansu, sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi amfani da dabarar da ta faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu. "Ku zo mu je na yi muku wanka na shirya ku babu wanda zai ji". A tare duk su biyun suka ɗago kai suna kallona kamar za su miƙa wuya sai kuma Ayan ya jan hannun Aryan tana faɗin"ka zo mu tafi mu yi wasan mu". Daga haka ya janye shi suka koma inda suka wasan na bi su da kallo ina tunanin mafitar da ta dace. [12/3, 7:18 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________ Page 6️⃣0️⃣ Na yi ɗam jim ina ta tunanin ta yadda zan ɓullowa lamarin, can na ji wani dabara ta faɗo mini a cikin kaina tamkar faɗuwar aradu, na tashi na je inda suke wasan na zauna ina faɗin"ina ma zan yi wasan ku biyu ni kuma ni ɗaya". Duk suka ɗago ido suna kallona kafin can Aryan ya ce"kin iya ne?". Na gyaɗa masa kaina alamar e, ya miƙo mini motar guda ɗaya yayin da su ma suka dauki guda-guda, muka soma yin wasan ba mu yi nisa ba suka cinye ni lamarin da ya faranta musu rai da ruhi suka daka tsalle tare da ƙyalƙyalewa da dariya kamar za su shiɗe. "Mun ci mun cinye ki Anti". Na ɗaga ido na kalla Aryan da ya yi zancen na ce"ai gobe ma za mu ƙara gwadawa, yanzu dai tun da mun kama wasan ku zo mu je na yi muku wanka ku sauya wani kaya ku ji sanyi a jikinki". Kamar an yi ruwa an ɗauke lokaci guda fara'a da annurin fuskarsu ya ɗauke, duk su biyun suka yi shigo har sai da na kawar da shurun ta hanyar faɗin"idan ba kya so shi kenan bari na tashi na shiga ciki". Na yi zancen ina yunƙirin miƙe wa suka riƙo hannuna. "Anti mu je ki yi mana wankan". Murmushi kawai na yi musu muka wuce ɗakin nasun, na cire musu kayan jikinsu na ɗaura musu towel muka shiga cikin banɗakin na yi musu wanka da ruwan ɗumin da na tara a cikin bokati. Na wanke musu sumansu da mayuka da sabule gyaran gashin, na ɗauko musu towel ɗin muka fito na ɗaura su akan gadon suna ta jijjiga kansu yayin da ruwan da yake cikin sumarsu yake watso wa a jikinsa, suna ta kyalƙyala dariya. Na ke jikin wadrode ɗin kayansu na buɗe na ɗauko musu wata jamfa launin ruwan ƙasa. Ina juyawa Aryan ya ce"Anti ni kam ba zan kayan nan ba". Ina rufe bakinsa ya diro daga kan gadon ya zo ya zaro wani wandon jeans ya ce shi zai saka, yayin da Ayan shi kuma ya dage akan ba sai saka wannan wandon ba. "To shi kenan Anti kowa ya saka kayan da yake so kawai ko?". Aryan ya yi magana ina tsayar da idanunsa a kaina, na durƙusa a gabansa kafin na furta"ai ba zai yiyu ku saka kaya daban-daban ba, tare aka haife ku tare aka raine ku tare ku ka girma komai tare ake yi muku. Kun ga Ummi ba za ta ji daɗi ba idan aka saka muku kaya daban-daban". Ina rufe bakina Ayan ya ce"shi kenan Anti a saka wanda Aryan ɗin yake so kawai. Ni na haƙura ba na son Ummi ta ji ba daɗi". Sosai na ji yaron ya ƙara shige mini can ƙasan ƙalbina yaro ne mai matuƙar nutsuwa ga shi sam ba shi da hayaniya balle ƙiriniya irin na yara masu shekarunsa, a ɗan saman da na yi a cikin gidan nan a lura ya fi Aryan maƙon ɗan uwansa. Take Ayan ma ya tadae rigima ya ce shi ma ya haƙura a saka kayan da Aryan ɗin yake so, haka suka din ga yi har sai da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98