Chapter 18
Chapter 18
tsinkayo muryar Altine daga bayana tana faɗin"sun fita da Saifullah tun da ya dawo ya ce a shirya su za su fita". "Ina suka je?". "Bai sanar da ni inda za su ba, amma ina kyautata zaton idan suka saba zuwa suka je. Ki na son wani abu a kawo miki ne Hajiya?". Ta ɗan lumshe idanunta kafin ta ce"ba na buƙatar komai, ku fara shirye-shiryen girkin dare tare da Amatullah, don zan yi baƙi da daren nan akwai abokan kasuwancina da za su zo mu tattaunawa. Ku shiga kicin ɗin ku duba duk akwai abun da babu ko ake buƙarin a ƙaro sai ki zo ki sanar da ni". Daga haka ta tashi ta haura sama wanda nake kyautata zaton a nan ɗakinta yake. "To sai ki tashi mu je ko tun da dai kunnuwanki su ji abin da ta faɗa". Altine ta yi zancen cikin ɗaure fuska tana barin cikin falon, na yi wuf na tashi na bi ta a baya muka nufin kicin ɗin. Ta fara duddube-duddube can kuma sai na ga ta tsaya tare da dafe kanta ta juyo tana kallona. "Sai ki je ki tambayo Hajiyar abin da za a dafa, in ta faɗa sai na duba na ga abin da ya dace a sayo ko wanda za a ƙaro". "To". Na amsa da shi a taƙaice ina ficewa daga cikin kicin ɗin, ɗakin Hajiyar na nufa na tsaya daga ƙofar ina yin sallama sai da na yi baki biyu a na ukun ta amsa ban shiga don a tunanina bai dace na shiga har cikin turakarta ba a matsayinta na matar aure, don na sha ji n ana cewa ɗakin mace sirrinta ne. Ta fito jikinta ɗaure da farin towel da ya tsaya daidai gwiwanta, na rusuna na gaishe ta ta amsa mini cikin wani irin yanayin da gaba ɗaya na kasa gane kansa. "Amatullah lafiya?". Na ɗan duƙa kaɗan kafin na amsa mata cikin faɗin"daman Anty Altine ce ta ce na zo na tambaye ki abin da za a dafa". Ta ɗan shafo saman goshinta kafin ta ce"a yi fried rice, fine apple and coconut drink, sai a soya kaji a yi paper meat". Tana gama lissafa mini jerin gwanon abubuwan da za a yi ta koma cikin ɗakin tare da turo ƙafan ta rufe gaf, na ja ƙafana na koma cikin kicin na sanar da ita abin da ta faɗa, ba ta ce da ni komai ba ta ci gaba da abin da take yi. Ta nuno mini wasu albasa ta ce na yanka su yayin da take ficewa daga cikin kicin ɗin, babu jimawa ta dawo muka ci gaba da aikin tare sai dai ba ta ce wa da ni uhm balle umm da zaran ta ba ni umarnin abin da zan yi ba ta ƙara cewa da ni komai. Aka kawo wasu kayan wanda duk dangin kayan marmari ne, ta ce na wanke su na yi kamar yadda ta faɗa aka zuba tuban da ayaba da inibi a cikin wani ƙayataccen kwanon gilashi, aka haɗa wanda za a markaɗa a yi lemon da za a yi. Muna gama aikin ana ƙiran sallan magrib har wani juwa ne yake ɗiba na tsabar yunwar da nake ji, idanuna suka yi ƙulu-ƙulu har wani dishi-dishi nake hangowa. Muka haɗe komai muka jere shi akan dinnig table, ni na wanke kwanukan da muka yi amfani da su wajen gudanar da girki na tsaftace kicin ɗin tsaf. Kana na je na yi alwala a inda na yi alwala na nema wani ɗan wajen na shimfiɗa ɗan kwalina na yi salla, don ba na so na je falo Hajiya ta fito ta ganni ko kuma na iske ta a ciki na hana ta rawan gaban hantsi. Sai da na iddar da sallan na tashi na shiga ciki kamar yadda na yi tsammani kuwa na iske ta zaune a falon tana latsa wayarta da yake hannunta. Na durƙusa na gaishe ta ta amsa mini ba tare da ta ɗago kanta ta kalle ni ba. "Ina Altine take ne?". Bakin na ba ta amsa Altine ta iso wajen ita ma ta zube tana yi mata sannu da hutawa. Ba ta amsa ba ta ɗago kanta tana kallon mu gabaɗaya kana ta ce"Altine me yasa ba ki kai ta ɗakinki ba, ina daga ɗakina na hango ta ta taga na ga tana salla a cikin garden. Ki ja ta a jikinki don daga yau tare za ku na gudanar da dukkan ayyukan cikin gidan nan, sannan a ɗakinki za ta dinga yin komai idan ta zo gidan nan". "Ba matsala ranki ya daɗe yadda kika ce haka za a yi, ai faɗa na ki ne cika wa kuma nawa". "An zuba wa Saif abincin shi ne, sannan kuma kun ɗeba naku ne?". Altine ta gyara zama kafin ta ce"na zuba masa komai, sannan mu ma na ɗeba mana na mu". Ta jinjina kanta"to ku je ku ci mana, na ga dare yana yi kuma Amatullah za ta koma gida". "To ranki ya daɗe, tashi mu je ke kuma". Altine ta yi zancen tana kallona, ta tashi na bi ta a baya ɗakuna uku ne jere da juna a cikin falon wanda ɗaya na su Aryan ne, na tsakiyan kuma kamar a rufe yake ba a buɗe sa, na ƙarshen muka shiga wanda ya kasance nan ne ɗakin Altine ta ido ta nuna mini wajen zama tana faɗin"bari na je na ɗauko abincin". Na yi zumbur na miƙa"Anty bari na je na ɗauko". Ta galla mini harara"ki je ina ɗin malama? Dalla koma ki zauna ba na son kinibibi da rawar kan banza da na wofi". Tana dasa aya ta juya ta fice daga cikin ɗakin tare da bankaɗo ƙofar ɗakin har sai da ya ba ta wani sauti, a sanyaye na zauna na tallafe kuncina, har ta je ta dawo ban gusa daga inda nake ba ta shigo da kula da flate a hannunta ta dosara mini a gabana. "Ga shi nan sai ki ɗeba ki ci". Daga haka ta haye kan katifa ta yi kwanciyarta. Na fi mintuna biyar ban ce komai ba kafin na buɗe kulan sai dai da mamakina sai na ga ba abin da muka girka ba ne a cikin kulan, shinkafa muka girka da ta amsa sunanta sai dai a nan fara ce da mai da yaji ko wake babu wata yajin ƴan ɗis a saman shinkafan kamar an roƙo daga maƙota. Ban ce da ita komai ba na sa hannu na soma cin abincin duk daga loman farko na sha jinin jikina, don da ƙyar na haɗiye shinkafan ya wuce ta cikin maƙoshina tsabar bushewa da sanƙarewan da ya yi da alama ya shafe tsawon awannin a dafe. Haka na ci gaba da cin abincin ina ji kamar ina haɗiyan ƙarangiya, ba don yunwan da nake ji ba tabbas da na haƙura da abincin amma babu yadda na iya dole na ci tun da ba ni da wani zaɓi. Na gama ci na tashe zan je na mayar da kwana ta dakatar da ni. "Ki ajiye kulan a nan ki yi tafiyarki". Duk da kalamanta sun ba ni mamaki ainun amma ban nuna mata hakan ba, na yi kamar yadda ta ce na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98