Chapter 34
Chapter 34
yanzu a cikin raina. Ina fitowa na yi kiciɓus da zinariya tana ƙoƙarin shiga ɗakin na ƙirƙiri murmushin dole na aza a bisa fuskana. "Barka da safiya ranki ya daɗe". "Ai ke ce ranki ya daɗe, dama na zo na ƙara duba jikin nakin ne. Ban saman shigowa ba". "Ai na je na iske ki na waya sai kuma daga nan ban dawo ba. Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi....". Kafin na rufe bakina na ji ta rumgume ni tsam a jikinta kafin na yi aune na ji hannayenta a gadon bayana tana shafa wa har zuwa ƙunguna. Jikina na mutu murus na kasa cewa da ita komai kamar yadda na gaza hana ta yawo da hannunta da take yi a cikin jikina. "Bari na bar ki haka tun da na ga kamar fita za ki yi ko?". Zallar ruwan mamakin da ta shayar da ni ya hana ni amsa mata cikin kalmomin da bakin kan iya furta wa illa gyaɗa mata kaina da na yi. "To sai kin dawo idan kin dawo sai ki shigo mu yi hira". Na kuma gyaɗa mata kaina a karo na biyu ta sakar mini wani shu'umin murmushin yayin da take ɗaukar hanyar koma wa cikin ɗakinta. Na fita da kallo ƙirjina yana buga wa tamkar zai faso allon ƙirjina ya bayyano waje ya taka rawar disko, na daɗe tsaye a wajen kafin na ja sanƙararrun ƙafafuna da nake jin su tamkar ba za jikin gangar jikina na fice daga cikin gidan. Ina tafiya ina tunani har na isa ƙofar gidan ina jin wani masifaffen yunwa hancin cikina sai kuka suke yi da neman agaji, na ƙwanƙwasa gate ɗin Baba mai gadi ya fito ya buɗe mini na durƙusa har ƙasa na gaishe shi ya amsa mini fuskarsa tamkar gonar auguda. "Kin iso ko?". Na gyaɗa masa kaina alamar e. "To madalla Allah ya taimaka ya yi jagora". "Amin ya Allah". Na amsa da shi yayin da nake shiga cikin gidan ina shiga na hango motoci guda uku a cikin parking space, ɗayan Kam ko a ina na ganta zan gane ta don motar Hajiya Muhibbat ce. Ɗayan kuma motar Saif ne ɗayar ce baƙuwa amma tabbas a gare ni ba baƙuwa ba ce don ba yau ne rana ta farko da na fara ganinta ba. Ƙirjina ya harba da ƙarfin Rabbussamawati da hakan ya tilasta mini runtse idanuna Ina karanton a'uziya a cikin raina. "Ƴarta lafiya kuma na ga kin tsaya a nan, ba ki shiga cikin gidan ba?". "Baba wannan motar baƙo aka yi a cikin gidan nan?". Ya washe bakinsa kafin ya amsa mini cikin faɗin"wannan motar baƙon Saifullahi ne, da ya zo da yammacin jiya. Yaron kirki ne matuƙa ga girmama manya gami da tsantsan tarbiyya daɗin daɗawa kuma ga nutsuwa da kawaici". "Tabbas ya cika mutumin kirki tun da har ya sama yabo daga bakin uba na gari kamar ka". Ya washe bakinsa tamkar wanda aka yi wa wani babban kyauta"duk inda ake neman yaron kirki wannan baƙon ya zarce duk tunanin mai tunani. Ni ɗin nan idan ya zo cikin gidan na irin girman da yake ba ni na daman ne, in ya shigo ya ganni ina wani aikin kuwa sai ya karɓa ya yi min babu ruwansa da matsayinsa, matakin karatunsa ko kuma azurkinsa". Na riƙe haɓata"dole na zo a ba ni labarin wannan baƙo". "Ai kuwa za ki sha labari, don duk suna makaranta a nan gidan yake hutunsa har sai sun koma". "In sha Allah zan zo na sha labari". Daga haka na bar wajen na ƙarisa shiga cikin gidan, na tsaya a ƙofar falo ina ta zabga sallama har baki uku ba a amsa ba sai a na huɗun Ayan ya buɗe ƙofar ya fito, na fafaɗaɗa fara'ar fuskarta kafin na ce da shi"ina kwana". Ya tsaya ya yi sakeke yana kallona kafin can ya ce"ki shigo Ummin tana ciki". Murmushi na sakar masa na riƙo hannunsa muka shiga cikin falon. Na tsuguna har ƙasa na gaishe da Hajiya Muhibbat da na iske zaune a falon tana danna wayarta, yayin da Aryan take zaune a kusa da ita yana wasa da motar da yake hannunsa. "Lafiya ƙalau kin tashi lafiya?". "Lafiya alhamdulillah ranki ya daɗe". "Lafiya jiya kika tafi babu sanarwa sai aikowa na yi a ƙira ki aka ce ba kya nan?". "Hajiya ba na jin daɗi ne shi yasa na tafi, amma tuba nake yi". "Ba damuwa Allah ya ƙara sauƙi. Ki shiga kicin ku ci gaba da aikin don yau mu na da baƙo na musamman a cikin gidan nan". Kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na yi hanyar kicin ɗin na tarar da Altine a tsaya ta juya wa ƙofa baya tana waya. Na yi gyaran murya da hakan ya ankarar da ita wanzuwa ta a cikin kicin ɗin, a firgice ta waigo tana datse ƙiran. "Ke kuma me ye kike yi a nan? Yaushe kika shigo?". Ruɗewan da ta yi lokaci guda shi ya fi komai ba ni mamaki, sai na ƙariso cikin kicin ɗin kafin na ce"yanzu na shigo na tarar ki na waya. Ina kwana mun tashi lafiya?". "Lafiya". Ta amsa mini a daƙile tamkar wacce aka yi wa dole, ba ta ƙara bi ta kaina ba ta ci gaba da abin da take yi. Dankalin turawa take soya wa da ƙwai gefe guda kuma tana haɗa dafa shayi da ya sha kayan yaji dangin su citta da kananfari ƙamshi ya buɗe ko'ina. Ina ta tsaye ba ta ce da ni ga abun da zan yi ba har sai da na ji ƙafafuna sun gaji sun yi sanyi ƙalau. Sai da na tabbatar da cewa ba ta tanka mini na half ƙafafuna na isa wajen da ake ajiye kayan abinci na ɗebo fulawa zan tankaɗe ta dakatar da ni"me ye haka kike ƙokarin aikata wa?". Ba tare da na kalle ta ba na amsa da faɗin"wainar fulawa zan soya". "Wainar fulawa kuma?". Ta maimaita cikin isa da taƙama kafin ta zarce da cewa"wani irin wainar fulawa kuma? Bayan ga abincin karin kumallo nan ina girka wa ko ba kya gani ne?". Ban ce da ita uffan ba hakan bai hana ta ci gaba da maganar ba tamkar mai amayar da wuta. "Babu wani wainar fulawan da za a yi a cikin gidan nan tun da ga abinci nan na girka. Duk wanda ba zai ci ba sai ya wuni da yunwa ai yunwa ba uwar kowa ba ce kuma ba a fushi da abinci ko ka yi ma kai ne a wahala". "Ai na ji Hajiya ta ce akwai babban baƙo a cikin gidan kuma ta ba da lasisin a girka duk abin da ya kamata don a faranta masa. Laifi ne don na girka wannan?". Na ƙare zancen da alamar tambaya, lamarin da ya fusata ta ainun ta yi watsi wani kallo tamkar za ta kai mini bugu tana gallo mini harara kamar idanunta za su faɗo ƙasa. "Sai kuma aka ce da ke baƙo irin baƙin da kika saba ji da gani ne ko? To wannan baƙon babban mutum ne da ya fito daga gidan manya, ina mai tabbatar miki da cewar ko kallon wainar fulawan nan ba zai yi ba balle
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98