Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 48

Chapter 48

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zo na iske shi a ciki, har na tashi na ji wayarsa da yake ajiye akan teburin ta soma ruri kamar ba zsn kula ba sai kuma na ɗauki wayar ban tsaya duba wanda yake ƙira ba na kara wayar a kunnena ina magana ciki sarƙafewar harshe da cushewar numfashi. "Don Allah ku taimaka mini Yallaɓai ne ba shi da lafiya. Gashi nan ko motsawa ba ya yi kamar ma ba ya yin numfashi". "Ina mai wayar? Ina shi Saifullah ɗin?". Aka jeranta mini tambayar a haɗe sai da na juya na kalle shi har yanzu bai motsa ba kafin na ce"ga shi nan a shi da lafiya ne". "Yana ina yanzu?". "Yana gida a cikin sashinsa". Aka ɗan yi shuru kafin can aka ce"ki karanta suratul Baƙara a cikin wuta ki shafa masa a fuskarsa, sannan idan inda yake akwai fanka ki kashe su sannan ki rufe tagogi, ki aiwatar da abin da na ce miki ba tare da kin katse ƙiran ba". Tamkar ina gabansa haka na gyaɗa kaina alamar duk na saurara abin da ya faɗa kuma na fahimta, na je na ɗauki ruwa na karanta ayoyi goma na farkon Suratul Baƙara na tofa a cikin ruwan, na sa hannuna na ɗeba na yarfa masa a fuskarsa na yi hakan har sau uku amma bai ko motsa ba balle na kai ga saka ran sai buɗe idanunsa har numfashinsa ya dawo. Ban san lokacin da na fashe da wani kukan ba ina rarumar wayar na mayar da ita kunnena ina faɗin" ka ga har yanzu fa bai tashi ba, ko buɗe idonsa ma bai yi ba". Da ƙyar na ƙare zancen sa boda wani gigitaccen da ya ƙwace mini. "Ki nutsu ki kwantar da hnakalinki sai mu yi tunanin mafita. Kin rufe tagogin?". "A'a yanzu zan rufe". Na furta ina miƙe wa na je na rufe tagogin kana na kashe fanka. "Ki lulluɓe masa jikinsa da bargo mai nauyi sannan ki zauna a kusa da shi ki na ci gaba da karanto masa karatun". "Ka na ga zsi tashi kuwa?". Na jefa masa tambayar cikin sarewa da kuma cire tsammani. "In sha Allah ke dai kawai ki yi abin da na ce". Ban iya amsa masa da kalmomin da baki kan iya furtawa ba, na hanzari na haura sama na shiga cikin ɗakinsa na ɗauko bargon da na gani akan gadon na fita. Garin sauri na zame daga matattakalan benin sai ji na na yi a ƙasa tim, ƙuguna ya bugu sosai da har sai da na runtse idanuna ina cije leɓena sa bosa azabar zafi da zogin da na ji ya ratsa cikin kwanyata. Da ƙyar na tashi ina dafe jikin gini har na iso inda yake na lulluɓa masa bargo a jikinsa tun daga ƙafarsa har zuwa kafaɗuna, na zauna a ƙasa kusa da kansa ina ci gaba da karatun a hankali cikin muryar kuka. Ban gushe ina karantun har sai da na ga ya soma motsa ƙafafunsa zuwa hannayensa, sai dai har izuwa lokacin bai buɗe idanunsa ba. Wasu hawayen suka gangaro daga cikin koramar idanuna, zan iya cewa tun da Uwata Hafsatu ta haifo ni cikin wannan duniyar ban taɓa ganin irin wannan rashin lafiyan da numfashin mutum zai ɗauke gabaɗaya, jikinsa ya sandare kamar itace ba. Tun ina karatun da tunani da burin zai buɗe idanunsa har na soma karaya na ɗauki wayar da nufin ƙiran lambar da muka yi waya da mai ita. Na ga wayar da lambobin sirri da hakan yake nufin ba zai iya aiwatar da komai da ita ba, tagwayen ajiyan numfashi na sauƙe tare da ɗaura kaina jikin kujerar da yake kwance akan ta, na koma yin karatun a cikin zuciyata don baki ya yi mini da hakan ya hana ni furta ko da kalma guda. Rurin da wayar ta soma yi shi ya sanya ni zabura na ɗauko kaina zan ɗauki wayar idanuna suka sauƙa akan fuskarsa. Yana zaune akan kujerar ya jingina bayansa a jikin kujerar tare da cije leɓansa. Idanunmu suka sarƙafe cikin na juna wani kukan ya ƙara kubce mini mai haɗe da farin cikin ganin ya buɗe ido har ya tashi ya zauna. Wayarsa da yake kusa da ni ya kai hannu ya ɗauka da hakan ya tilasta mini janye idanuna daga gare sa. "Za mu yi magana an jima kaɗan yanzu ba na jin daɗin jikina inna dawo daidai zan ƙira ka". Ban san me ye aka ce masa daga ɗayan ɓangaren ba sai ji na yi ya furta"waye ya sanar da kai ba ni da lafiya Sultan?". Ban san amsar da aka ba shi ba a taƙaice ya ce"ok". Daga haka ya datse ƙiran ya ajiye wayar yana lumshe idanunsa tare da furzar da zazzafan iska da bakinsa da har sai da na ji sautin fitarsa. Muryarta a shaƙe na ce"sannu ranka ya daɗe ya jikin?". Bai amsa mini ba illa idanun da ya tsura mini kamar zai cinye ni da ido, dole na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa sa boda kwarjini da cika idon da yake da shi. "Za ki iya tafiya". Kalaman da ya saka mini da su kenan bayan sautin maganarsa ya fita raɗau, na saci kallonsa na ga ya mayar da idanunsa ya lumshe su, sai dai har yanzu numfashinsa bai daidata. "Allah ya ƙara sauƙi". Na furta yayin da nake tashi na fice daga cikin falon ina goge fuskana da hawaye ya damalmala mini shi. Ƙarar rufe ƙofar da ta yi shi ya sanya Saif buɗe lumshashshun idanunsa yana bin ƙofar da kallo daidai sa'ilin da wayarsa ta soma ruri. Sunan Sultan ya bayyana cikin screen ɗin wayar. Sai da ƙiran ya kusa tsinkewa kana ya ɗaga bai sanya a kunnensa ba maimakon hakan sai ya sanya ta a amsa-kuwwa. "Saif". "Ina jinka". "Ya jikin nakan? Wallahi hankalina ya tashi sosai da na ji halin da kake ciki". Sai da ya cije naman leɓansa kafin ya ba shi da faɗin"da sauƙi fa yanzu yadda nake ji na ma zan iya wasan polo da ingarman doki, sa boda ƙarfin da nake ji a jikina". Murmusawa Sultan ya yi kafin ya ce"daman har yanzu ka na fama da wannan lalular Saif? Na yi tunanin zuwa lokacin abubuwan sun yi sauƙi ba kamar da ba". "Babu abin da ya sauya daga abin da ka sa ni Sultan". Shuru ya biyo bayan zancen Saif na ƙarshe. Sai can ya ce"wace ce yarinyar da ta ɗauki wayarka muka yi waya da ita? Don na san gidanku babu ɗiya mace". A dake ya furta"ni ma ban san ta ba". "Mu bar maganar wasa mana Saif, wace ce?". "Ka riga da ba wa kanka amsa tun da tun farkon zancenka kai ma ka ce gidanmu babu ɗiya mace". Dariya sosai Sultan ya yi sai da ya tsagaita ya furta"any way ko ma dai wace ce, tabbas ta shiga cikin firgici ganin halin da kake ciki ka ji yadda take kuka kuwa tsakanin da Allah. Tambaya kuwa ta yi min ya kai sau ashirin akan za ka tashi kuwa? Na ce da ita in sha Allah, ba don ta zo akan lokaci ba Saif wataƙila da yanzu wani labarin ake yi ba wannan ba. Ko wace ce wannan yarinyar haƙiƙa ta ceto rayuwarka

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});