Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 92

Chapter 92

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nuna maka cewa ba ka kai ka kafa mini umarni na bi ba. Yaya Alhassan na tuba na you nadama na gurfana a gabanka ina neman afuwa da yafiyarka". Falon ya yi tsif babu abin da ake ki face sautin kukana. Cikin taushin murya Yaya Alhassan ya soma cewa"Amatullah ba ki yi min komai hasalima kin yi tunanin da ni kaina ban yi shi, wallahi na ji daɗin abin da kika yi na kuma cika da alfaharin kasancewarki ƴan uwa a gare ni. Kin yi wani babban lamarina da ya dace a yaba miki kuma a jinjina miki". "Ƙwarai don tabbas kin zamo silar wanzar da haske a cikin rayuwata kin haska min hanyar da zan yi tafiya ba tare da ɗan jagora ba. Ba zan da wani baki zan yi miki godiya Amatullah". Muhammad Taukif ya yi zancen cikin sanyin murya harrufan har suna harɗe wa waje guda. "Ba na buƙatar godiya don na yi hakan ne domin Allah ba don a gode mini ba". Na yi zancen cikin ƙarfin tare da tashi na koma cikin ɗaki ina shiga na zubo akan katifa ina ci gaba da kukan, na daɗe ina kukan har sai da na ji numfashina ya toshe. Lokacin Anty Sawwama ta shigo cikin ɗakin ta din ga lallashina da ba ni baƙi. "Tashi ki je falo ki same su don ke suke jira". Ta yi zancen ta na goge mini hawayen da suka ɓata mini fuskana, kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na fito kamar yadda ta umarce ni. Kaina a ƙasa na fito falon bakina ɗauke da siririn sallama na ƙariso na zauna a ƙasa, shuru-shuru cikin mu babu wanda ya yi magana kafin can Muhammad Taufik ya yi kawar da shurun. "Ni dai kam ba zan iya daina yi miki godiya ba, kuma ina so na ƙara tabbatar miki da cewar abokina yana yi miki ingantacciyar soyayya ina ji a jikina shi ne mijin da ya dace da ke, don haka ina fata da addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakaninku". Ban iya amsa wa da baki ba sai a cikin zuciyata na amsa. Har ya tashi ya fita daga cikin falon yana tsokalan Saifullah ban ɗago kaina ba. "Amatullah". Na tsinkayo muryar Saifullah a kunnuwana, ban amsa ba illa ɗaga kai da na yi ina kallon sa ido cikin ido a karon farko a cikin rayuwata. Kamar an buɗe fanfo na ji hawaye suna zuba daga idanuna. Da ƙyar na buɗe bakina na yi magana"ina ta jir ƙiranka shuru idan na ƙira kuma ba ya tafiya, ka san girman tashin hankalin da na shiga kuwa?". "Ban sani ba sai dai yanzu ki sanar da ni". Babu shiri na watsa masa harara da wutsiyar idona ina goge hawayen idona. "Afuwan ranki ya daɗe na san na aikata gagarumin laifi. Tashin hankalin ganin Sultan cikin halin da ya shiga shi ya hana ni kunna wayata, Sultan ya shiga tashin hankalin da ko maƙiyinsa ne sai ya tausaya masa har ma ya zubar masa da hawaye, don har kwanciya ya yi a gadon asibiti ya shafe kwanaki uku ba tare da ya san inda kansa yake ba. Wannan tashin hankalin shi ya hana ni samun lokacin wayata balle har na ƙira ki, amma yanzu na kawo kaina a yi min ko wani irin hukuncin da ya dace da ni". Ban iya cewa da shi komai ba illa kukan da na ci gaba da yi, ban yi aune ba na gan shi zaune a gabana dan da ni ina ɗago kai muka haɗa ido da shi. "Don Allah ki daina wannan kukan idan ba so kike yi ni ma na fara hawayen ba". Yadda ya furta zancen ya sanya jikina gabaɗaya sanyaya tabbas yadda na ga idanunsa sun kaɗa sun yi jajir ga jijiyoyin kansa sun fito sun yi ɓaro-ɓaro a saman goshinsa hawayen ma idan ya yi ba zan yi mamakina. Ba don na daina jin zafin da nake ji a cikin ƙirjina ba na kai hannu na goge hawaye fuskana, ya furzo mini iska daga bakinsa a fuskana da har sai da na lumshe idanuna. "Yauwa ko ke fa, to yanzu an yafe min ne ko kuma?". "Ai daman babu abin da ka yi". "Ni dai ki ce kin yafe min sai na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa". "To shi kenan na yafe maka, Allah ya yafe mana baki ɗaga". "Amin ya Allah". Daga haka na yi shuru har sai zuwa lokacin da ya ce"to yanzu kuma me ye ya rage?". Na ɗage masa ido ɗaya alamar rashin fahimta da hakan ya sanya sa faɗin"ko sai na tuna miki alƙawarin da kika yi kafin ku fuskanci idan maganan tawa ta dosa?". Numfashi mai nauyi na sauƙe kafin na sama zarafin cewa"na ba ka dama Saifullah ka turo iyayenka gidanmu, don su nema maka aurena". A kunyace na ƙare zancen ina rufe fuskana da tafukan hannayena. "Alhamdulillah". Ya furta yana yin sujudul shukur ga Ubangiji, ya ɗago ya ɗaga hannayensa sama yana addu'a cikin tsananin farin ciki. "Allah na gode maka bisa wannan damar da ka ba ni. Ina roƙonka ka ba ni ikon killace soyayyarta a cikin zuciyata ba tare da na haɗa ta da wata ɗiya mace ba, Allah ka ba ni ikon riƙe ta bisa amana na kuma inganta rayuwarta ta hanyar da ta dace. Ka hana ni yi mata kishiya har abada". Ganin na yi shuru ban amsa ko ɗaya daga cikin addu'o'insan ba ya sanya faɗin"ba ki amsa ba ke nan?". "Na amsa a cikin zuciyata". "To ki amsa da bakinki na ji". Na taɓe fuska ina faɗin"na amsa a cikin zuciyata fa". "Na amsa a cikin zuciyata fa". Ya yi zancen cikin kwaikwayon muryata da salon yadda na yi zancen, sunkuyar da kaina ƙasa na yi sa boda kunyar da ya lulluɓe ni. "Wai kunya kike ji? Uhmm! To yanzu idan kin shiga ciki ki sanar da su cewar iyayena za su zo jibi in sha Allah". Babu shiri na ɗago kaina"da sauri haka?"? Ya ɗage mini giransa ɗaya"to me ye za a jira". Ya ƙare zancen yana sunkuyo da kansa daidai saitin fuskana. Babu shiri na tashi na yi ciki da sauri sa boda kunyan da ya gama ba ni. Ɗakina na nufa na zauna na tsawon awanni ji nake yi saƙayau duk wani damuwana ya hau, zuciyata ta yi fes yayin da raina ya yi tas, haka na wuni cikin karshashi da ƙwarin gwiwan da ya zagaye jikina da yamma muka yi waya da Amira na sanar da ita komai ta taya ni murna matuƙa, ita ta hanyar ni shawaran na ƙira Anty Zulaihatu na sanar da ita zancen zuwan iyayen Saifullah jibi na yi na'am da shawaranta. Mu na gama waya da ita na ƙira Anty Zulaihatu na irge masa komai, Baiwar Allah har da kaddara kafin ta shiga rero mini ruwan addu'a ta kuma shaida mini a ranar za ta ƙira Anty Sawwama da Yaya Alhassan ta shaida musu zancen. Daren ranar mun fi awannin biyar muna waya da Saifullah yayin da na ji ya ƙara shiga cikin raina sosai, ya ba ni Hajiya Muhibbat muka gaisa a waya har da kukanmu ni da ita. Washe gari tun da asuba Anty Sawwama ta

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});