Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 93

Chapter 93

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ƙira don ta ji daga gare ni akan abin da Anty Zulaihatu ta ƙira ta sanar mata, na kuwa tabbatar mata da zancen ta yi hamdala tare da yi mana addu'a. Take aka soma shiri da shirye-shiryen tarban iyayen Saifullah gobe ranar Anty Zulaihatu a gidan ta kwana, washe gari da yamma lilis magabatan Saifullah suka zo su gidan Anty Sawwama neman aurena a hannun Yaya Alhassan aka kuma ba su tare da sanya auren nan da sati huɗu masu zuwa. Ranar wuni na yi da zazzaɓi da boda fargaba da zulumi da dare muka sha kukanmu tare da Anty Sawwama da Anty Zulaihatu sa boda tuno Abba da muka yi da hashashen irin farin cikin da zai yi don ganin wannan ranan in da yana raye. Bayan kwana biyu Amir ya ɓullo da wani zancen wai na je na yi gwajin genotype, Anty Sawwama ta yi kai da fata ta ce ba zan je ba, har da faka hujja da cewar su a lokacinsu duk ba a yin wannan gwaji ga shi kuma har suka gama haihuwarsu lafiya sumul, daga su har ƴaƴan. Sai da ta ga shi ma kansa Saifullah ɗin ya goya bayan a je a yi gwajin sa boda gujewa afkuwar matsala, sannan ta saduda ta zubar da makaman yaƙinta. Muka cire ranar da za mu je mu yi gwajin lokacin ana sauran sati uku bikin, duk da tun kafin lokacin shi Saifullah ya shaida mini cewar na shi AS ne don ya daɗe da sanin hakan. Rananr gwajin tare muka je da Anty Zulaihatu da kuma Umar muka je aka yi mana gwaji ni da shi, aka je mu ɗan jira kafin sakamakon ya fito haka muka jira aka fito sakamakon Saifullah da Umar suka shiga amsowa. Babu jima wa suka fito ba su ce da mu komai ba muka shiga mota muka tafi, maimakon mu koma gida sai muka ƙara wuce wa wani asibitin, Anty Zulaihatu ta gaza jurewa har sai da ta tambaya ko lafiya suka ce da ita lafiya kawai su na so tabbatar da wani abu ne. Wani gwajin aka ƙara yi mana, kamar karon farko Saifullah da Umar ne suka shiga suka also sakamakon. A wannan lokacin yanayin da suka shiga ya yi muni sosai haka muka shiga mota zuwa gida ya faka a ƙofar gidan, ya ce mu shiga ciki ga shi nan shiga wa, haka muka sauƙa ni da Anty Zulaihatu muka shiga cikin gidan, kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa. [12/27, 5:50 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 8️⃣1️⃣ Tun da muka shiga cikin gidan na kasa zaune balle tsaye ɗaki na shiga na yi ta safa da marwa, yayin da tunani kala-kala suke ziyartar ƙaramar curin kwanyata. Cikin wannan halin Anty Zulaihatu ta shigo ta ƙira ni ta ce na zo falo ana nema na, haka na biyo ta a baya har suka iso cikin falon inda muka iske Umar da Anty Sawwama zaune a cikin falo. Muka ƙariso ciki muka zauna. "Da kuke asibitin ya ya aka yi? Na ga kamar gabaɗayanku hankalinku ba a kwance yake ba. Ko dai wata cutar aka ce ɗaya daga cikinku yana ɗauke da ita?". Anty Sawwama ta yi tambayar tana kafe Saifullah da ido da ya kasa cewa uffan illa sadda kansa ƙasa da ta yi. Anty Zulaihatu ne ta yi magana a madadinsa"wallahi Umma mu ma ba mu san abin da yake faruwa ba, sun dai ce mu shigo ciki ne kawai ba tare da sun sanar da mu komai ba". Takardan sakamakon gwajin Saifullah ya miƙa wa Anty Zulaihatu ta amsa yayin da yake koro jawabansa. "Mun je asibitin farko aka yi gwaji inda sakamakon ya nuna cewa ni da ita Amatullah gabaɗayanmu AS ne, daman ni na san nawa na zo ne don a ƙara tabbatar wa, ban yarda da sakamakon don a wasu lokutan ana samun matsala dangane da kayan aikin gwaji ko kuma daga su kansu ma'aikatan hakan ya sa muka ƙara zuwa wani asibitin aka ƙara gudanar da wani binciken, nan ma ba a sama canji daga wancan gwajin na farkon ba. Tabbas ta tabbata ni da Amatullahi dukkan mu AS ne". "Me ye hakan ke nan ya ke nufi ɗan nan? Shi AS ɗin mene ne aibunsa? Ni fa shi yasa tun farko ban yarda aje a yi wannan gwajin ba sa boda gudun wanzuwar matsalolin da wannan nan mutanen masu jajayen kunnuwan nan suka kawo". "Umma hakan ya nufin aure a tsakaninsu ba zai taɓa yiyuwa ba, sa boda ko da an yi auren matsaloli da tashin hankalin da za su biyo bayan auren sai ya tushe duk ginin soyayyar da aka yi ta wargaza komai". Anty Zulaihatu ta yi zancen tana juya farar takardar sakamakon gwajin da yake riƙe a hannunta. "To sai me ye don dukkan su AS ne? Mu da can a lokacin mu ana wannan gwajin ne amma ba ga shi mun yi auren mun haihu lafiya sumul ba. In sha Allah babu abin da zai hana auren Saifullah da Amatullah". Anty Sawwama ta yi zancen tana tashi ta yi shigewarta cikin ɗakinta, da kallo dukkaninmu muka bi ta kafin Anty Zulaihatu ta saka salati cikin tsananin damuwa da rashin mafita da kuma madafa. "Anty yanzu ya ya za a yi a fahimtar da ita illan da yake tattare da hakan?". Saifullah ya yi zancen muryarsa har rawa take yi yayin da yake tsayar da idanunsa akan Anty Zulaihatu. "Wallahi ban san yadda zan yi wa Umma bayani ta fahimta illan wannan abun ba. Amma bari na ƙira Yaya Alhassan na sanar da shi halin da ake ciki". "A'a kar ki ƙira shi alhalin yana can wajen aikinsa, idan ya dawo kawai ki yi masa bayani ni ma in sha Allah zan ƙira shi mu yi magana a waya". "To shi kenan duk yadda ka ce haka za a yi". Sai a lokacin Umar ya buɗe baki ya yi magana damuwa jingim a tattare da furucinsa"ni na ma rasa abin da zan ce, gabaɗaya lissafina ya katse". Dafo kafaɗarsa Saifullah ya yi cikin salon ƙarfafa masa gwiwa ya soma faɗin"haka Allah ya ƙaddara Umar, sannan ko wani Bawa ba ya wuce ƙaddararsa a rayuwa. Wataƙila Allah bai ƙaddara akwai aure tsakanina da Amatullah ba. Mu ƴan Adam ne kawai muke lissafinmu amma tun kafin wanzuwan mu a bayan ƙasa ya rubuta abin da zai kasance da Bawa, mussamman a sha'anin aure ka san an ce wani ba ya auran matar wani". Anty Zulaihatu kam kasa jurewa ta yi ta tashi ta bar cikin falon ta na matsar ƙwalla, daga bisani ma Umar tashi ya yi ya fita. Ban taɓa zato da tunanin cewa tashin hankali idan ya girmama ba a ma samun damar zubar da ƙwalla ba, sai da na tsinci kaina cikin wannan matsanancin halin. Duk yadda na so na zubar da hawaye na kasa yin hakan idanuna ya bushe ya soye tamkar na soyayyan kifin da aka tsamo daga cikin mai. Na yi nisa cikin tunanin da na dulmiya a cikinsa na tsinkayo muryarsa dab da ni da hakan ya ba ni tabbacin cewar ya sauya wajen zama ya dawo kusa da inda nake zaune. "Amatullah

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});