Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 75

Chapter 75

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ruwan sama ta yi mata mungun bugu. "Yaya Alhassan duniyar gabaɗaya ta fara ba ni tsoro komai na cikinta ya daina burge ni. Tabbas iyaye daban suke a cikin dukkan jerin mutanen shi kenan Abba ya tafi ya bar ni yanzu ma Umma ta bi shi, ina zan saka raina? Ina zan soma kaina na ji sanyi da sauƙin halin da nake ciki? Wallahi zuciyata zafi take yi mini raina yana tafasa tamkar ƙirjina zai fashe. Na daina samun bacci tunani ya yi mini yawa har ina tsoron zuwan wani rana da za su zo ku tarar da gawata a cikin ɗakin nan, zuciyata ya buga na mutu kowa ya huta". "Ke Amatullah". Yaya Alhassan ya dakatar da ni cikin kakkauran amo, ban iya ɗaga ido na kalle shi ba illa rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa da na yi wasu hawaye su na ci gaba da ambaliya a bisa kuncina suna zarce wa har izuwa tudun wuyana. Sai da ya sassauta amonsa kafin ya zarce da faɗin"Amatullah ki zama mai tawakkali, haƙuri da miƙa lamuranki ga Allahu malikulƙuddusu mana. Sarkin da ya yi mana alƙawarin komai tsanani yana tare da sauƙi haka nan komai duhun dare hasken alfirjir zai keto ya yi wannan baƙin duhun daren. Allah ba ya taɓa jarabtar Bawa da abin da ba zai iya ba don haka ki lallashi zuciyarki ki ba ta haƙuri akan wannan jarabawan da suka faru da ke. Ki sani Allah ya na tare da masu haƙuri kuma a ko wani irin yanayi su ne da riba. Zuciyata ta kan cika da rauni a duk lokacin da na zo na iske ki a cikin ɗakin nan kin yi shuru ki na tunani, zuciyata ta kan karaya a duk lokacin da na zo na tarar da ke ba kya iya furta komai illa kallo da ido. Amatullah ina jin ki har a cikin ƙasan raina ke ɗin ƴar uwata ce kuma jinina, duk wani abun da ya shafe ki ina ji kai tsaye tamkar ni ya shafa". Shuru na yi ina ci gaba da sauraron zancen da ya ɗaura da su cikin sanyin amo da sigar lallashi"Amatullah ina ji a jikina in sha Allah rayuwarki za ta inganta. Matuƙar ina raye a cikin wannan duniyar ba zan taɓa bari ki yi kukan maraici ba, zan tsaya miki a cikin ko wani irin yanayi na daɗi ko akasin hakan. Zan yi amfani da gumina wajen ganin na faranta miki, ina so ki sama nutsuwa ki yi tunani da zuciyarki ki duba ki ga abin da kike ganin ya dace ki yi wanda zai taimaki rayuwarki, in ma karatu ne, sana'a ko kuma aure" . Babu shiri na ɗago kaina ina bin sa da kallo cikin rawar harshe na furta"aure kuma Yaya Alhassan?". Ya gyaɗa mini kansa cike da tabbatarwa ya ce"aure mana Amatullah me ye za ki zauna ki yi a cikin gidan? Ke fa yanzu ba yarinya ƙarama ba ce kin yi girman da kin mallaki hankalinki kanki. Aure shi ne rufin asirin ko wacce ɗiya mace komai gatanta, komai dukiyarta, komai iko da izzarta ke ko da kuwa uban ne ya fi kowa kuɗi a kaf cikin nahiyar Afrika da kewayenta aure shi ne cikar mutumcinta. Duk wani farin ciki, nutsuwa da kwanciyar hankalin mace ta na samunsa ne a cikin gidan aurenta amma idan ta yi dace da samun abokin zama na gari. Wanda ya san kima da darajarta". Bai gama maganar na dakatar da shi cikin faɗin"Yaya Alhassan to ni yanzu waye ma kake ganin zai iya aurena? Aure fa baban lamari ne alaƙa ce da in an ɗaura ta ake fatan ta ɗaure har zuwa ƙarshen numfashi. Ko Annabinmu cewa ya yi idan ɗayanku a tashi aure ya zaɓi ƴar gidan mutunci, mai kyakkyawan nasaba da asali, mu faɗa wa kanmu gaskiya duk waɗannan abubuwan babu su a tare da ni. Kar ka manta ta fa har ciki na yi ba tare da aure ba, na sa ƙafa na tafi can wata uwa duniya na yi zaman kaina. Idan tarihi da asali za a bi shi ma babu wani kyakykyawan abin da za a tarar, ko ka manta ni ce wannan ɗiyar da duk unguwa suka shaida cewan mahaifinyarta ta raina mahaifinta ba ta ganin kowa da gashi? Shin waye zai iya yin jihadin haɗa zuri'a da mace mai irin tarihina? Yaya Alhassan akwai hanyoyin bautawa Allah wanda duk wanda ka yi daga ciki da ikilashi zai kai ka zuwa aljanna, ba dole sai ta hanyar aure ba". Tun da na soma zancen ya yi shuru yana ta kallona ba tare da ya ce komai ba har sai da na kai aya. Ya ja dogo numfashi ya fesar kafin ya furta"aure ya zama dole Amatullah. Shi zai goge duk wani mummunan abun da yake cikin tarihinki, aure ne zai ba ki damar hayyafa ta yanda ko bayan ranki za a ga zuri'arki a tuna da ke har a yi miki addu'a". Cikin zubda ƙwalla na ce"akwai wani burin da nake so na cimma". "Wani irin buri ne?". Kafin na kai ga ba shi amsa Umar ya yi sallama a ƙofar ɗakin duk muka juya muna kallonsa, Yaya Alhassan ne ya amsa masa sallamar da hakan ya ba shi damar shigowa ciki tare da cewa"Yaya daman baƙi aka yi, sun zo gaisuwa kuma sun ce su na buƙatar ganin Amatullah ita ma su yi mata gaisuwa". "To koma ka ce ta na zuwa". "To Yaya". Ya amsa da shi a taƙaice yana juya wa ya fita daga cikin ɗakin. "Sai ki tashi ki shirya tun da kin ji akwai baƙin da suka zo gaisuwa ko?". Kaina kawai na gyaɗa masa da hakan ya ba shi damar tashi ya bi bayan Umar. Sai da na ɓata a ƙalla mintuna biyu kafin na goge fuskana na ta saka hijabina na fito falon kaina a ƙasa. Can ƙasan maƙoshina na yi sallama Anty Sawwama ta amsa mini yayin da nake ƙarisowa na zauna kusa da ƙafafunta. "Amatullah baƙi ne suka zo yi mana gaisuwar Hafsatu, shi ne suka buƙaci ganinki ke ma su yi miki gaisuwa". Sai a lokacin na ɗago kaina don ganin mutanen da ake magana akan su, take na ji zuffa ya keto mini ƙirjina ya buga da mungun ƙarfin bala'i. Saifullah da Muhammad Taukif idanuna suka sauƙa akan su suna zaune a cikin falon yayin da suma ɗin ni suke kallo. "Ku ne daman?". Na yi furucin ina nuna su da yatsana. Ban jira amsar kowa ba na ce"Anty me ye waɗannan mutanen suke yi a cikin gidan nan? Wallahi ba na son ganin wannan mutumin balle har mu zauna inuwa ɗaya da shi". Na ƙare zancen ina musu nuni da Saifullahi. "Daman kin san shi ne?". Amir ya jefa mini tambayar cike da mamaki. Kaina na gyaɗa kafin na ce"shi ne fa wanda na ba ku labarinsa, shi ne wanda na yi aiki a cikin gidan wansa". Daga nan na ƙara kwashe komai da ya taɓa haɗa mu na ƙara sanar da su a karo na biyu. Tun da na fara zancen Anty Sawwama take ta ƙara jinjina kanta. "Amatullah duk wani abin da ya taɓa faruwa a baya ki manta da shi ya wuce. Yadda ya tako

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});