Chapter 69
Chapter 69
ke jin ta tamkar ba ta kasance ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikina ba yayin da wani jiri yake kwasa ta da barazanar buga Ni da ƙasa haka muka ƙarisa cikin gidan da Anty Zulaihatu da ta fito daga banɗaki na fara tozali. Mamakin ganina ya sanya ta sakin butar da ke hannunta ya faɗi zuwa ƙasa, ta murtsuke idanunta don tabbatar da cewa ni ɗin ce dai ko kuma gizo nake yi mata, sai da ta tabbatar da cewa ni ce tsaye a gabanta kuma a zahiri ba mafarki kana ta kurm salati ta bi bayansa da hamdala tana faɗin"Umma Umma fito ki ga wallahi ga Amatullah ta dawo". Ta ƙare zancen tana isowa inda nake ta rungume ni, ni kam na kasa yin komai illa hawayen da suke ta zuba daga idanuna har izuwa lokacin da Umar da Anty Sawwama suka fito, mu na haɗa ido da ita ta ja ta tsaya a wajen guda kawai ta kafe ni da ido ba tare da ta ce da ni komai haka nan ba ta ƙariso inda nake ba. Na sa ƙarfi na ɓanɓare Anty Zulaihatu daga jikina na isa gaban Anty Sawwama na durƙusa akan gwiwoyina sai dai na gaza cewa komai na tsawon mintuna illa kukan da na ci gaba yin sa da dukkanin ƙarfin da Ubangiji ya azurta ni da shi. [12/19, 1:20 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________________ Page 7️⃣3️⃣ Na salwantar da wasu mintuna masu tsayin gaske ba tare da na iya cewa komai ba illa kukan da har izuwa lokacin bai yanke daga idanuna ba, haka nan babu wanda ya ba ni haƙuri balle kalman lallashina Anty Zulaihatu ma kukan da take yi yayin da har nake jin sautinta. Sai da na fizgo numfashina da yake maƙale mini a ƙahon ƙirjina kafin na sama lasisin fesar da zantukan da suke bisa kan harshena cikin raunin da kai tsaye yake fitowa daga can ƙasan zuciyata da ta yi nauyin gaske. "Anty don Allah ki yi haƙuri ki yafe mini. Na san da cewan na aika muku ba daidai ba ina roƙonku da ku yafe muni dukkan kurakuren da na aikata a gare ku, ko hakan zai haifar mini da salama a cikin ruhina har ya yi silar wanzar da kwanciyar hankali da nutsuwa a cikin ƙirjina". Shuru ta yi ba tare da ta ce komai na tsawon wasu mintuna har sai da na yanke tsammani na kuma cire rai daga cewar za ta amsa mini, kafin na ji ta soma magana cikin rawar murya da ya taimaka wajen fallasa sirrin da yake taskace a cikin tsokar zuciyarta, na tarin damuwar da take ciki. "Amatullah ba ki yi mana laifin komai ba. Kuma ba mu riƙe ki a cikin zuciyoyinmu ba". Ta ƙare zancen hawaye yana zuba daga idanunta, da hakan ya ƙara gigita ragowar nutsuwar da ya yi saura a gangar jikina. Na cira kai na kalle ta na ga dai lalle hawayen da take yi, ban san sa'ilin da na ja jikina na riƙo ƙafafunta na rungume tare da jingina kaina a jikinsu ba. "Don Allah Anty ki yi haƙuri ki sassauta mini wannan halin da nake ciki. Duba fa ki ga kuka ki ke yi sa boda baƙin ciki da takaicin da na yi silar cusa muku a cikin zuciyoyinku. Wallahi ba zan taɓa yafewa kaina ba akan halin da na yi dalilin faɗawarku cikinsa". Da ƙyar na ƙare zancen sa boda numfashi da yake ta sama da ƙasa yana maƙale mini a ƙirji, ta sa hannu ta ɗago ni tsaye daga durƙushewan da na yi yayin da take goge mini ruwan ƙwallan da ya gama damalmala mini fuskana. Sai dai ita ma ta kasa magana sai da ta runtse idanunta kafin ta iya faɗin"kamar yadda na sanar da ke tun farko duk cikin mun nan babu wanda ya ƙullace ki a cikin ransa. Kullum fata da burin da muke kwana mu tashi da shi a cikin zuƙatanmu shi ne Allah ya amintar da ke a duk inda kike a cikin faɗin duniyar nan, kuma Allah ya karkato da hankali da tunanin zuwa gida sai kuma ga shi Allah ma ji roƙan Bayinsa ya amsa mana addu'armu a lokacin da duk ba mu yi tsammani ba. Amatullah yadda nake jin su Alhassan a cikin raina kuma na jin babu wani abun da za su aikata a gare ni wanda idan suka tuba suka yi nadama Ba zan iya yafe musu ba, haka nan ke ma babu abin da za ki yi wanda ba zan iya yafe miki shi ba. Sa boda kamar ƴata nake jinki". Ta riƙo hannuna"ta ku mu je ciki". Daga haka ta ja hannuna muka shiga cikin falonta haka ta sa Anty Zulaihatu ta tafasa mini ruwan zafi ta kai mini banɗaki na je na yi wanka haka nan na iske suturuna a gyare tamkar an san da dawowa ta cikin gidan, ɗakin ko'ina tsaf da shi babu alamar datti balle ƙazanta. Kayan sawana kuwa har da waɗanda aka goge su sai tashin ƙamshi suke tamkar mun haɗa iri da ƴan maiduguri. Haka na durƙushe akan kayan na ci kukana tamkar raina zai fi ta tabbas na so na butulcewa rahama da ni'iman da Ubangijina ya lulluɓe rayuwata da ita kamar yadda Yaya Alhassan ya furta hakan a gare ni, na ja dogon numfashi na fesar yayin da nake ƙara shaƙan ƙamshin da ya buɗaɗe cikin ɗakin ina tuno tarin ƙarni sa ƙazantan da yake tattare a cikin ɗakin da na dawo, hatta banɗakin ɗaya muke amfani da shi duk yawan jama'ar da suke rayuwa a cikin gida, mata da kuma matan ƴan gida da kuma baƙi, kafin ka tsuguna ka sauƙe buƙatanta wajibi ne sai ka kora ruwa. Sai da na ci kukana kamar babu gobe kana na tashi na gabatar da sallan zuhur da kuma Asr nan inda na yi sallan na zauna na haɗa kaina da gwiwa yayin da na faɗa cikin cakwalkwalin tunanin da yake barazanar tarwatsa ƙalbina. Ji da na yi an dafa kafaɗuna shi ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa, na cira kaina ina bin Anty Zulaihatu da kallo har ta iso gabana ta zauna tana kallona tamkar mai son gano wani gaskiyar da na haƙa rami na burne. "Amatullah". "Na'am" Na amsa da shi cikin sanyin amo da hakan ya ba ta lasisin ci gaba da maganar da take. "Mun yi kukan rashinki irin wanda baki ba zai iya furtawa ba, mun yi baƙin cikin kasancewarki a kusa da mu mussamman idan muka tuna amanarki da Kawu ya ɗauka ya damƙawa Umma lokacin da rai yake ƙoƙarin sallama da gangar jikinsa. Babu inda ba mu neme ki ba Amatullah sai dai tunaninmu bai taɓa ayyana mana cewa za ki iya zuwa ki yi rayuwa a cikin karuwai ba har ma ki ɗabi'antu da irin rayuwar da suke yi". Kalamanta na ƙarshe suka zaunana zuciyata tare da baƙanta mini rai da ruhina take wani kuka mai matuƙar sauti ya tsinke mini. Na kifa kaina a kan cinyoyinta ina ta fama rera kukan jikina har wani rawa yake ye yi ga wani zafin da nake ji yana ratsa har cikin jijiya da ɓargona.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98