Chapter 10
Chapter 10
ma'ana da asali gami da tushe". "Ba zan ma fara wannan garajen ba Amatullah, na san ma Ummata ba za ta taɓa barin na yi hakan ba. Tun da ƙaddarata ta faɗo a haka babu yanda zan yi face na rumgume ta yadda ta zo min". Zan yi magana ta ɗaga mini hannu alamar ba ta son jin komai daga gare ni"Amatullah kar ki kawo min rikici da ruɗu a cikin rayuwata. Na yi kowa sanin wace ce Ummanta don ita ta haife ni hakan ba zai hana ta hukunta ni idan na bujire mata ba, ba abin wahala ba ne a wajen ta ta saka a haukata ni. Don haka maganin bari kar a fara Hausawa suka ce zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki". Ina ƙare zancen ta tashi ta fita da sauri ba tare da ta ba ni damar cewa komai ba. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina dafe jikin gini na tashi na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da sallan isha'i. Ina zaune a inda na yi sallan aka ɗago labulen ɗakin akan shigo. Wata matasjiyar budurwa ce ta tsuke cikin shirgar ƙananan kaya dogon wandon da aka tsatstsaga gwiwansa sai kuma wata rigar da babu hannu a jikinta, ta tula uban gashin doki a kanta da ya sauƙo har bayan wuyanta tana taunar chewgum da yake ba da sautin ɗas ɗas. "Ke ce Amatullah?". Na gyaɗa kaina"e ni ce". "To ki zo Hajiya Babba tana son ganawa da ke a cikin ɗakinta". "Na shiga uku! Allah ya sa ba wani laifin na yi ba". Na galla mini harara"wannan kuma idan kin je za ki ji ko ma me nene. Ni dai na isar da saƙo". Tana dire zancen ta juya ta fice ta bar ni cikin tarin zulumi da fargaban abin da zan je na tarar. Cikin mutuwar jiki na tashi na fito na nufi ɗakin Hajiya Babba na tsaya daga waje ina kwaɗa sallama sai da ta ba ni iznin shiga kana na shiga. Tana zaune akan kujera ta ɗaura ƙafarta ɗaya akan ɗaya na zauna a ƙasa tare da gaishe ta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa. "Hajiya sannu da hutawa, an ce wai ki na nema na". Na ajiye wayar da take latsa wa ta fuskanto ni da kyau tare da faɗin"kwananki nawa a cikin gidan nan?". Ƙirjina ya buga na shiga tsoron kar ta ce na haɗa nawa ya nawa na bar cikin gidan don na ga hakan ba wani abu ne mai wahala a wajenta ba. Kafin na ba ta amsa ta ci gaba da cewa"na lura har yanzu ba ki fara mu'amala da kowa ba balle har ki sama kuɗin da za ki dinga biyan kuɗin hayan ɗakinki. Sannan har zuwa wannan lokacin Aminu shi yake ɗaukan nauyin ci da shanki, shin dama ba ki shiryawa rayuwar bariki ba kika saka ƙafa kika fito daga gidanku? Ba ki tanadin guzurin irin rayuwar nan ba kika baro gaban iyayenki?". Jikina gabaɗaya ya yi laushi na kasa cewa da ita komai illa sadda kaina ƙasa da na yi da hakan ya ba wa hawayen da nake dako damar tsiyaya. Muryata can ƙasan maƙoshina na furta"Hajiya in sha Allah zan nema sana'ar da zan din ga ɗaukar ɗawainiyyar kaina da shi kwanan nan". "Wane irin sana'a kenan?". "Kowani irin aiki idan zan samu na cikin gida, ko wankau ne ko kuma rauno....". Tun kafin na rufe bakina ta katse mini numfashina"wankau dai da na sani?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta damar zarce wa da faɗin"mace kamar ki ta tsaya tana yin wankau ai wannan abin a duba lamarin ne, yadda kike da dirin nan ga kuma kyawun sura da ko mace ƴar uwarki ce ta gan ki sai ta ƙara bin ki da kallo balle kuma ɗa namiji. Me ye zai hana ki yi amfani da damar da Allah ya ba ki wajen cin duniyarki da tsinken sakace". "Ban gane abin da kike nufi ba?". Ta gyara zamanta kafin ta ce"ina nufin akwai maza masu kumbon susa masu hannu da maiƙo da suke neman mata ire-irenku ruwa a jallo. Ba don komai ba sai don biyan buƙatar kansu kuma ba sa ƙyashin kashewa mace ko nawa ne matuƙar za su sama abin da suke so a wajen ta, idan ma tsoronk ɗaukar ciki ne yanzu zamani ya zo da abubuwa da yawa, ana amfani da comdon domin hana ɗaukar ciki. Idan kin yi dace ma wasu mazan ba sai kun kwanta da su ba kawai da zaran sun sama nutsuwa da ke shikenan buƙatarsu ta biya. Sannan idan duk hakan bai yi miki ba kawai wata hanya mai sauƙin gaske, akwai matan manyan mutane a cikin ƙasar nan da kewaye da mazajen suka tara musu dukiyar da ko za su yi shekaru ɗari a duniya ba za su iya cinye shi ba, duk wani nau'in jin daɗi na duniya suna samunsa su ci abin da suke so su sha abin da ransu yake so, su sa suturar da duk suka ga dama sannan su hau duk kalar motar da suka yi ra'ayi, su je duk ƙasar da suka zaɓa, su kashe duk adadin kuɗin da suke so. Sai dai matsalarsu guda ɗaya ce jal ita ce ba sa samun lokaci da kulawa mazajen su. Wannan dalilin ya san da yawa da cikinsu suka soma neman maza a waje sai dai masu wayo a cikinsu ba maza suke bi ba, mata ƴan uwansu suke sawa a nemo musu su yi duk abin da za su yi da mijinsu na aure da ita. Su kan ɗauki dukkan nauyinta su yi mata komai da komai, su jiyar da ita daɗin da ba ta taɓa jin makamancin sa". Tun da ta soma zancen nake bin ta da ido har ta kai aya. Na numfasa kafin na ce"shin Hajiya aikata hakan yana daga cikin sharaɗin zama a cikin gidanki ne?". Ta watsa mini wani wulaƙantaccen kallo kafin ta amsa mini a taƙaice "A'a". "To in dai har hakan ba shi ne sharaɗin zama a cikin gidanki ba. Ina so ki ba ni dama na je na nema aikin da zan riƙe kaina da shi ba sai na bi wannan hanyar da duk kika zayyana ba". Ta yi banza da ni ba tare da ta ce da ni uffan ba haka na ci gaba da zama ba ta ce da ni ci kanki ba. Har sai da na gaji don kaina na ce"Hajiya zan iya tafiya?". Ta yi mini wani kallo ta wutsiyar idonta kafin ta ce"wai dama ba ki tafi ba? Za ki iya tafiya". "Na gode mu kwana lafiya". Na furta yayin da nake tashi na fice daga ɗakin, tun kafin na isa cikin ɗakina hawaye suke zuba daga idanuna har na isa, na rufa ƙofar na rufe tare da jingina a jikin ƙofar ina sulalewa a hankali har zuwa ƙasa. Na kifa kai da gwiwana ina saki wani irin gigitaccen kuka mai ratsa zuciya. Na raba dare ina kuka kamar raina zai fita kafin wani wahalallen bacci ya ɗauke ni ban tashi sai da gari ya fara yin gaske, na tashi a firgice saboda mafarkin da na yi da Abba. Wai ya zo cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98