Chapter 50
Chapter 50
mun yi aure duk wannan soyayyar neman ta za mu yi mu rasa, duk marmarin junan da muke yi za mu koma jin haushin juna. Kin ga zaman auren nan zaman takura ne da rashin samun cikakken ƴancin kai mussamman aure a yanki arewacin ƙasar nan da za su san darajar mace ba sun mayar da matayensu tamkar bayin da ba su da ƴancin kansu, komai sai an ba ki izini za ki yi shi". "To ai wannan abubuwan da kika lissafo ba ɗabi'ar ba ce, koyar wa addini ne cewar miji yana gaba da matarsa. Kuma ko fita za ki yi ƙofar gida sai da iznininsa". Taɓe bakinta ta yi tana gyara ƙarin gashin doki da yake kanta kana ta ce"yanzu dai me ye kike so ki ce da ni?". "Ku yi aure ya fi wannan rayuwar da kuke ciki. Ku ma kanki sai kun fi girmamawa da mutunta junanku". "Ni fa yanzu ba aure ba ne a gabana Amatullah, kuma ke ki na tunanin aure a cikin wannan lokacin abu ne mai sauƙin da kike ta faman faɗinsa haka? Duk wacce ta sako ƙafarta ta tako cikin gidan nan da zummar shigowa harkan bariki to kafe ta ake yi, su shanye ta ta yadda ko ta so fita daga harkar ba za ta iya ba, wannan dalilin ne ya sanya da yawa daga cikinmu ko mafarkin fitan ma ba sa ya yi balle su yi wani yunƙurin ganin hakan ya faru. Wasu ma da suka riƙa a cikin harkan har ƙungiya ne da su da zaran kin yi yunƙurin fita za su sanya miki wani cutar da za ki yi ta fama da shi har sai kin gwammace mutuwarki akan ci gaba da rayuwa. ko ma su haukata ki gabaɗaya wasu ma idan kika yi karo da masu rangwamen imani sai sun yin sanadin rayuwarki. Kin ga duk wacce ta yi gangancin barin cikn gidan iyayenta ta bijire musu ta zaɓi ta yi nisa da su har tsautsayi ya sanya ta sako ƙafafunta cikin harkar bariki sai dai a fitar da gawarta ba daidai ta sauya sheƙa ba". Kalamanta suka sanya ni faɗa cikin tunani mai zurfin haske sai na ɗau wasu mintuna kafin na magana a hankali. "Ki na nufin matan cikin gidan nan ma duk Hajiya Babba ta kafe su ke nan? Ko suna son barin wannan harkar ba za su i ya ba?". Maimakon ta amsa mini sai kawai ta fashe da dariya mai matuƙar sauti har tana shiɗewa ta kwanta akan katifar tana dariyar. Na tsaya kawai ina ta kallonta cikin al'ajabi da mamaki. "Ki gwada ƙoƙarin fita ki ga ni sai ki zo ki ba wasu labari". Ganin ta mayar da abin shiririta ya tursasa mini yi wa bakina linzami sai dai giyar mamaki da al'ajabin da zantukanta suka shayar da ni bai sake ni har yanzu wannan lokacin. Jiya ina jin hayaniyarku da Shaaqana ikon Allah. Kin yi min daidai don tun kallon farko da na yi wa yarintar na ji ba ta kwanta min a cikin rai ba, ita ba kyau ba, ita ba kyakykyawan sura balle giri haka nan babu murya mai daɗin sauraro uwa uba ga duhun fata tamkar bayan tukunya". "Ta kai ni maƙura ne amma ni ma hakan ba halina ba ne". "Ai babu abin da bariki ba ta saka mutum ya yi duk wani halin da bai kasance naka ba dalilin bariki da rayuwar jikinta, za ta sanya ki fara ɗabi'antuwa da shi ba tare da ita ma kanta ta sani ba. Kin ga bariki da kike gani kike raina wa awwbillahillazi babu abin da ba zai sa mutum ya yi ba, take za ki rikiɗe ki soma sauya launi tamkar hawainiyya". "To Allah ya kyauta". "Amin". Ta amsa da shi a taƙaice tana tashi ta zauna daga kwanciyar da dariyar da take yi ya tursasa mata yin sa. "Yanzu dai za ki raka ni kasuwar ne ko ƙaƙa?". Ta ɗan yi shuru kafin na yi tunanin abin da zan faɗa"sai dai mu yi wani abu ki ba ni gishiri na ba ki manda". Ta bi ni da ido"yi min yadda zan ga ne". "Zan raka har sai kin gama duk siyayyar da za ki yi ko da kuwa za mu kai dare a can. Amma ni ma fa za ki taimaka mini ta wani fannin don cimma wani daɗaɗɗan burin raina". "Wani buri ne wannan haka? Kuma ta wani hanya zan iya taimaka miki?". Na gyara zamana kafin na hau zazzago mata bayani ina zuba tamkar bishiyar magarya. "Akwai wani mutumin da nake son ko ta wani hali ne na gan shi ya ganni ko da kuwa na minti guda ne. Sai dai kasancewarsa babban mutum kuma mai kima da daraja a idanun mutane hakan yana neman ya gagare, idan har kika taimaka mini ki ka yi mini hanyar ganinsa kin gama yi mini komai a cikin rayuwar nan". Cike da zaƙuwa ta ce"wane mutum ne haka?". "Sunansa Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe, amma na ji a garin nan ana ce wa da shi ba baƙin balarabe". Tun kafin na gama zancen ta waro idanu waje tare da dafe ƙirji"anya kanki ɗaya kuwa kin san abin da kike faɗa? Duk da ban cika sauraron wa'azi da halattar inda ake faɗin Allah ya ce Annabi ya ce ba, tabbas wannan sunan ba ɓoyayye ba ne ga kunnuwan kowa da yake cikin garin na babba da yaro. In ban yi ƙarya ba a iya sani na shi ɗin babban Malamin addini ne da aka yi masa shaidar dukkanin halaye da ɗabi'u na ƙwarai. In kin haɗu da shi me ye za ki ce masa ke kuwa?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na soma kora mata bayani daki-daki ban ɓoye mata komai tun daga farkon haɗuwarmu na kwashe na sanar da ita. Ta yi shuru tamkar mai nazarin wani abun kafin can ta ce"to ke yanzu ta ina za ki fara neman sa? Sannan in kin yi dace kin gan san ma me ye za ki ce da shi har ki ja ra'ayinsa? Wallahi da gwamma garin nan kika yi wannan alwashin akan sa sai na ce da ke hakan zai ya fi miki sauƙi n akan wannan da kika yi". "In dai har na gan sa ɗin to haƙiƙa na yi mai wuyar". Ta yi shuru tare da zabga tagumi tana kallona kafin ta ce"tabbas ba ki da hankali". Ta yi zancen tana ƙoƙarin tashi ta fita na yi hanzarin cafko hannunta. "Ina cikin hnakalina sai dai ku da kuke yi mini kallon zautacciya ku ya kamata a bincike ƙwaƙwalwarku. Ke dai inda taimakon da za ki iya yi mini kawai ki yi mini inda babu taimakon da za ki yi mini kuma to ki bi ni da fatan alkhairi". Sai da ta ƙare mini kallon tsaf irin kallon da mai hnakali yake yi wa zautacce kafin ta ce"ban san me ye zan ce miki ba Amatullah". Ta koma ta zauna kafin ta ɗaura daga inda ta tsaya. "Taimako ɗaya zan yi miki shi ne na haɗa ki da wata mata da take ba ta sirrin mallaka da karkato da hankali mutum zuwa gare ka, shi ma kuma fa sai ku na garin ɗaya ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98