Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

san inda kike". A dunƙule ta jefa mini zancen ba tare da ta warware mini ƙulin ba ta yi shigewarta cikin ɗakinta, na kasa jan ƙafana na bar wajen har sai da kowa ya watse ya bar ni a waje, masu shiga ɗakunansu da samarinsu suka shige masu shirin fita suka fita. Sai da na ja dogon gashin na fesar kafin na nufi cikin ɗakina ina doso ɗakin na ji wani gungumemen wari ya doki hancina babu shiri na toshe hancina da tafukan hannayena. Ba n i da tocila balle na haska na ga abin da ya haddasa warin haka na ci gaba da tsayiwa a ƙofar ɗakin tun ina tsaye har na zauna, a nan ƙofar ɗakin na kwana. Sanyin asuba da ya soma ratsa ni shi ya farkar da ni daga nauyayyen baccin da ya sace ni. Na farka na shiga na ɗauko buta na yi alawa a ƙofar ɗakin na shimfiɗa ɗan kwalina na yi salla, sai da na ɗan jira gari ya yi haske kana na koma cikin ɗakin. Na tsaya cak tamkar gumki ganin yadda aka ɓata kan tabarman da amai ya yi kaca-kaca, ni na yi tamkar na ɗaura hannu a ka na dinga zunduma ihu ko zan ji sauƙin takaicin da ya cika mini zuciya. Ban san sa'ilin da hawaye suka fara gangarowa daga koramar idanuna ba sai jin ɗumin su na yi a bisa fatan fuskana. Ba ni da ajiyayyen ruwa ko kaɗan illa wanda na rage da na yi alwalar sallan asubahi. Na fito na ga La'aniyatu ba su buɗe ƙofa ba, na rasa yadda zan yi. Ina waigawa na ga wani bokati na ɗauka na fita domin ɗeba ruwa, layin sharau don har zuwa wannan lokacin gari bai gama waye wa sosai ba. Ina tafiya ina kuka har na isa wajen ɗeban ruwan na ɗeba na ɗaura akaina na juyo zan tafi kenan na hango shi yana fitowa daga cikin masallaci. Ban san dalili haka kawai na ji jikina ya ɗauki rawa ya kafe ni da ido kamar yadda ni ma na ɗaura idanuna akan sa, bai ce da ni komai ba ya zo ya wuce ni ma na ɗauki hanyar komawa gidan. Tun daga zaure na ji ana kwararo ruwan ashariya, har na shigo cikin gidan ba a fasa ba ina shigowa aka nuno ni. "Kin ga shegiyar da ta ɗaukar min bokati". Zuby ta yi zancen tana nufo inda na ke tsaye gadan-gadan, kafin na na yi aune ta tankaɓar da ruwan da yake kaina ya malale a jikina ya yi mini lijif. "Yanzu ke don kuturun wulaƙanci ki rasa bokatin wacce za ki ɗauka a cikin gida nan sai bokatina?. To wallahil azim zan ja miki layi da kayana a cikin gidan nan". Tana dire zancen ta wafce bokitin ta yi shigewarta cikin ɗakin. Na dubi jikina da ya yi lajab na tuna irin dogon tafiyar da na yi kafin na je na ɗebo ruwan kawai sai na ji hawaye suna sauƙa daga idona, na koma ƙafan ɗakina na zauna na zabga uban tagumi. A haka La'aniyatu ta fito ta iske ni ta nema jin ba'asin abin da yake faruwa na irge mata komai cikin kuka, ita ta taimaka mini da ruwa da wanke ƙazantar da Habu ya yi mini akan tabarmata, na fito da ita na shanya akam igiya na koma ciki na sha lemo da biskit daga cikin abin da Hajiya Muhibbat da ta ba ni. Sai da na jira tabarman ta bushe kayan jikina ma ya bushe na shigo da ita ciki na shinfiɗa, duk da ban da agogon da zan duba lokaci na fahimci lokaci ya ja don hasken rana ya game ko'ina, sai da a rufe ɗakin na ba da ajiyan ɗan makulin a La'aniyatu kafin na tafi. Kamar ƙafafuna za su tsinke haka na ke ta zabga sauri har ƙafafuna suna sarƙewa, ina isa ƙofan gidan na ƙwanƙwasa mai gadin ya fito ya buɗe mini na durƙusa har ƙasa na gaishe shi kafin na shiga cikin gida. Na yi sallama Altine ta fito ta watsa mini wani matsiyacin kallo, na rusuna na gaishe ta maimakon ta amsa sai ta jefo mini tambaya. "Ke sai yanzu kika yi niyyan zuwa aikin? Wannan in ke za a tsaya jira sai kin zo ki girka ai kuwa watarana ba za a ci abinci a gidan ba". A nutse na ce"ki yi haƙuri wani uzuri ne ya sani na makara. Amma in sha Allah ba zan sake maimaita irin hakan ba". Ta gallo mini harara"Dalla can rufe min baki sai wani fiƙi-fiƙi kike yi da idanu kamar ta Allah. Sai ki jira don karin kumallo suke yi". Daga haka ta juya ta bar ni tsaye a wajen, haka na ci gaba da tsayiwa har sai da na gaji na zauna a bisa dakalin wajen. A ƙalla na fi mintuna talatin a zaune a wajen kafin Altine ta fito ta cikin izgili ta ce na shigo. Da rawan jiki na tashi na bi bayanta muka shiga, suna zaune a falo tare da tagwayenta da ba su wuce shekaru biyu da haihuwa ba a hashashena kenan, na durƙusa har ƙasa na gaishe ta ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa. Kafin ta ce wani abu na soma da ban haƙuri"Hajiya ki yi haƙuri na makara wani uzuri ne ya riƙe ni, amma in Sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba". Fuskanta ɗauke da maɗaukakin murmushi ta ce"kar ki damu ba komai, ai jiki da jini dole daman wataran a sama irin haka, yanzu mu je sai na zagaya da ke ki ga gidan ko?". Na gyaɗa mata kaina ina jin wani daɗi yana mamaye mini raina na fahimtan da ta yi mini, har na yi gaba zan ji ta a baya muka jiyo sautin da ya tilasta mata tsayawa. "Anty wace ce wannan?". Ta waigo tana kallonsa yayin da su Aryan suka nufa wajensa. "Ita ce sabuwar ƴar aikin da na yi maka bayani akan ta jiya". Yana ɗaura agogo a damtsen hannunsa ya ce"Anty a sallame ta, a nema wata kawai". Babu shiri na ɗago kai ina kallonsa ƙirjina yana tsananta bugu, jikina ya yi sanyi kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 4️⃣8️⃣ Cike da maɗaukakin mamaki a bisa fuskan Anty Muhibbat ta ce"Saif me yasa wani abun ka ga ta yi?". Har yanzu idanunsa yana kan agogon da yake ɗaurawa a tsintsiyan hannunsa ya furta"Anty kawai yarinyar ba ta yi min ba ne, ki dubi yanayinta da kuma ƙarancin shekarunta ba na tunanin da za iya yin duk aiyukan da kika lissafa min jiya. Zai fi dace a sallame ta a nema wata kasai". Dukkanmu biyun muka yi sakeke muna kallonsa ni kam na gaza cewa komai saboda sanyin da jikina ya yi ƙalau tamkar jinjirar kazar da ruwa ya yi mata ɗan banzan duka. "Saif ba wannan za ka duba ba, na lura tana cikin tsananin buƙatan wannan aikin ko don ta kula da rayuwarta a matsayinta na ƴa mace. Mata nawa ne masu irin shekarunta suke yawon ta zubar? Mata nawa ne masu irin shekarunta suke sayar da jikinsu don su sama abin da za su ɗauki

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});