Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 89

Chapter 89

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,212 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fuskar Anty Sawwama da take zaune kusa da ni. Na murtsike idanuna yayin da nake ƙoƙarin tashi na zauna ina faɗin"har gari ya waye?". "Wani irin gari ya waye kin san yanzu ƙarfe nawa kuwa? To yanzu kusa ƙarfe sha ɗaya ake nema na rana duba fa ki ga yadda rana ta take haskenta ya mamaye ko'ina". Zumbur na yi na tashi tsaye ina leƙa taga na ga hasken rana ya dalle tar. "Innalillahi har rana ta fito haka Anty? Da kin tashe ni na yi aikin cikin gidan ai". Taƙaitaccen murmushi ta yi kafin ta ce"kwantar da hankali ai na gama duk wasu aikace-aikacen da ya kamata, hatta girki na yi ke dai abin da nake so da ke ki tashi ki je ki wanka ki zo ki ci abincinki ga shi can a cikin kicin". Daɗin zantukanta da yadda suka faranta mini ruhina ya sanya ni sakar mata da murmushi ina zuwa na rumgume ta ina ta jeranta mata godiya wani na bin wani. Albarka ta din ga sanya mini tamkar za ta yi aron baki. Haka na fito na yi wanka na shirya sannan na ɗauko abincin na tisa kwanon gabana kafin na saka hannuna wayata ta soma ruri, na ɗauko wayar ƙiran Saif ya shigo cikin wayar ban ɗaga ba har sai da ya katse ya ƙara ƙira a karo na biyu kafin na ɗaga, cikin sanyin murya na yi sallama ya amsa mini cike da kulawa. "Har kin tashi ke nan?". "E". "To ina miki fata da addu'ar Allah ya sanya wannan ranar ta zama rana mafi daraja da alkhairi a gare ki". Cike da jin daɗin addu'ar tasan na amsa da faɗin"amin ya Allah tare da kai gabaɗaya". "Jiya kin yi min wani furuci wanda nake son ki tabbatar min da shi a yanzu ido yana ganin ido, don na sai na gama sakankancewa akan hakan ashe kuma gigin bacci ne yake ɗeban ki san da kika yi zancen". "Wani zance ke nan?". "Alƙawarin amincewa da aure na da kika yi mana". Sai da na ja dogon numfashi na fesar da shi daga bakina kafin na sama zarafin cewa"a cikin hayyacina na yi wannan zancen kuma ba a iya fatan bakina ya sanya ya ratsa har cikin zuciyata". Ina iya jiyo sautin ajiyan zuciyan da ya sauƙe kana ya ce"ni kuma in sha Allah zan yi iya ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai". Shuru ya biyo bayan zancensa na ƙarshe kafin can ya kuma cewa"to bari na bar ki ki huta, in sha Allah a yau ba sai gobe ba zan yi duk yadda zan yi na ga sautin muryan nan ya shiga hannun Sultan. Na san duk yadda zan yi memory card ɗin nan ya je hare sa duk da yanzu ba ma tare da shi a gari guda". "Fatan nasara". Na furta masa a taƙaice da hakan muka yi sallama da shi na ajiye wayar tare da jingina bayana jikin bango na ɗan lumshe idanuna ina sauraron yadda zuciyata take buga wa a hankali hankali. Yayin da wasu tunani kala daban-daban suke ziyartar cikin kwanyata tabbas izuwa yanzu na ji zuciyata ta nutsu da Saif ban san ko hakan ake ƙira da soyayya ba don ban taɓa tsintar kaina cikin irin makamancin wannan yanayin ba. Haka na gama cin abincin cikin rashin daɗin yanayi na fito na wanke kwanun, na leƙa ɗakin su Yaya Alhassan na ga ba ya nan Umar ne kawai a ciki yana karantu wani littafin turanci. Ya ɗago kai ya na kallona kafin ya ce"ke kuma me ye kin wani tsare ni da idanuna kamar za ki cinye ni? Mai sunan tsofaffi kawai". Murmusawa na yi kafin na furta"za ka ji da shi dai, ai sai an kula kare sannan yake haushi". Dariya ya ƙyalƙyale da shi tare da faɗin"yanzu ni ne karen ke nan? Ai wallahi in da ni kare ne da tunin na daɗe da cinye namanki har na taune ƙasussuwanki yarinya". Dariya na aka mai sauti ina jijjiga kaina na juya na fice daga cikin ɗakin na koma ɗakina, karatun Alkur'ani na ɗan yi kafin na fito na haɗa girkin rana. Haka na wuni cikin tsammanin ganin ƙiran Saif ya sanar da ni yadda ake ciki amma shuru tamkar an shuka dusa har na kwanta ƙiransa bai shigo cikin wayata. Ni kuma ina kunyar ƙiransa haka na daure safiya ta yi ko ƙaran shigowar saƙon kamfanin layin MTN na ji ya shigo cikin wayata sai na yi zumbur na tashi na duba ko zan ci karo da saƙon Saif amma wayam, haka na ƙarar da wunin wannan ranar komai cikin sanyin jiki nake aiwatar da shi tamkar majinyaciya. Har dare ta yi bai ƙira ni ba muna tsaka da cin abinci na ji wayata ta yi ruri na kusa bazama da sauti na je na ɗauko ta da yake ajiye a saman firijin da yake cikin falon Ina duba wa na ga baƙuwar lamba ce take na ji raina ya ɓaci don ba wannan nake tsammani ba, ban yi ƙasa a gwiwa ba na katse ƙiran tare da ajiye wayar na dawo na zauna ina zama wani ƙiran ya ƙara shigowa a karo na biyu na yi biris da shi tamkar ban ji ba. "Wai ba wayanki ake ƙira ba ne Amatullah?". Yaya Alhassan ya jefa mini tambaya cikin kakkauran murya. "Baƙuwar lamba ce ban san wanda yake ƙira ba". "Ɗauko min wayar na gani". Ya furta cikin ba da umarni, hakan ya tilasta mini tashi na je na ɗauko wayar na miƙa masa daidai sa'ilin da wani ƙiran yake ƙara shigowa a karo na barkatai. Ya ɗaga tare da sanya ta a amsa-kuwwa aka yi sallama ya amsa. "Mansur ne mijin Amira". Aka furta daga ɗayan ɓangaren sai a lokacin da na ji muryarsa na tuna cewar lokacin da na je gidansu ta amshi lambana a fefa da nufin idan Mansur ya dawo za ta ƙira ni da wayarsa. Miƙo mini wayar da Yaya Alhassan ya yi bayan sun gama gaisa wa da Mansur shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa. Na amsa wayar muka gaisa da shi kafin ya miƙa wa Amira ita muka gaisa. "Ya na ji muryarki haka ba ki da lafiya ne ko kuma dai akwai wani abun da yake damunki?". Sai da na saci kallon Anty Sawwama kafin na mai da wa Amira amsar tambayar da ta yi mini. "Lafiya ƙalau me kika ji da ya sa ki faɗin haka?". "Haba! Amatullah ki na nufin ban san halinki ba ne ko kuma mene ne?". Da hanzari na taka mata burki ganin ta na ƙoƙarin wuce mini zani a cikin tsakiyar kasuwa. "Mu na cin abincin bari inna gama zan ƙara ƙira". Ina gama maganan na katse ƙiran tare da ajiye wayan, na ci gaba da cin abincin sai dai duk a tsarge nake. Har muka gama cin abincin ban ɗago kaina ba muna gama wa na tattare kwanukan na je na wanke su kaina a ƙasa na zo na wuce zuwa ɗaki sai da na yi shirin kwanciya sannan na danna wa Amira ƙira, bugun farko ta ɗaga. "Wai Amatullah ki na lafiya ƙalau kuwa? Na ji a jikina akwai matsala ga

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});