Chapter 53
Chapter 53
shi yasa na zo har nan na same ka" Na ɗan yi jim kafin ya furta"gaskiya ba na tunanin ciki kwanakin Sheikh zai zo cikin garin nan wataƙila sai dai cikin azumi. Kin ga azumi kuma yanzu akwai aƙalla watannin huɗu zuwa biyar, amma in dai wani abun ya zo da zai shigo da shi cikin garin nan zan sanar da ke. Don kin san duk zuwan da yake yi garin nan ba ya yarda ya sauƙa a ko ina face cikin otel ɗin nan. Duk da kuwa yana da alfarma a wajen manyan mutane ciki har da mai Martaba da kuma shi kansa gwamna". Muka haɗa ido da Zinariya cike da tashin ƙwarin gwiwa, na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina sadda kaina ƙasa yayin da nake ci gaba da sauraron zancen da ya ɗaura da faɗin su. "Amma me yasa kuke son ganinsa a nan? Idan wani abun ne ai za ku iya zuwa can gidansa ko?". "Ba za ka gane ba ne Oga da dai za mu sama ganin sa a nan ɗin, sai abubuwan sun fi zuwa mana da sauƙi". "To shikenan in da ya zo zan yi ƙoƙarin sanar da ke. Mu je gefe mu yi magana ko?". Ya ƙarishe zancen yana kashe mata ido guda tare da rangwafo kansa daidai saitin fuskarta. Sai da suka miƙe tsaye kafin ta kallo ni ta ce"Amatullah bari mu yi magana da shi ki ɗan jira mu nan". Kaina kawai na gyaɗa mata don na kasa motsa bakina da nake jin ya yi mini nauyi ainun. Suka tafi suka bar ni a wajen ina ta saƙa da warwara a cikin raina. Kaina yana ƙasa na ji hayaniyar wajen ya ɗan ƙaru ina ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan fuskar Saif da ya tsaya cak yana kallona, muka tsaya muna kallon kallo ƙirjina ya ci gaba da bugawa tamkar zai bayyano waje. Mun ɗauki wasu mintuna mu na kallon juna kafin wani mutum ya iso inda yake. "Ranka ya daɗe baƙin sun iso haka nan ɗakin taron kowa ya zo, kai kaɗai ake jira". Kansa kawai ya jinjina masa ya yi gaba suka hau wani benin yayin da mutum ya bi shi a baya. Tashi na yi na rasa inda zan je da abin da ya dace na yi don gabaɗaya na rasa nutsuwata. Take jikina ya soma rawa zuffa ya soma jiƙa mini jikin kamar wacce aka juye wa bokatin ruwa. Ina ƙoƙarin fita na hango Zinariya ta nufo inda nake. "Amatullah na tarar da ke a tsaye?". "Ke dai kawai ki zo mu tafi. Don Allah mu bar nan wajen". Mamakin ganin yadda na rikice ya ƙi ba ta damar cewa komai, na ja hannunta muka fita daga wajen mu na fita muka sama abin hawa muka hau. A hanya take sanar da shi cewar ita fa daga nan ba gida ta nufo ba, don haka na ce wa mai napep ɗin ya sauƙe ni a hanya kusa da gidan Hajiya Muhibbat na ƙarisa da ƙafata sa boda ba nisa. Na tarar da Hajiya ba ta nan haka nan ma su Aryan ba sa nan wanda ina da tabbacin tare suka fita da Hajiyar, na shiga ɗakin Altine na gaishe ta amma ba ta amsa mini ba dole na fito don na san zaman cikin ɗakin ba zai haifar mini da ɗa mai ido ba. Na nufi kicin na tarar da wanke-wanke jimgim har da na daren jiya da ya haɗe da na safiya na wanke su tsaf, na share kicin ɗin. Na fito na share falon kafin na ɗauko bokati da mopper na soma mopping cikin sanyi jiki tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, ban ankara ba na ji hawaye suna gudun famfalaƙi a bisa kuncina, na kai hannuna na share su ina ci gaba da aikin. Na kusa gama wa na ji an buɗe ƙofar falon an shigo kallon ɗaya na yi masa na ɗauke kaina sa boda yadda ya murtuƙe fuskarsa babu alamar annuri a tattare da shi, ya ƙariso cikin falon ya zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya. Sai da na tattaro jarumta na yafa wa kaina kafin na ce"sannu da dawowa ranka ya daɗe". Kamar yadda na yi zato bai amsa mini ba hakan ya ba ni damar ɗaukar bokatin zan fita ya dakatar da ni ta hanyar faɗin"wace ce ke? Da wani irin mungun nufin kika kutso kai cikin gidan nan?". Cak na tsaya jikina yana rawa tamkar ana jona mini mazari. [12/12, 5:53 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________ Page 6️⃣7️⃣ Ina jin takun takalminsa yana ƙara nufo inda nake tsaya da duk kusancin da yake ƙara wa da ni ina jin ƙirjina yana tsananta bugu tamkar zai fito waje. Na runtse idanuna a ƙoƙarin daidata nutsuwar da ya yi nisa da gangar jikina, jikina ya ci gaba da rawa tamkar wacce aka jona wa wutar lantarki, duk da idanuna suna a rufe amma ƙamshin sanyayyan turaren da ya bulbula a jikinsa shi ya ba ni tabbacin ya iso inda nake. "Wace ce, me yasa kika ɓoye ainihin wace ce ga Anty, me yasa kike da fuska biyu? Ki na nuna wa kamar ke ɗin mace ce mai nutsuwa da hankali bayan zahirinki ba hakan kike ba, karuwa ce ke wacce take rayuwa a cikin gidan karuwa da masu zaman kansu. Tun ranar da Anty ta kawo ki cikin gidan nan na sa a yi min bincike akan ki kuma an kawo min cikakken labarin rayuwarki, me yasa kika ɓoye wa matar da ta yarda da ke gaskiyar wace ce ke? Me yasa kika ɓoye wa matar da ta aikata miki a lokaci da kike tsananin buƙatar taimako ainihin kalarki? Ta yarda ta ke wannan dalili shi ya ba ta ƙwarin gwiwar kawo ki cikin gidanta, ka sakar miki tagarman kula da cikin gidanta da kuma ƴaƴanta. A wasu lokutan har su na shafe tsawon awanni tare da ke wanda ba sa yin rabin sa tare da ita sa boda yanayin aikinta da yake tursasa mata fita a cikin ko wani irin yanayi". Ya ɗan tsagaita kafin ya ɗaura daga inda ya tsaya. "Me yasa kika shigo cikin rayuwarmu? Waye ya aiko ki kuma nawa suka ba ki? Aikin tsawon wani lokaci za ki yi musu?". Ban san sa'ilin da hawaye suka fara wanke mini fuska ba, na buɗe lumshashshun idanuna da suka rikiɗe suka sauya launi zuwa launin ja, suka yi jajir da su har wani zafi da zogi suke yi mini. Ba tare da na sani ba bokatin da yake hannuna ya faɗi ƙasa ruwan da yake cikin ya malale a waje. A karo na farko da na yi jarumta jefa ƙwayoyin idanuna cikin nasa sai dai na kasa magana sa boda rawan jiki da kuma nauyin da bakina ya yi mini, su suka haɗu suka yi mini taron dangi na gaza aiwatar da komai. Ya cije leɓɓansa kafin ya furta"ba za ki iya cewa komai ba to ma ina karuwa take da kalaman kare kanta ko kuma ta wanke kanta? Amma tabbas ki tanadi kalaman da za ki wanke kanki da shi a gaban Allah don ba ki da wani hujjan zuwa bariki face son zuciyarki da kike biye wa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98