Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 96

Chapter 96

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta zauna tana fuskantana. "Amatullah". "Na'am". Na amsa ina sadda kaina ƙasa. "Ko dai zan yi wa Umma magana ne a dakata da yin wannan auren nan? Don na ga kamar duk kin shiga damuwa, na lura kuma kaman kawai kara da alkunya kika yi ki ka amsa ba wai don ki na son Yaya Alhassan ba". "Ba buƙatan hakan Anty ki sanar da ita komai. Ai shi zaman aure ba a yi masa kara, kawaici ko kuma alkunya da ba na son sa ko kuma ban yarda da jagorancin da zai yi mini a cikin gidan aure ba, tabbas da zan san hanyar da zan bi wajen na fahimtar da Umma hakan. Sai dai ina ji har cikin zuciyata cewa zan sama dukkanin gata da kulawan da ya dace a cikin gidan Yaya Alhassan, roƙona ɗaya a gare ki shi ne ki bi mu da addu'a kawai". "Haƙiƙa Amatullah kin cika ƴar halak, in sha Allah wannan auren zai zamu silar wanzuwar farin ciki a cikin rayuwarki". Ban iya amsa mata ba illa kwantar da kaina da na ji akan cinyarta tare da lumshe idanuna daidai lokacin da wayarta ta yi ƙara ta ɗaga ƙira, a amsa-kuwwa take don ina jin sa'ilin da Yaya Mu'azzam yake shaida mata aure ya ɗauru nan ta din ha hamdala tana gode wa Ubangiji. Washe gari da safe tun kafin gari ya yi haske Anty Sawwama ta ƙira ɗakinta sadakina Naira dubu ɗari da hamsin ta damƙa mini, na nuna mata cewar babu abin da zan yi da shi ita ya kamata ta riƙe a yi wasu buƙatun da shi, amma ta nuna mini rashin yiyuwan hakan ta ce da ni a addinance ma ni nake da iko da sadakina, don haka na riƙe na je na yi tunanin abin da zan yi da shi. Tun ranar nake wasan ɓoya tsakanina da Yaya Alhassan duk abin da yake yi inna shi shigowarsa bari nake yi na shige cikin ɗakin ba na fito wa har sai ya tafi, cikin sati ɗayan da ya rage Yaya Alhassan ya ƙarisa aikin gidan da yake ginawa da yake can gangare daman fenti ne kawai ya rage sai ruwa da za a ja, kiwonta da yake ƙauye Anty Sawwama ta ɗaga ta sayar aka yi mini kayan ɗakin da na kitchen yayin da Yaya Mu'azzam ma ya raka rawar gani matuƙa. Duk halin matsin rayuwar da Amira suke ciki hakan bai hana Mansur dunƙulo Naira dubu hamsin ya ba ni ba a matsayin gudumawansa da farko na ƙi karɓa har sai da Amira ta nuna mini ɓacin ranta kafin na amsa. A bakin Anty Zulaihatu nake jin cewa wai Saifullah da Muhammad Taufik sun zo sun taya Yaya Alhassan murna har ma da kawo gudumawa a Anty Sawwama da ta kasance uwar amarya kuma uwar ango. Ranar da za a kai ni tare muka wuni da Anty Zulaihatu da kuma Amira ranar mun sha kuka sosai har sai idanuna suka kumbura har ya kai jallin da ba na iya buɗe su. Gidan a cike yake da mutane maƙota, ƴan uwa da kuma abokan azurki. Dangin mahaifin su Yaya Alhassan ba su nuna mini tsana ko ƙyama ba sai ma ja na a jiki da suke yi da yi wa iyayen addu'ar samun rahamar Ubangiji. Ban gaskata cewar da gaske an ɗaura mini aure ba sai da aka fito ni aka saka ni a cikin mota domin kai ni ɗakin miji, tun da motar ta soma tafiya ƙirjina yake dakan lugudai taka birkin da aka yi ya yi daidai da lokacin da hawaye suka zubo daga idanuna sai dai mayafin aka rufe mini fuskana da shi ya hana mutane fahimtar kuka nake yi, haka aka fito da ni daga cikin motar aka shigar da ni cikin gidan. Bayan wata dattijuwar mata ta yi mini umarnin na shiga da ƙafar dama tare da addu'ar Allah ya sa na shiga ke nan sai dai a fito da gawa ba. Anty Zulaihatu ne ta kai ni har cikin ɗakin miji ta kuma jira har aka yi rakiyar ango ta damƙa amanata a hannun Yaya Alhassan tare da yi nasihar idan ya cutar da ni ko ya wulaƙata ni, to ba ni ya wulaƙanta ba kansa ya tozarta. Haka suka tafi suka bar ni ni ɗaya ƙwal don na kai ga roƙon Amira ta kwana murzawa idanunta toka ta yi, da na matsa mata sai ce wa da ni ta yi to ita kuma na ta mijin ta yi ya ya da shi? Haka ina ji ina gani duk aka watsa aka bar ni ni ɗaya tamkar mayya. Ina zaune a cikin ɗakin ina kuka na ji an buɗe ƙofa an shigo ƙamshin turaren da na ji ya bugi hancina shi ya tabbatar mini da wanzuwar Yaya Alhassan kusa da inda nake, kafin na ji ya kai hannu ya yaye mayafin da yake kaina ya sanya hannunsa ya tallafo haɓana yana kallon fuskana da ta kumbura ta yi tsimtim tamkar kwaɓin fanken da ya ji yis. "Kukan nan ya isa haka Amatullah. Ki tausayawa kanki haka mana tun yaushe kike wannan kukan. Ya kamata kin san cewa kuka fa ba ya magani". Shuru na yi ban amsa masa ba don ina da yaƙinin ko na buɗe bakina sautina ba zai fita ba. "Amatullah". Na ɗaga kai na kalle shi da hakan ya ba shi tabbacin cewa ina sauraronsa. "Aurena da ke ya ƙara tabbatar min da cewar duk abin da kasance rabonka ne to fa ba ya taɓa wuce ka, na kuma ƙara tabbatar da sahihancin wannan karin maganan ta Malam Bahaushe da yake cewa zakaran da Allah ya nufa da cara to fa ko ana muzurai ana shaho sai ya yi. Allah ya ƙaddara cewa ke ce matar da zan aura a duniya ga shi kuma hakan a tabbata a lokacin da dukkanmu ba mu yi tsammani ba balle zato. Ina so ki cire komai a cikin ranki ki manta da duk wasu abubuwan da suka faru a baya domin yanzu sabon shafi ne ya buɗe a cikin rayuwarki. Na yi miki alƙawarin zame miki mijin marainiya wanda zai share miki hawayenki a duk sa'ilin da zuba kwanrayo. Zan kasance mai yi miki hidima har zuwa ƙarshen rayuwata, zan hidimta miki da karfina, lokacin da kuma aljihuna. Na yi ɗamarar sauya rayuwarki daga duhu zuwa bayyanannen hasken da zai haskaka miki hanya". Take na ji kalamansa sun samar mini da nutsuwa a sashin ruhina, na ɗau lokacin kafin na yi magana cikin dushashewan amo. "Ina fatan na kasace mace ta gari kuma saliha a gare ka kamar yadda Annabinmu ya ƙira mace ta gari da mafi ƙololuwan jin daɗin duniya ga raywuar ko wani ɗa na miji, ina addu'ar Allah ya ba ni ikon yi maka biyayya akan komai matuƙar komai ɗin bai hauce wa hanyar Allah da koyarwan manzonsa ba". Cike da jin daɗin kalamaina yake amsa wa da Amin, ya dafa kaina ya yi mini addu'a kamar yanda yake a addinance kana muka je muka yi alwala muka gabatar da salla raka'a biyu mu ka yi godiya ga Allah da ya nuna mana wannan ranar a cikin rayuwarmu, sannan muka roƙe shi albarkar da yake cikin auren da kuma zuri'a

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});