Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 62

Chapter 62

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da ƙosawa da sauraron zancenta na ce"ba komai na ce miki in akwai a zan gaya miki". Daga haka na kwanta na juya mata baya na lumshe idanuna kamar mai bacci, sai dai musayar wuƙaƙe da mashin wutan da ake yi a cikin farfajiyar ƙirjina ba zai taɓa sauƙar mini da nutsuwar da zan iya runtsawa ko da na sankan guda ba ne. Ban ankara ba na ji wasu hawaye masu ɗumi su na sauƙar akan fatan fuskana. Abubuwan da suka wakana suka soma dawo mini cikin kwanyata. Ko da na tashi na yi sallan asr ban ba wa Zinariya fuskar da za ta ƙara yi mini wani tambaya, sai da na yi har sallan isha'i kafin muka haramar tafiya otel muka shirya duk abin da mu buƙata muka rufe ɗakin muka tafi. Muna sauƙa a bakin otel ɗin ƙiran Oga Deeno yana shigowa cikin wayar Zinariya ta ɗaga ta sanar da shi ga mu mun iso ya fito ya yi mana jagoranci har zuwa cikin wani garden muka zazzauna, ya soma yi mana jawabi. "Yanzu haka shi da tawagarsa su fita zuwa gidan mai martaba amma ina da tabbacin zuwa karfe tara ko goma za su dawo, don haka zan san yadda zan yi na buɗe miki ɗaki ki shiga cikin kafin ya dawo, daga nan kuma ke kike san abin da za ki yi, san a kashe CCTV cameras ɗin dukka sashin. Ni da Zinariya kuma mu ma za mu keɓe". Cike da gamsu na ce"ba damuwa". Ya ɗan sausata amon muryarsa"don Allah duk abin da za ku yi kar ki cutar da shi, kar ki yi silar da za ki ɓata min aikina ki wargaza min burin da na daɗe ina ginawa". "In sha Allah babu abin da zai faru". Ya jinjina kansa alamar shi ma haka yake fata. Muka tashi muka shiga wajen rukunin ɗakunan otel ɗin, shuru wajen yake don an sallame mi kowa babu wanda za a ƙara ba wa ɗaki a cikin VIP site ɗin har sai shi da tawagarsa sun tafi. Ya buɗe mini ɗaki yayin da Zinariya ta miƙo mini jakan jakan da yake hannunta wanda har da babban waya a ciki da ta sayo shi sabo dal da ta fita ciro kuɗi. Muka rumgume juna da ita tare da yi mini fatan alkhairi. Na ƙarewa ɗakin tsallon tsaf tabbas ya tsaru iya tsaruwa, don babu wani abun buƙatan bisa mutum zai nema a cikinsa ya rasa. Na fito da kayan zan sauya daga cikin jakan, na ajiye shi a ƙasan gadon na shiga cikin banɗaki kamar yadda muka tsara. Wanka na yi ƙirjina ya na buga wa duk kyawu da tsaftan banɗakin amma hakan bai hana ni ƙanƙaninsa ba, haka na yi wankan na gama na saka wani doguwar riga da ya kama jikina tam sai dai ya sauƙa mini har ƙasa na ɗaura ɗan mayafinsa a kaina. A ƙalla na yi mintin talatin a cikin banɗakin kafin na ji alama an buɗe ƙofar ɗakin an shigo, na yi maza na soma aiwatar da shirinmu na jawo towel ɗin da na gani lanƙaye a cikin banɗakin na ɗaura a kaina ina yi kamar ina tsane sumar kaina, na buɗe ƙofar na fito daidai lokacin da ya waigo muka haɗa ido ni da shi. Tabbas shi ɗin ne tsaye a gaba ba gizo ba kuma ba a cikin mafarki ba, duk da har yanzu zuciyata ta na buga amma na dake na ci gaba takuwa cikin ɗakin yayin da duk ɗaga ƙafar da zan yi na sauƙe sai ya bi ni da kallo. Gaban madubi na je na zauna ina kallonsa ta cikin madubin da har yake tsaye inda yake bai ko motsa ba, na sakar masa da wani laulausan murmushi mai kashe zuciyata kana na juyo ina yi masa wani shu'umin kallo. Ya nuna ni da ƴatsansa zai yi magana na yi caraf na mashe zancen cikin faɗin"Amatullah". "E na gane ki, amma me ye kike yi a nan? Ta ya ya kika shigo cikin ɗakin nan? Sannan mafi muhimmanci ma ya ya aka yi kika san da cewa ina cikin otel ɗin nan har kika gano ɗakin da nake?". Na ƙara yin wani murmushin a karo na biyu kafin na ce"ban yi zaton waɗannan tambayoyin ne za su fito daga bakinka ba". Ya katse ni"wani tambayoyi ke nan kike so ji?". Ya ɗan ja numfashi sannan na furta"na za ta tambayata za ka yi shin dama har izuwa wannan lokacin ban mance da kai ba". "Ina cikin da aka ce ki na ɗauke da shi?". Ba tare da tunanin komai ba na ce"na zubar don zai hana ni rawan gaban hatsi ya kuma kawo mini cikas wajen cin duniyata da tsinke". Ya yi shuru kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce"me yasa kika bar gida? Sannan da kika bar gidan ina kika koma da zama?". Na kashe masa ido ɗaya kafin na ce"bariki na shigo ta yadda zan sama cikakken ƴancin kai". Muryarsa babu alamar wasa ya ce"tashi ki fita daga cikin ɗakin nan". Na tashi daga inda nake zaune na iso gabansa na riƙe ƙugu ina faɗin"ai na ga waje babu inda zan fita". Bai ce da ni komai ya wuce ya shiga banɗaki da alama wanke fuskarsa ya yi ya fito ya ɗan yi turus da ya ganni har yanzu ina cikin ɗakin. Ya nufi wajen wayar talhon da yake kan teburin ɗakin yana faɗin"bari na ƙira otel ɗin na ji uban waye ya buɗe miki ɗakin nan har kika sama damar shigowa". Na yi hanzarin miƙe na riƙe wayar"kar ka yi hakan don kamar ka ɗauki wuƙa ne ka daɓawa cikinka". Ina rufe bakina aka soma buga ƙofar ɗakin a hankali kuma a nutse, muka haɗa ido da shi"ana buga maka ƙofa ka je ka buɗe ko kuma ni na je na buɗe". Ya yi banza da ni da hakan ya ba ni damar juya wa da nufin zuwa na buɗe ƙofar ya yi hanzarin shan gabana. "Me ye haka za ki yi?". "Buɗe ƙofar mana zan yi". Na ba shi amsa cikin halin ko ina kula. "Koma zan je na buɗe". Ya yi maganar a gajarce yana nufar ƙofar ya buɗe abinci aka kawo ya ƙarba ya shigo da shi ya ajiye akan teburi, muka tsaya mu na kallon kallo ga juna. Ganin ba shi da niyyar jin komai ya sa ni zaunawa na soma bubbuɗe abincin, ya fi minti goma ya na kallona kafin ya koma cikin banɗakin. Hakan ya ba ni damar tashi na yi wuf na je na ɗauko jakar da na ajiye na ɗauko wannan ƙwayar da wannan wayar na ɓoye ta a jikina, na zo na jefa ƙwayar maganin a cikin ƙaramin flask ɗin ruwan shayin da aka haɗo tare da abinci na jijjiga kana na ajiye, na ja plate ɗaya na ajiye gabana na soma ci, a haka ya fito daga banɗakin ya same wannan karon da alama wanka ya yi don ya fito yana tsane fuskar da wani ƙaramin towel. Ya zauna a kujerar da take saitina da na ɗago kai muka haɗa ido sai na sake masa murmushi na ci gaba da cin abincina. Sai da ya gaji da kansa ya ce"me ya kawo

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});