Chapter 95
Chapter 95
ke nan, mussamman ni da Yaya Alhassan da muka yi mutuwar zaune tsabar yadda maganar ta daki zuƙatanmu. "Umma daman su na son junansu ne?". Amir ya yi tambayar cikin tsananin buƙatar amsar. "Amincewar su kawai nake nema, matuƙar suka amince to komai zai zo da sauƙi. Amatullah zo nan kusa da ni". Cikin rawar jiki na ja jiki na je gabanta na gurbana ta riƙo hannayena ta riƙe tare da umartana akan na ɗaga idona na kalle ta sai dai duk yadda na so ƙarfafa kaina na cira kaina lamarin ya gagare ni. "Ina so ba ki dama ki faɗi abin da yake cikin ranki don ki na da wannan ƴancin. Shin kin amince da auren Alhassan?". Take na ji zuciyar da take dashe a cikin farfajiyar ƙirjina ya harba sai da na ɗau sakanni kafin na furta"Anty ba na fatan zuwan ranar da za ki buƙata wani abu a wajena na kasa yi miki matuƙar ina da ikon yin sa. Ko wani mutum daban kika zaɓo mini a matsayin miji tabbas zan aure shi komai munin hali da ɗabi'unsa don na yi imanin ba za ki taɓa zaɓa mini abin da zai cutar da ni ba, balle kuma Yaya Alhassan da ni ma kai na shaida ce akan kyawawan halayensa. Na amince da aurensa har cikin raina matuƙar yin hakan zai faranta miki". "Na gode sosai Uwata Allah ya yi miki albarka yadda kika faranta min in sha Allah ba za ki taɓa yin ƙunci a rayuwa, Allah ya ji ƙan iyayenki ya kyautata makwancinki". "Amin". Duk muka haɗe baki waje amsa addu'ar da Anty Sawwama ta yi kafin ta juya ga Yaya Alhassan. "Alhassan ka amince da wannan zaɓin?". Sai da ya furzar iska daga bakinsa kafin ya ce"Umma ba zan iya bijire wa duk wani abun da kika zaɓa min, don na ba za ki ba ni abin da zai cutar da ni ba. Na amince zan auri Amatullah na kuma riƙe ta bisa amana, adalci da kuma tausayawa. Ni daman na ri ga da na san genotype ɗinsa tun da daɗe wa AA ne don haka ba wani matsala in sha Allah". "Alhamdulillah! Allah na gode da ka azurta ni da ƴaƴan masu ladabi da biyayya. Allah Ubangiji ya yi muku albarka ya albarkacin rayuwarku ya kare gabanku da bayanku ya ƙara haɗa kawunanku waje guda". "Amin". Muka dinga amsa wa da shi, haka Anty Sawwama ta din ga zubo mana addu'o'i kala-kala, daga bisani ma kawai fashe wa ta yi da kuka muka din ga lallashinta tare da ba ta haƙuri. Ƙiran sallan isha'i shi ya tursasawa su Yaya Alhassan fita bayan sun tsara yadda ɗaurin auren zai kasance, Yaya Mu'azzam ne waliyina a ɓangaren Yaya Alhassan kuwa wani ƙanin mahaifinsu Anty Sawwama ta riƙa ta sanar da shi komai, ya yi farin ciki matuƙa tare da balbale mu da ruwan addu'o'i. Ya kuma taso domin yi wa Yaya Alhassan waliyanci bayan ya yi alƙawarin biyan sadaki. Tun da na yi sallan isha'i na zauna nan kan sallayan na zabga wani uban tagumi, rurin da wayata take yi shi ya ja hankalina zuwa gare ta na ɗauko na kafe ta da idanuna sakamakon ganin lambar Saif ya fito cikin wayar, ban ɗauka ba har ƙiran ya katse ban ɗauko, don ban yi tsammanin ganin ƙiran sa a wannan lokacin ba, ya ƙara ƙira a karo na biyu kana na ɗauka cikin sanyin murya na yi sallama ya amsa kana na gaishe shi. "Ya na ji muryannki wani irin ko dai ba ki da lafiya ne?". "Lafiya ƙalau". Ya ɗan yi shuru kafin ya ci gaba"na ƙira ne daman mu yi wani magana idan ba kya yin wani aikin". Sai da na kawar da hawayen da suka kwaranyo mini kafin na ce"babu abin da nake yi, yi magananka ina sauraronka". "Ban san yadda zuciyarki za ta ɗauki maganar ba Amatullah, ba na so kuma ki yi tunanin ko ban yarda da ƙaddaran da ta tsara tsakaninmu ba ne. Ina so ki yi wa lamarin duba na tsanaki wallahi tsananin son ganin rayuwarki ta inganta kuma ta ci gaba ne ya sanya ni aikata wannan abun". Na katse shi"tafi kai tsaye ka yi magananka Yaya Saif". "So nake yi ki ba wa Sultan dama ya nema aurenki. Tun da lamarin ya afku nake ta tunani da zulumi ina tsoron ki faɗa hannun wanda bai dace ba, ina tsoron ki je inda za a yi miki gori akan rayuwarki ta baya, ina tsoron ki je inda ba a san mutuncinki ba balle a mutunta ki, ina tsoron ki je inda za a wulaƙanta ki ko a tozarta ki shi yasa nake ganin kamar Sultan shi ya dace da ya aure ki idan har kin amince. Sa boda shi na san dukkan halayensa na san shi ɗin mutumin kirki kuma duk wasu kyawun hali ya fi ni". Na buɗe bakina zan yi masa bayani kawai wani kuka ya kwace mini don yadda na so na hana sautinsa bayyana, sai da lamarin ya gagare ni wai ƙoƙarin cire wando ta kai. "Subhanallahi! Kuka kuma Amatullah? Me ya faru?". Ya watsa mini tambayar cikin kiɗima sai da na yi da gaske wajen daidaita fitar numfashina da yake maƙale mini a ƙirji kafin ina yi furzo da zancen wajen"Saif yanzu haka taron ɗauri aurena ake yi a masallacin ƙofan gidanmu". "Aurenki kuma? To auren ki da waye?". "Aure na da Yaya Alhassan wataƙila ma yanzu haka har aikin gama ya gama an ɗaura". Na yi zancen wasu hawayen suna gudun famfalaƙi a bisa kuncina. Ya ɗauki tsawon wasu mintuna kafin ya yi magana"alhamdulillah! Na ji daɗi da ya kasace cewar Alhassan ne ya aure ki ba wani ba, don ina da yaƙinin ba za ki tozarta ba a hannunsa. Duk inda ake neman mutumin kirki mai ƙoƙarin sauƙe haƙƙin ƴan uwantaka tabbas Alhassan ya kai, ina yi muku fatan dawwamanmen zaman lafiya da kuma samun zuri'a ɗayyaba". Ban iya amsa addu'ar ba illa furta sunansa da na yi cikin wani irin sanyin murya. "Saif". "Na'am Amatullah". "Ban san ina sonka ba sai da wannan lamarin ya faru, kai ne mutum na farko da ya taɓa nuna mini soyayya babu dangin uwa balle na uba, tabbas littafin tarihin rayuwata ba zai taɓa cika ba ba tare da an rubuta sunanka a cikin shafin farko ba. Na gode da dukkanin abubuwan da ka yi mini a cikin rayuwa, Allah ya saka maka kuma ya yi maka tagomashi da samun mace ta gari wacce za ta ƙaunace ka domin Allah". "Amin ya Allah, wannan shi ne ƙirana na ƙarshe da za ki gani ya shigo cikin wayanki. Don daga yanzu shari'a ta ja layi tsakanina da ke, in sha Allah zan zo na taya Alhassan murnar samun mace ta gari, ina yi muku fatan samu zaman lafiya. Allah ya haɗa fuskokinm da alkhairi". Ya na gama maganar kit! Ya datse ƙiran ya bar ni da ɓarin hawaye ji da na yi an dafa kafaɗana shi ya sanya ji waiga cikin sauri, idanuna suka sauƙa akan fuskan Anty Zulaihatu wanda da dukkan alamu ta daɗe a cikin ɗakin kuma ta saurari duk maganganun da ta yi. Da kallo na bi ta har ta iso gabana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98