Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tsuguna akan gwiwansa tare da ware hannayensa suka faɗo kan ƙirjinsa. "Uncle Saif tun ɗazu Inna Altine ta dawo da mu, ba mu gan ka ba". Ya shafa kan yaron da ya yi magana tare da cewa"Aryan na tafi wajen aiki shi yasa, amma ai na je can gidan Hajiya Maman ai na gan ku kafin na tafi". Ɗayan yaron ya yi caraf ya amshe zancen"ai Hajiya Mama ma ta yi ta masifa bayan tafiyanka, Anty Talatu ma cewa ta yi wai....". Kafin ya dirar zancen ya rufe masa bakinsa"Ayan ba na hana ka yawan sutura ba? Kai duk abin da ya faru zai ka kaso ka faɗa. Shi yasa Aryan ya fi ka hankali". Take Ayan ɗin ya cuno baki gaba gami da buga ƙafa yana kai wa Aryan ɗin da yake yi masa gwalo duka ya zame. "Wallahi bai fi ni hankali ba, ai Mummy ma ta ce ni ne babanta Aryan kuma ba babanta ba ne tun da shi sai kukan banza". Tana ƙare zancen ya bi Aryan ɗin da gudu suka shige cikin gidan, na bi su da kallo don ba ƙaramin burge ni yaran suka yi ba, kamansu guda, yanayinsu, girman jikinsu hatta muryar su kala ɗaya ne. Sai dai abin da na lura da shi ɗaya ya fi ɗaya suturu. Figigi na dawo cikin hankalina saboda fizge wayarsa da ya yi daga hannuna bai ce da ni komai ba, ya bi bayan yaran yana ƙira sunan Ayan, na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na ja ƙafafuna da suka sanƙare na bar wajen, kafin na isa gida har an fito daga masallacin sallan magrib ina zuwa na karɓa makuli na buɗe ƙofan ɗakin na shiga na ɗauko buta na zo na yi alwala na koma ciki. Sallan magrib na yi na haɗa har da na isha'i na zauna a wajen ban motsa ba na zuba uban tagumi, so nake yi na yi karatun alƙur'ani amma na waigo ko ina ban ga alamar alƙur'ani ba. Na runtse idanuna wasu siraran hawaye suna gangarowa daga gefe da gefen idona, a bayyane na furta"Allah ya jiƙan ka Abba, Allah ya yi maka rahama ya kai haske cikin kabarinka". "Amin". Na ji an amsa da shi da hakan ya tursasa mini buɗe lumshashshun idanuna, na kafe La'aniyatu da su har ta iso inda nake ta zauna a gaba na. "Kin dawo kenan?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta lasisin ci gaba da maganan"kin ce za ki ba ni labarin aikin da kika samu idan kika dawo". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na kwashe komai na juye mata tas, sai da na dire zancen ta ce"Allah ya saka mata da alkhairi, amma gaskiya ta kyauta kuma ta na da kirki. Amma har dubu ashirin kuɗin da yawa gaskiya". Na jinjina kaina"ni ma haka na gani, kuma a hakan ma ta ce za ta ƙara mini wani abu idan ta ga yanayin kamun ludayina". Ta riƙo dukkan hannayena"Allah ya sa a fara a sa'a". "Amin na gode sosai". Na furta ina ƙoƙarin samar da annuri a bisa fuskana, haka muka ɗan taɓa hira da ita kafin muka yi sallama tare da yi wa juna sai da safe. Tsabar farin ciki kasa bacci na yi na kwanta kawai ina ta juye-juyen ji nake yi kamar gari ba za ta waye ba balle har na fara fita wajen aikin. Ina daga kwance na ji an bankaɗo labulen ƙofar ɗakin an faɗo cikin ɗakin, duk da a cikin dubu ne amma ina gani gizon mutum yana nufo inda nake. A kiɗime na rarumo ɗan kwalina da ya zame daga kaina na mayar kaina. "Waye ne wannan? Waye ne?". Na yi maganar harshena har yana harɗewa, ba a amsa mini ba aka ci gaba da nufo inda nake zaune, babu shiri na tashi na miƙe tsam akan ƙafafuwana da suke rawa, babu wadataccen hasken da zai ba ni kallon fuskarsa balle na iya bambamce wane ne, har lokacin ba a amsa mini ba haka nan ba daina nufo inda nake ba, ya kawo hannu da niyyar kawo mini cakfa na yi hanzarin zamewa ya faɗi akan tabarman ruf da ciki. Yana wani irin numfarfashi kamar ragon layan da aka zarcewa wuya za a yanka shi. A guje na bazamo waje ina kurma ihu, take waɗanda suka rage a cikin gidan ba su fita ba duk suka fiffito suka dallo ni da tocila. "Ke dalla banza mene ne kika fito ki ma hurmawa mutane ihu?". Ɗaya daga cikin ƴan matan da suke tsaye a wajen ta furta a zafafe kamar za ta kai mini duka. Hajiya Babba ta fito tana gyara ɗaurin zanin jikinta da yake ƙoƙarin zame wa. "Wa ye yake son ya tada min da hankali da daren nan?". "Hajiya wa ye kuwa ban da wannan kucakar yarinyar mai zubin ƴaƴan aljanu, duk ta fi ta fitsine mutane a cikin gidan nan". Hajiya Babba ta nuna wacce ta yi zancen da ƴatsarta"ke Zuby ba na son ɗiban albarka, daman har masu zubin ƴaƴan aljanu ne a cikin gidan nawan ban sa ni ba?". "Hajiya ga ta nan ai sai ki tambaye ta abin da yake faruwa ta yi miki bayani". Zuby ta ƙarƙare zancen tana yi mata nuni da inda nake tsaye har zuwa lokacin ban dawo daidai daga kiɗimar da na yi ba. "Ke wace ce kike da suna?". "Amatullah". "To Amatullah lafiya kike zake ƙarfinki ki na kurma mana wannan ihun, gobara ce ta tashi ko kuma ƴan fashi ne suka yi mana da'iri ban sani ba?". Na girgiza mata kaina alamar a'a. "To mene ne?". Ta yi zancen cikin tsare gida da turmuƙe fuska babu alamar wasa ko wargi a tattare da ita. "Wani ne ya faɗo mini ɗakina yanzu ma haka ya na ciki, ban san wane ne ba?". "Wani kuma?". Ta jefa mini tambayar cikin mamakin ba ta jira amsar da zan ba ta ba ta juya ta shiga cikin ɗakin yayin da ragowar matan suka rufa mata baya, babu jima wa suka fito tare da mutumin da yake ta layi duk ya ɓata jikinsa da alama a matuƙar burge yake na fitar hankali. Cikin maye ya ce"sorry sister mance ɗakin cikas ɗin tawa na yi na faɗa na ki". Ban ce da shi uffan ba har ya gama galantolinsa ya gama. Zuby da tun farkon lamarin take tsaye a ƙofar ɗakinta ba ta gusa ba, ta dafe ƙirji tare da fiffito da idanu waje"na shige su ni Zubaida ɗiyar Sani mai kayan koli, wannan ai Habu ne saurayin Hafsy ƴar jama'are me ye ya kai shi cikin ɗakinki?". Idanuna ya yi tsilli-tsilli kafin na furta"wallahil azim ban san shi ba, ko fuskanshi ma ban gani ba saboda babu haske a cikin ɗakin". Ta galla mini hararar da ya tursasa mini yi wa bakina limzami babu shiri. Hajiya Babba ta ce"yanzu ina ita Hafsyn take wannan abun ya faru?". Zuby ta kada baki ta ce"Hajiya ta tafi club da wani sabon kamun da ta yi". Cikin zafin rai Hajiya ta ce"to kama shi ki san yadda za ki yi da shi, na kashe wannan case ɗin kowacce shegiya ta koma ɗakinta". Tana kama zancen ta juya gare ni"ke kuma ina so ki nutsu ki

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});