Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nauyin kansu? Mata nawa ne masu irin shekarunta da suke iskanci don su sama abin da za su saka a baki salati? Mata nawa ne masu irin shekarunta suke faɗa harkan banza da na shaye-shaye?. Ga su nan wasu sun rasa hankalinsu, sun rasa tarbiyya da kamun kansu, sun rasa kyawun jikinsu wasu ma sun faɗa harkan barace-barace akan titi wasun su ma sun haukace. Duk waɗannan hanyoyin ba ta zaɓa ta bi ɗaya daga cikinsu ba ta zaɓa ta fito ta nema aiki don ta rufawa kanka asiri ta kuma ci halaliyarta. Saif irin waɗannan yaran su ya dace a ringa taimakawa". Tun da ta fara maganar ya yi shuru yana kallon ƙasa bai ɗago kansa ba har ta gama maganar ta kai aya, kafin ya furzar da dogon numfashi a taƙaice ya furta"shikenan Anty amma dole zan yi bincike akan ta, idan na same ta da wani aibu tabbas dole a sauya ta a nemo wata". "To ubana yadda ka ce haka za a yi". Sadda kai ƙasa ya yi yana ɗan sosa ƙeyarsa ya ce"Anty ni fa ba haka nake nufi ba, zan tafi wajen aiki sai na dawo don Allah a kula da yaran nan". Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce da shi komai ba ya juya ya fice sai da ya fita kafin ta ce da ni"sai kin yi haƙuri da Saifullah haka yake, miskili ne na buga wa a jarida. Yana da wuyar sha'ani ga wanda bai san halinsa ba amma da zaran kun saba da shi za ki fahimci yana da daɗin zama da sauƙin kai uwa uba yana da tausayi da son taimakawa na ƙasa da shi". Kaina kawai na iya jinjina mata don bakina ya yi mini nauyin da na kasa cewa komai, ta yi gaba ina biye da ita muka zagaya ko'ina a cikin gidan nan, kicin ɗinta tsaf-tsaf da shi ga wani uban faɗi da girma. Girmansa ya kai a haɗa falo da ɗakinmu da muka yi rayuwa a cikinsa kafin Abba ya rasu. "Hajiya ban iya amfani da irin wannan abubuwan na zamani ba". Na yi zancen ina ƙara ƙare wa girman kicin ɗin kallo. Ta dafo kafaɗana tare da faɗin"a hankali zan koya miki komai idan na sama lokaci, kafin nan za ki na yi shara da mopping ɗin ko'ina a cikin gidan nan, amma ban da harabar gidan iya ɗakuna da falo ne sai wanke banɗakuna". "Na gode sosai". "Ki godewa Allah, ni yanzu zan fita wajen sana'ata amma ba zan daɗe ba zan dawo. Don haka za ki zauna da tare da Altine da su Aryan kafin na dawo". Kaina na jinjina mata kana na ce"a dawo lafiya Allah ya tsare ya ba da abin da aka fita nema". Cike da jin daɗin addu'ata ta amsa da faɗin"Amin ya Allah". Muka dawo falo ta shaida wa Altine za ta fita ta yi mata addu'ar a dawo lafiya, ta kwashe Aryan da Ayan suka yi mata rakiya har waje kana suka dawo. Ina zaune a cikin falon Altine ta dawo daga rakiyar da suka yi mata muka kalla juna ta banko mini harara kamar idanunta za su faɗo ƙasa, ba ta zauna a inda nake ba sai ta ja gefe ta zauna suna wasa da su Aryan, haka na ci gaba da zama shuru babu wanda zan yi magana da shi balle taɗi. Muna zaune a wajen har aka yi ƙiran sallan zuhur Altine ta tashi da yaran suka hau sama babu jimawa sosai suka sauƙa. Za ta wuce su fita na dakatar da ita ta hanyar faɗin. "Anty ina zan sama ruwa na yi alwala na yi salla kar lokaci ya ƙure?". Ta watsa mini wani kallon uku saura kwata kan ta mayar mini da martani a zafafe"tun ɗazu da na tashi na je na yi sallan ba ki yi min magana ba sai yanzu? Ai na yi tunanin ba za ki yi sallar ba ne". Na rusunar da kaina ƙasa ina ci gaba da sauran abin da take faɗa daki-daki. "Sai ki fita ta ƙofan can za ki ga fanfo ki yi alwalan ki dawo ki yi sallan a nan". "Sallaya fa?". "Ki yi akan ɗan kwalinki don ban yarda da tsarki da tsaftan jikinki ba". Tana gama faɗin haka ta ja hannun yaran suka fita, ƙofar da ta nuna mini na bi na yi alwalan na dawo na shimfiɗa ɗan kwalina na yi sallan akai. Ina raka'ar ƙarshe suka dawo suka zube akan kujera, na iddar da sallan na shafa addu'ar da na yi kana na juya ina duban ta"Anty akwai aikin za da a yi ne?". "Ban sani ba wannan kuma sai dai ki jira matar gidan ta dawo, sai ta yi miki wannan bayanin da bakinta". Tun da ta yaɓa mini wannan maganar ban ƙara cewa da ita komai ba, Ayan ya soma jan hannunta yana cewa"Anty ki tashi mu je ki yi mana alwala mu yi salla, Uncle Saif ya ce idan an ƙira salla mu na yi kar Allah ya ƙona mu a wuta". Hankaɗe shi ta yi ya faɗi bakinsa ya saki hannun kujera. "Wai ku kam wasu irin jarababbun ƴaƴa ne haka? Babu dama ku ga mutum ya zauna yana huta wa sai kun addabe shi da jaraba, ku dai ku na gaba da ku ganni ina zaune ina hutawa. An gaya muku ni ɗin jakar uwarku ce ko ta ubanku ko kuma ni inji ce da ba na buƙatar hutu? Ubanku na can wata uwa duniya na kuma ta tsallake ku ta tafi neman duniya ni da ban haifa ba an bar ni da jalala". Ta yi zancen tana miƙewa ta bar cikin falon, ganin yadda bakin Ayan yake zubar da jini ya tilasta mini tashi na je na ɗago sa, don tun da ya faɗi ya kasa tashi daga wajen. Ƙofar da na bi na je na yi alwala nan na nufo na wanke masa bakinsa sannan na cire masa rigarsa don ita ma ta ɓaci da jini muka dawo cikin falon, na zaunar da shi akan kujera kusa da ɗan uwansa na je na ɗauko mopper na gyara wajen. Na zo na zauna a kusa da ni ina duban Ayan da yake ta sauƙe ajiyan zuciya akai akai. Na riƙo hannunsa kana na ce"a ina ake ajiye muku kayanku?". "A ɗakinmu yake". "Ina ne ɗakin nakun?". Da hannunsa ya yi mini da wata ƙofa ya ce"wancan ne". Na tashi na shiga komai guda bibbiyu ne a cikin ɗakin kala ne kawai ya bambanta su. Na buɗe sit na ɗauko masa wata riga na juya zan fita na hango Altine tsaye a ƙofar ɗakin ta naɗe hannayenta a ƙirjinta tana yi mini wani irin kallon da na gaza cewa ma'anarsa. "Me ye kike yi a nan?". "Riga na zo ɗaukawa Ayan". "Saboda ke kike kula da su ko?". Da saurina na ce"A'a Anty na jikin nasan ne ya ɓaci da jini shi ne na cire masa na zo ɗauka masa wani." Ina rufe bakina ta ƙariso cikin ɗakin ta wafce rigar daga hannuna. "To ba zai sa wata rigar ba, haka zai wuni ba riga tun da an sa masa ya ɓata. Ai ni ba jakar gidansu ba ne da kullum ba

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});