Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,212 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yin maganan na ji zuffa ya jiƙa jikina sharaf ƙirjina ya soma dakan lugudan-lugudan tara-tara sau tara, daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin akuya ai kuwa tunin na soma sakin hawaye. "Don Allah Hajiya ki taimake ni ki taimaki rayuwata ki yi mini rai, kar ki ce na bar cikin gidan nan. Don wallahi ban san inda zan cusa kaina ba inda na bar nan ki tausaya mini.......".Tun kafin na dire zancen ta dakatar da ni. "Dakata ki ji ni yarinya nan gidan ba tausayi ko kuma jin ƙai nake yi ba, gidan na zo kin zo ne ki baje hajarki ki kwashe ƴan sulallanki. Ki yi hidimar kanki har ma ki yi kyauta ki yi sadaka, idan tausayi kike buƙata sai ki bari sai ranar juma'a ki tafi ƙofar babban masallaci na gidan mai martaba wataƙila ki yi dace ki sama masu taimaka miki bila adadin. Amma a cikin gidan nan dai kam jikinki ne da ƙoƙarinki zai ƙwace ki har ya yi miki riga da wando har da singileti". Ta juya tana kallon Aminu"daman ba ka sanar da ita dokoki da ƙa'idodin cikin gidan nan ba ne?". "Aradu na sanar da ita komai in detail in ji ƴan boko. Ita ɗin ce akwai ta da daurin kai yadda kika san jinjirin haihuwar jaki, babu irin bayanin da ban yi mata ba amma kanta ya ƙi ɗauka ta dage akan ba za ta aikata zina ba. Na sanar da ita cewar akwai hanyoyi da yawa da za ta sama ƴan kuɗaɗenta ba ma tare da sun yi ido huɗu da na mijin ba amma ta ƙi amincewa". Da alama bayyanin da Amimu ya yi mata ya taimaka wajen rura wutar takaicin halina da yake ci a cikin ranta. "Zan ba ki zaɓi biyu wanda a ciki dole ki zaɓa ɗaya kafin nan zuwa ƙarfe goma sha biyun daren yau. Ko dai ki bi hanyar da ko wacce yarinya take bi ko kuma ki haɗa komatsanki ki setawa kanki hanya". Gabaɗaya na ji jikina ya yi sany tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, na kasa cewa komai na tsawon wasu daƙiƙu kafin na yi ƙarfin halin faɗin"Hajiya kafin wa'adin lokacin da kika ɗauka mini in sha Allah zan zo miki da abin da na yanke cikin zaɓin da kika ba ni". "Da kuwa kin yi wa kanki adalci yarinya. Yadda kike da suran nan ai za ki ci abinci sosai a harkan nan". "Amatullah ki nutsu ki yanke shawarar da za ta fishshe ki kar ki yi wa kanki baƙin ciki. Ki na da sura da dirin da ko wani ɗa na miji in ya ganki sai kin tafi da hankalinsa. Ke ɗin matar manya ce kalar shiga gaban mota irin matan da suke ba za taro su tashi kan kowa". Galla masa harara na yi sa boda haushi da takaicin da kalamansa suka cusa mini na miƙe da nufin barin cikin ɗakin na ji ya furta"tabbas Allah ya yi halitta a nan wajen. Irin wannan zubin kamar kika zama surarki". Ban tanka masa ba na fice daga ɗakin na faɗa cikin ɗakinmu na zube akan tabarman kwanciyata, duk yadda zuciyata take suya da raɗaɗi idanuna sun daina zubar da hawaye sai sa'ilin na yarda wani tashin hankali ya fi ƙarfin a yi masa kuka sai da kukan zuciya wanda ya fi ciwo gami da raɗaɗi. Na yi shuru ina sauraran bugawan zuciyata da yake ɓat ɓat. Na koma sauƙe numfarfashi mai ɗumi ina lumshe idanun yayin da zantukan Hajiya Babba da na Aminu suka dawowa mini cikin kaina tiryan-tiryan. Tabbas rayuwa za ta yi mini matuƙar wahala har ma sai na gwammace wataƙila gwara mutuwa akan rayuwa, sai dai duk rintsin da na yi wa kaina alƙawarin cewar ba zan ƙara aikata wani aikin zunubi da zai sanya Ubangiji ya yi fushi da ni ina cikin sani da hankalina ba. Sai dai in ban bi hanyar da suke so ba ina zan sama kuɗin da zan nema wa kaina matsuguni?.Na cire leɓena ina ci gaba da tunanin zucin da nake yi yayin da na sama salamar zubda da hawaye a daidai lokacin. "To fa! Ikon Allah wai na kwance ya faɗi. Ke kuma kukan me ye kike yi? Ai tun da kika sako ƙafarki kika shigo duniyar bariki duk daga lokacin za ki sabar wa zuciyarki dakiya, juriya da kuma shan duk irin yanayin da kika tsinci kanki. In ki ka ce kuka za ki dinga yi ina mai tabbatar miki da cewar sai an wayi gari watarana kin rasa hawayen da za ki tsiyayar, ni na fita sai kuma Allah ya yi dawowata zan je na kafa na tsare a bakin manyan ma'aikatu har sai na samu nawa rabon". Na ɗaga kai ina bin ta da kallo ta shirya tsaf cikin shirgar ƙananan kayan da suka kama jikinta tamau kamar fatanta. Da wani uban gashin kantin da ta watsa wa kanta ta sha kwalliya kamar mai shirin zuwa gasar tantance sarauniyar kyau. "Ki yi rayuwarki na tawa babu ruwan biri da gada. Zaman kanki kike yi haka ni ma shi nake yi". Na mayar mata da zancen muryata a dake. "To Allah ya kyauta". "Amin". Na amsa da shi a taƙaice da hakan ya ba ta lasisin fita ta tafi gararambana. Haka na ci gaba da zama a haka har na tashi na yi fita na yi alwala na dawo cikin ɗakin na yi sallan magrib, ban tashi daga inda na yi sallan ba har sai da na yi sallan isha'i. Na bi kayan jikina da kallo tun da na zo garin jafari ban sauya wasu kayan ba, balle hijabi da takalmin da wannan mai gadin ya taimaka mini da su. Jikina ya soma rawa ina jin wani zafi yana ratsa wa har cikin naman jikina. "Allah na tuba ka yafe mini sannan ka kawo mini ɗauki da mafita akan halin da nake ciki". Na furta a bayyane yayin da nake miƙe wa tsaye na fita daga cikin ɗakin na nufi ɗakin Hajiya Babba tana zaune a falon tana irga wasu tulin kuɗaɗen da suke gabanta, na durƙusa na yi mata sannu ta amsa mini ba tare da ta kalle ni ba. "Hajiya daman na zo na sanar da ke hukuncin da na yanke akan zaɓin da kika ba ni ne". "Ina jinki". Sai da na sauƙe wai gauron ajiyar zuciya kafin na furta"na amince zan bi hanyar da kuke so". [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________________ Page 5️⃣5️⃣ Tun da na so zancen ta kafe ni da ido har na kai aya, cike da mamaki ta furta"abin da kike faɗa ɗin nan ya kai har cikin zuciyarki kuwa? Sa idonki a cikin nawa ni ɗin nan da kike ji da gani cikakkiyar ƴar bariki ce mai lasisi babu inda ƙafafuna ɗin nan ba su taka ba a cikin duniyar bariki. Duk wani salon munafukarci, luggu da nurƙufanci na san shi tare da alamominsa. Nan cikin gidan nan kwanakin baya wata yarinya ta zo simi-simi da ita kamar ba za a sanya mata hannu a baki ta ciza ba, mun sha fama da ita kafin ta bi layi mutumin farko da ta fara mu'amala da shi babban

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});