Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 35

Chapter 35

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya sa shi akan harshensa". "Sanin daga gidan da ya fito ne ya sa zan yi masa wainar fulawa, don ina da yaƙinin wannan dankali da shayin da kika yi abubuwa ne da kullum yake gani kuma yake cinsu. Amma ina da yaƙinin wannan wainar fulawan zai zama sabon abu a wajensa". Kafin na gama kammala zancen kawai na ga ta ɗaga hannu za ta zabga mini mari na yi hanzarin riƙe hannunta tare da jefa idanuna a cikin na ta. "Kar ki kuskura ki yi gangancin ɗaura hannunki a jikna da sunan mari. Don abin da zai bi yo bayan hakan daga ni har ke ba zai mana daɗi ba". Kafin ta ce wani abu Hajiya Muhibbat ta shigo cikin kicin ɗin ta iske mu a haka. "Me yake faruwa na gan ku kun tsaya cirko-cirko?". "Babu komai Hajiya, da inna fere dankalin nan ne na kuskure hannuna shi ne take so ta ɗauke min wajen". Altine ta kora mata bayanin da ta ƙirƙire shi a take a wajen, ban ce da ita komai hasalima ko hannun ta ban yi ba. "To Allah ya kiyaye gaba. Wannan fulawar fa?". Na yi caraf na amshe zancen kamar ji nake yi ta ce kule na ce cas. "Hajiya wainar fulawa ne zan soya wa baƙo?". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"watau a baƙo kawai ban da mu ƴan gidan ko Amatu?". Na murmusa kafin na ce" har da kowa da kowa ma ranki ya daɗe. Amma Anty Altine ta riƙa da ta shirya abin karin kumallo shi yasa na taƙaita wainar fulawan ga baƙon kawai". "Ai kuwa ni ma dai ina ga wainar fulawan nan zan ci, don dankalin nan gabaɗaya ya gama fita daga kaina zan dai sha shayin. Amma fa sai ki hanzarta don sun kusa fitowa kuma fita za su yi". Cike da jin daɗin kalamanta na ce"in sha Allah Hajiya ba zan ɓa ta lokaci ba". Murmushi kawai ta sakar mini ta juya ta bar cikin kicin ɗin, ko ido ban ɗaga na ga Altine ba balle na tanka mata sai dai ina jiyo sautin ƙwafan da ta dunga sake wa wani na bin bayan wani na tsawon mintuna. Har na yi ƙare suyar wainar fulawan ba ta ce da ni da komai ba. Na ɗauko hula na zuba a ciki, can na hango cabbage na ɗauko na yanka na wanke na zuba a gefen a wani plate na rufe shi. Na waiga na kalle ta. "Ranki ya daɗe na gama sai kuma me ye ya rage?". Ban yi mamaki ko na haɗu ba da na ga ta gallo mini wata uwar harara kafin ta ce"a tambayi kaza hanyar zuwa tafi?". "Tabbas kam ba za a tambaye ta tun da ba zuwa take yi ba" Daga haka ban ƙara ce mata komai na ɗauko tray na jere su a kai na fita ina jin tsakin da take dokawa yayin da nake ƙoƙarin ficewa daga cikin kicin ɗin. Ban iske kowa a falon ba sai ƙarar iskan AC da yake aiki a cikin falon na jere su akan dinning table, Ina tsaye a wajen Aryan da Ayan sun rugo a guje suka shigo cikin falon suka nufo inda nake tsaye. "Wai in ji Uncle Saif an gama abinci? Za su fita da abokinsa". Kafin na yi magana Hajiya ta sauƙo ta karɓe zancen"babu inda za a kai musu abinci idan ba za su zo nan su ci ba, sai dai su haƙura". Tana ƙare zancen ta ɗaga waya ta ƙira shi ina jin ta abin da take faɗi cikin tsare gida babu alamar wasa a tattare da ita. "Ku shigo an kammala abincin". Tana gama faɗin haka ta katse wayar ta ƙariso ta zauna, ban bar cikin falon ba ya shigo take na ji ƙirjina ya buga da ƙarfi ta gabana ya zo ya wuce na gaishe shi ya yi banza da ni wanda kuma ina da tabbacin ya ji gaisuwar da na yi masa sarai. "Hajiya Antynmu tun ɗazu fa abincin nan muke jira, idan ba za a ba mu ba ne sai a gaya mana mu san inda dare ya yi mana". Ya ƙare zancen cikin sigar zolaya yana ɗan sosa ƙeyarsa. "Ina shi baƙon nakan?" "Yana can sashina". "To sai ku fito ku zo mu ci abincin". "Hajiya Anty kin san Taufik fa da kunya ba zai taɓa iya nan gabanki ya sha ko da ruwa ne ba balle har ya saki jiki ya ci abinci". Ta harare shi"mace ne ƙarshen kunya kenan ai ko?". Ya marairaice murya"mu dai yanzu Anty ki yi haƙuri a ba mu abincin. Kin san fa an ce koro da yunwa ba shi da kyau kuma ba shi da daɗi". Dariya ta tuntsire da shi kafin ta waigo tana kallona da har yanzu ina tsaya a inda nake ban motsa ba. "Amatullahi ɗauki girkin kika jera ki kai musu. Ayan zai biyo ki da flask din tea ɗin". "To ranki ya daɗe". Na amsa da shi a taƙaice na ƙara jere su akan tray ɗin na fita na nufi sashinsa, ina jin ƙirjina yana tsananta bugu da ƙarfi da ƙarfi. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na sanya ƙafata a cikin falon na yi hamdala sa boda iske falon da na yi babu kowa a cikinsa sai sautin karatun Alqur'anin da aka kunna yana tashi. Na ajiye tray ɗin akan table na juya da sauri xan fita na ji an tsayar da ni ta hanyar faɗin"baiwar Allah tsaya mana". Take jikina ya soma rawa mussamman da na ji sautin takunsa yana ƙara nufo inda nake tsaye, ban yi ƙasa a gwiwa ba na yi saurin ci gaba da tafiya sai dai ban yi taku huɗu masu kyau ba. Aka buɗo ƙofar falon Saif da su Ayan suka shigo yana riƙe da flask ɗin tea, Ayan yana riƙe da sacet ɗin madara da milo yayin da Aryan ya riƙo kofuna. Sanƙarewa na yi a inda nake tsaye, tabbas wannan shi ne gaba kura baya ƙura, na rasa inda zan yi gaba ko gaba. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________________ Page 5️⃣8️⃣ Ina ɗago kai idanuna suka sauƙa a cikin na Saif kallon da ya watsa mini ya sanya jikina yin la'asar tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Ƙirjina yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi na rusunar da idanuna ƙasa yayin da Aryan da Ayan suka ƙarisa shigowa cikin falon suka je suka ajiye abin da yake hannunsa akan teburin. "Za ki iya tafiya tun da kin gama abin da ya kawo ki ko". Ya yi zancen cikin tsare gida fuskarsa babu alamar wasa balle ya ɗauki wargi. "To ranka ya daɗe". Na yi zancen ina ɗaukar hanyar fita daga cikin falon cikin matuƙar sauti tamkar zan tashi sama, har na kai ƙofar fita na ji an dakatar da ni. "Wace ce wannan ɗin Saif? Ban san ta ba tun da nake zuwa cikin gidan nan". "Baƙuwa ce". Ya ba shi amsa a taƙaice da hakan ya ba n damar ficewa da sauri ban sarara ba har sai da na zo ƙofan falon sashin Hajiya Muhibbat na tsaya ina mayar da numfashi tare da daidaita nutsuwata kana na shiga ciki,

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});