Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ni da aiki sai hidimarsu". Na yi mutuwar tsaye ina bin ta da kallo ganin yadda ta zage tana zazzago masifar babu kwama balle fulsutop. Cike da maɗaukakin mamaki na ce"amma na yi tunanin ai an ɗauke ni saboda hidimansu. To me ye ba za ki yi aikin da ya kallafa akanki ba ko don ki ci halaliyarki?". Ta riƙe ƙugu tana kallona"madalla tun da har kin fahimci cewa an ɗauke ni domin na yi musu hidima, to na haɗa ki da girman mai yi mana ruwa da ƙanƙara ki bar ni na yi aikina kar ki yi min shishshigi akan lamarin da bai shafe ki ba. Ki yi aikinki ni ma na yi nawa don haka ki fita daga ɗakin nan". Ban kuma cewa da ita komai ba na fita daga ɗakin cikin tsananin mamakin da ya bayyana har a kan fuskata ina fitowa na ga har sun yi bacci akan kujerar sun manne da junansu. Na bi su da kallo cike da mamakin abin da Altine ta aikata gare su. Na koma gefe na zauna a inda na yi salla na kifa kaina akan gwiwana ban yi aune ba ni ma bacci ya kwashe ni don daren jiya ban samu na yi bacci mai kyau ba. Ƙiran sallan asr shi ya tilasta mini tashi na ina karanto sunanyen mahaliccina tsarkaka guda ɗari babu ɗaya, na fita na je na yi alwala na zo na yi zama, tun ina sallan nake jin cikina yana kukan yunwa har na iddar na shafa addu'ar da na yi. Na kafe yaran da ido ina ta kallonsu tun ranar farko da na fara tozali da yaran na ji sun shiga raina can ƙololowa, mussamman yadda na ga suna da nutsuwa sosai kamar ba yara ba sannan ba su ƙiriniya ko kaɗan. Ban ji sallamarsa sai gani na yi ya zauna kusa da yaran yana shafa kansu, na yi saurin gyara zamana rare da ɗaukan ɗan kwalina na ɗaura a kaina. Na rusuna ina faɗin"sannu da dawowa ranka ya daɗe". Bai amsa mini ba ya ci gaba da shafa kan yaran ya kai hannunsa wuyan Ayan babu shiri ya waigo yana kallona haɗe da faɗin"me ya same shi na ji jikinsa da zafi gau haka?". Na yi ƙasa da idanuna na rasa me ye zan ce da shi sai kame-kame nake yi, kafin na kai da cewa wani abun Altine ta fito fuskarta kamar gonar auduga bakinta har kunne ta zo ta zube a gabansa"Barka da dawowa Alhaji ƙarami sannunka da shigowa". Bai amsa ba ta ya jefa mata makamamcin tambayar da ya yi mini. "Me ya sa Ayan na ji jikinsa da zafi haka gau, kuma jikinsa babu riga?". Ta ɗago kai muka haɗa ido da ita ta yi hanzarin kawar da nata tana faɗin"sun yi wasa a baya ne wajen bayin shuke-shuke shi ne ya jiƙa rigar, na cire masa na shiga domin ɗauka masa wani kuma sai na fito na tarar ya yi bacci. Ni kuma ban son tashin su shi yasa ban ɗaga sa ba". Ya cije leɓansa"sun ci abinci sun yi salla?". "Duk biyun sun yi kafin su kwanta wannan bacci da ka shigo ta tarar da su suna yi". Ya jinjina kansa yana miƙe wa tsaye"ki tada su ki yi musu wanka ki shirya su za mu fita tare". Yana dire zancen ya bi wata ƙofa ya bar cikin falon. Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina duban Altine da take tayar da yaran ta riƙe hannunsu suka shige cikin ɗakinsu, na koma inda na taso na zauna gabaɗaya yunwa ta addabe ni, ina zaune a wajen ya fito ya sake shiga cikin wani farin sol ɗin yari haka nan ya bar kansa ba tare da ya saka hula ba amma da dukkan alamu ya gyara gashin don har wani ƙyali da sheƙi yake yi. Sai baza ƙamshi yake yi kamar wanda aka yi ɓari durom ɗin turare a jikinsa. Ya nema waje ya zauna yana murza zoben da yake hannunsa ya ce"me ye sunanki?". A nutse na furta"sunana Amatullah". "A ina kike da zama sannan su waye iyayenki?". "Mahaifina ya rasu mahaifiyata kuma ba na tare da ita yanzu, hasalima ni kaɗai nake zaune a garin nan". Ya ɗago ido yana duba na"faɗaɗa min bayanin ban ga ne ba". Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa kana na ce"ina zaman kaina ne bisa wasu dalili da suka tirsasa faruwan hakan". "Mace mai zaman kanta, karuwa kenan ko kuma magajiya?". Da hanzari na ɗago ido ina kallonsa wanda shi ɗin ma ni yake kallo a ci gaba da maganan. "Idan na faɗa ba daidai ba sai ki gyara min". Na girgiza kaina"haka ne yadda ka faɗa". Fitowar Aryan da Ayan shi ya hana sa furzo da zancen da ya yi niyya ya tashi tsaye ya je ya riƙo hannunsu suka fita, Altine sai washe baki take yi tana ɗaga musu da faɗin su kawo mata tsaraba. Ta wuce ta shige ciki ta bar ni a wajen, baƙin cikin kalaman da ya watsa mini ya sanya har sai da na zubar da hawaye, na ji duk son da nake ji wa wannan aikin da zumuɗin da na yi a lokacin da na yi katari da samun aikin duk ya fita daga raina. Tabbas ina son wannan aikin sai dai ba zan juri wulaƙanci wannan mutumin da kuma cin zarafin Altine a gare ni ba. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 4️⃣9️⃣ Rawan da ƙafafuna suka soma yi shi ya tilasta mini zama dirshan irin na ƴan bori, ina jin ƙirjina yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi. Ji na yi kamar na tashi na ruga da gudu na fice daga cikin gidan, tabbas na shiryawa dukkan ƙabuluaben da zai biyo bayan samun wannan aikin sai dai ban taɓa zaton zai zo mini a ranar farko ba. Yunwan da ta ci gaba da ƙwaƙwulan ƴaƴan hancin cikina har ina jin mayar ana musayar kifiyoyi a cikin cikina. Ba tare da na yi shawara da zuciyata ba na tashi da nufin tafiya don har cikin raina na ji cewar ba zan iya juran wannan cin mutuncin da tozarcin ba, ina fitowa harabar gidan na ga an wangale gate ɗin mota tana shigowa, na tsaye a inda nake har ta daidaita parking ta fito ta iso inda nake. "Ya na ganki a nan?". "Ranki ya daɗe zan tafi ne na ga yamma ta na ta gabatowa". "A'a wani yamma ne ta yi yanzun dududu ma ƙarfe nawa ne? Mu koma ciki". Daga haka ta yi gaba ba tare da ta tsaya sauraron jin abin da zan faɗa ba, ba ni da wani zaɓi da ya wuce na bi ta kamar yadda ta buƙata, don haka na bi ta a baya a har cikin falon gyalen kanta ta yaye yayin da take zama akan kujera tana mayar da numfashi. "Ki zauna mana". Amon sautinta da ya sauƙa a masarrafar jina ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina, na zauna a ƙasa a hankali na furta"sannu da dawowa ranki ya daɗe". Cike da kulawa ta amsa mini da faɗin"yauwa Amatullah sannu ko? Ya na ji gidan shuru kaman ƴaƴan ba sa nan". Kafin na kai ga ba ta amsa na

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});