Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ƙyar". "To Allah dai ya sa kin yi salla?". Ta taɓe baki"so nake yi yanzu idan na yi wanka, inna ci abinci sai na samu na yi sallan. Don ina jin sallan daren jiya ma ban yi ta ba na ɓige da yin waya". "Sallan kike haɗa wa a kanki haka?". "To ya ya zan yi Amatullah ayyuka su yi min yawa, dole wani abun sai ana ajiye shi a gefe idan aka sama sarari sai a ɗago shi". Shuru na yi don mamaki da al'ajabi ya hana ni furta ko da kalma guda, sai da na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kana na sama lasisin faɗin"ya dai kamata kam ki samu ki yi sallan, ni na fita wajen aiki". "In kin dawo za mu yi magana". Ta murmusa"akwai zancen bakinki na ga alama sai na dawo ɗin dai kawai sai mu tattaunawa". Dariya ta fashe da shi har ta tafa hannu, ban tsaya jiran abin da za ta faɗa ba na fice don ko ban tambaya ba na san cewa na makara. Gudu-gudu sauri-sauri nake tafiyar ƙafafuna har suna sarƙewa tsabar sautin da nake zuba wa tamkar za tashi sama, kamar daga sama na ji an danna mini horn lamarin da ya yi matuƙar gigita ni. Na ɗaura hannuna aka tare da runtse idanuna ina jiran na ji ta inda motar za ta doke ni da yadda Allah zai yi da ni. Ji na yi motar ba ta dake ni ba hakan ya ba ni ƙwarin gwiwan buɗe idanuna don ganin abin da yake wakana, take idanuna suka sauƙa akan fuskar Saif da yake tsaye a gabana ya zube dukkan hannayensa a cikin aljihun wandon suit ɗin da yake jikinsa, idanunmu suka sarƙafe cikin na juna na tsawon wasu daƙiƙu kafin na yi ƙarfin halin janye nawa gefe guda. "Amatullah ko?". Na gyaɗa masa kaina da hakan ya ba shi damar ci gaba da maganar da yake kamar an yi masa dole ko kuma mai ciwon baki. "Da kin daina wahalar da kanki ki na yin sammakon zuwa wajen aikin da ba zai amfane ki da komai ba, da zan ba ki shawara ki ɗaura da na ce da ke tun wuri da kin ɗauke ƙafarki daga cikin wannan gidan". Na cira kaina ina kallonsa sai dai kwarjininsa da cika ido ya hana ni ba ni damar yi masa dogon kallo. "Me ye yake nufi da waɗannan maganganun nakan?". "Ina nufin ba za ki taɓa samun gurbi a cikin zuciyoyin mutanen da suke rayuwa a cikin wannan gidan nan, ba ki da tarbiyya da nagartar da ya dace ki kasance a kusa da mu kasancewarki mai zaman kanta kuma a cikin gidan magajiya cikin tsakiyar karuwai da ƴan daudu. Da babu abin da suka sanya a gabansu face saɓon Allah da kaucewa koyar wa Annabinsa". Hawaye suka ciko mini kurmin idanuna sa boda zafin kalamansa da na ji, kaina na ƙasa da hakan ya ba wa hawayen damar kwaranya na kuma gaza samun ikon tsayar da su. "Amma ka san cewar ko wani bawa da irin na shi salon ƙaddarar da Ubangiji yake ƙaddara masa ko....?". Tun kafin na gama zancen ya ɗaga mini hannu alamar ba ya ƙaunar sauraron raguwar zantukan nawan. "Allah ba ya taɓa ɗaura wa Bawa abin da ba zai iya ba. Kuma duk wani abin alkhairin da kika ga ya sama Bawa to daga Allah ne akasin hakan kuma daga mu ƴan adam ne". Jinjina kaina na yi ina haɗiya kukan da yake ƙoƙarin kufce mini, na kai hannu na kawar da hawayen da suka ɓata mini fuskana kana na furta"duk kalamanka babu kuskure a cikinsu, amma ka roƙi Allah kar ya jarabce ka da abin da ba za ka iya ba kuma ba ka taɓa tsammanin tsintar kanka a cikin irin rayuwar ba". Ina dasa aya a nan na juya na bar shi tsaye a wajen, na karya kwanar da za ta sada ni da gidan. Baba Mai gadi na iske zaune a bakin gare ɗin na durƙusa har ƙasa na gaishe shi ya amsa mini cike da kulawa, ban bari mun yi wani dogon zance da shi ba na tashi na shiga cikin gidan. Babu kowa a falon don hakan kaina tsaye na wuce ɗakin Altine na shiga cikin banɗaki na kulle kaina na jingina jikin ƙofar banɗakin yayin da wasu hawaye masu ɗumi suke gudun famfalaƙi a bisa kuncina suna zarce wa har izuwa saman haɓata. Tabbas juyi-juyi ce in ji kwaɗo ya ce wash! Da ya tsinci kansa tsumgum a cikin ruwan zafi. Haƙiƙa ta kan zo a ko wacce irin siga ba tare da ta yi raunin mutumin da za ta faɗa kansa ba. A zamanin baya idan wani ya kalle ni ya ce wannan yarinyar za ta iya sanya ƙafa ta bar cikin gidan mahaifinta ta shiga duniya ta yi zaman kanta, ilahirin mutanen da suka sanni kuma su ka san wace ce ni, sai sun yi haɗaka sun yi taron dangi sun ƙaryata abin da ya furta cikin babbar murya. Sai ga shi ƙaddara ta jefo ni cikin duniyar da babu kulawar uwa balle uba, babu mai tsawartawa balle ƙwaba, babu mai hana ki balle ya saka ki duk abin da kika ga damar aikatawa shi za ki yi babu mai tambayarki dalili balle har ki sama tagomashin shawara. Babu tswatarwa iyaye balle dangi babu mai tanƙwara ka balle ya tursasa ka ka yi abin da ba kya yi niyya ba. Ko a cikin mungayen mafarkan da na yi sheiɗan bai taɓa kimtsa mini cewar wata rana zan yi zaman kaina ba, balle har na kwana na tashi a cikin gidan karuwa. Zazzafan iska mai ɗumi na fesar daga bakina ina sulale ƙasa na yi zaman dirsham ina wani irin kuka mai rauna zuciyar mai saurare. Haƙiƙa sai yanzu na ƙara yarda cewar babu abin da ya kai mutuwa tonon silili da ban kaɗo rufaffun sirrukanta ta sanya a faifayi ta raba a duniya. Ina da yaƙinin da Abbana yana raye a cikin wannan duniyar da ban tsinci kaina a cikin wannan rayuwar ba, ko da kuwa ƙaddara ta jawo ni to tabbas ba zan yi nisan zango a cikinsa ba. Tun ina kukan hawaye suna zuba har sai na na koma yin kukan zuci sa boda hawayen sun tsaya sun kafe tamkar rijiyar da ruwan cikinta ya kafe na tsawon shekaru masu nisan zango. Jin da na ji ana ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin shi ya fargar da ni na dawo cikin hayyacina daga na tunanin da na yi nitso a cikinsa. Da ƙyar na iya miƙewa akan ƙafafuna sa boda ciwon kan da lokaci guda ya rufe har ya sauƙar da mini da zazzaɓi mai zafi a cikin jikina. Sai da na wanke fuskana kafin na buɗe ƙofar muka haɗa ido da Altine na yi saurin kasar da nawa idon daga gare ta ina ƙoƙarin fitowa daga cikin banɗakin na ce"ina kwananmu mun tashi lafiya?". Ban damu da sai ta amsa mini ba na sa kai zan yi wuce ta ta jawo ni na koma da baya. "Me ye kika aikatawa a cikin banɗakin da kika shiga kika ƙulle ƙofa?". "Har abun da na aikata a cikin banɗakin ma zai na sanar da ke ranki ya daɗe?". Ban

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});