Chapter 49
Chapter 49
kuma ta ba da gagarumar gudummawa wajen tabbatar da numfashin da kake yi yanzu a cikin duniya, ka gode mata don ta cancanci hakan sosai". Kit! Saif ya datse ƙiran ba tare ya ba wa Sultani damar amayar da sauran zancen da suke cikin bakisa ba. Ya zame daga zaunen da yake ya kwanta akan bayansa yana jan bargon ya lulluɓe rabin jikinsa, numfashi mai zafi ya furta daga bakinsa yana ɗan lumshe idanunsa sa boda ciwon kan da yake ji yana damun sa kaɗan kaɗan. Ya daɗe kwance a wajen yana saƙa da warwara cikin ransa kafin ya tashi ya haura sama zuwa cikin ɗakinsa, wanka ya yi ya ɗauro alwala ya fito ya sanya farar doguwar jallabiya da aka yi wa ado da zare launin ruwan zuma mai ƙyalli da ɗaukar ido, ƙaramar hula ya sanya a kansa ya shimfiɗa sallaya ya gabatar da sallan zuhur tare na sallan asr yana iddarwa ya ɗauko alƙur'ani ya soma karantawa. Dole ne ya tursasa masa rufe alƙur'anin ya ajiye a gefe sa boda rawar da jikinsa yake yi tamkar mazari. Ya kunna ƙira'an Sheikh Ahmad Suleiman a cikin wayarsa ya ajiye, a nan kan sallayan ya kwanta take wani bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da shi ba tare da ya shirya wa hakan ba. Tun da na fito daga sashinsa na nufi hanyar gate ina tafiya a hankali tamkar babu laka a jikina, ina dab da fita na tsinkayo muryar Baba Mai gadi. "Ƴar nan lafiya kuwa na ga kamar kuka kike yi?". Na yi saurin goge fuskana da ban san lokacin da wasu sabbin hawayen suka fito ba, na waigo tare da duƙawa na gaishe shi, ya amsa yana bi na da kallon tuhumar son gano abin da yake faruwa da ni. Ya zauna akan bencin da yake wajen ni ma na je na zauna. "Ko dai cikin gidan ne babu lafiya? Don ɗazu na ga Saifullahi ya fito daga cikin gidan ya nufi sashinsa cikin wani irin yanayi, wanda har ina tsoron har hakan ya tasar masa da ciwon da yake damunsa". Na sauri na ce"wani irin ciwo ke nan Baba?". Ya yi ɗan jim kafin can ya ce"tun yana ƙarami yake fama da wani irin ciwo ga shi nan dai kamar aikin aljanu ko iskokai. A duk lokacin da ransa ya ɓaci ko kuma ya yi cacar baki da wani ke wani lokacin ma ko dogon zancen ya yi sai ki ga kawai ya yanke jiki ya faɗi jikinsa ya sanƙare haka zai koma ba shi da maraba da gawar da rai ya yi bankwana da gangar jikinsa, sai ta yi masa karatun alƙur'ani kafin yake dawowa daidai kuma da zaran ya tashi zai koma kamar ba shi ba". Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe ina jin ƙaran da ƙirjina yake yi tamkar zai faso allon ƙirjin ya fito waje ya taka rawar disko. Sai da na harhaɗo kalaman kafin na yi nasarar cewa"Allah ya na shi lafiya, Baba bari na je gida na dawo". "Amin ya Allah, to ƴar nan a gaishe da mutanan gidan". "Za su ji in sha Allah". Na amsa da shi yayin da nake tashi daga kan bencin, tafiya kawai nake yi ba tare da na san inda nake cilla ƙafafuna ba ina tafe ina tunani tare da nazarin kalaman Baba mai gadi. Saura ƙiris wani mai napep ya kwashe ni Allah a rufa asiri, ai kuwa ya fito ya balbale ni da bala'i da masifa tamkar zai yi aron baki da ƙyar ya haƙura ya ja napep ɗinsa ya tafi bayan ya gama wurwurga mini ashariya tamkar ya hana jini da dangin maguzawa. Sai yamma lilis na iso gida lokacin ko wacce budurwar dake cikin gidan ta ci ƙwaras tana ƙoƙarin fice wa wajen harkanta. Gidan ya yi shuru sosai ina shigowa na kai duba na ƙofar ɗakin Hajiya Babba na ga ƙofar ɗakin a rufe an buga masa kwaɗo. Na lura cikin kwanakin nan ba na ganin La'aniyatu a cikin gidan nan kuma na rasa wanda zan tambaya. Har na ɗauki hanyar ɗakinmu sai kuma na fasa don har cikin raina ba na ƙaunar haɗa ido da Sha'awanatu don har yanzu ban huce daga abin da ya faru ba. Ganin ƙofar ɗakin Zinariya a buɗe ya ba ni ƙwarin gwiwar faɗa wa cikin ɗakin. Na iske ta tana kwance akan katifarta tana bacci na zauna a gefen tana dukan ƙafarta har sai da ta shi, ganin ni ce ya hana ta ƙarisa ashariyar da ta danno. "Au wai ke ce?". "Da waye kike yi tunani?". Ba ta amsa mini ba har sai da ta tashi ta zauna ta ce"kin dawo daga aikin wahalar ke nan?". Na yi murmushi har sai da haƙwarana suka bayyana"aikin rufa wa kai asiri dai ko?". Ta taɓe baki ba tare da ta ce da ni ko kanzil ba sai ma sauya akalar zancen da ta yi "Ki na da lokaci ki raka ni kasuwa?". "Duk a cikin shirin tarban Yallaɓai ɗin ne?". Ta yi fari da idonta"ƙwarai kuwa". Na gyaɗa kaina"Allah ya bar ƙauna Madam ta gaban goshin Saddam". Caraf bakina ya yi furucin ba tare ta yi shawari da zuciyata ba. "Saddam kuma? Ina kika san sunansa?". Cike da dabara na wayince"kar ki daina basirar duk wata macen da kika ga ni a cikin harkan bariki". [12/9, 6:43 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________________ Page 6️⃣5️⃣ Tun da na yi zancen take bi na da kallo da mamakin zancen ya tilasta mata wartsakewa daga baccin da take yi. Ta rarumo hannuna ta riƙe gam"sanar da ni inda kika san sunansa don Allah". Na saki wani shu'umin murmushin gefen baki kafin na furta"ki fa kwantar da hankalinki na canza ne kawai. Sai kuma aka yi dace sunan ya zo daidai". Ta yi jim tana ta bi na da kallo kafin can ta ce"kin tabbata?". Na yi fari da idona kafin na amsa mata da faɗin"ki yarda da ni wallahi ki ji rantsuwar ɗan musulmi ke nan ko? Ban taɓa ganin sa to ina ma za mu haɗu da shi mutumin da kika ce ba ya cikin ƙasar nan". Da alama ta sama nutsuwa da kalaman da na furzar don ina jin sautin sauƙar numfashin da ta sauƙe. "Na yarda da ke". "To ba ta labarin abin da ake shiryawa yallaɓai ɗin namun?". Washe baki ta yi tamkar gonar auduga don na ga alamar tamkar babu maganar da yake sanya ta cikin tsananin farin ciki kamar batun Saddan da ta yi masa laƙabi da Oganta. "So nake yi na je na sayo abubuwan gyaran jiki da kayan ƙamshi. Don so nake yi na shirya kaina kafin mu haɗu da shi, ina so wannan haɗuwar tamun ta zama abar tunawa a gare shi ta yadda ban bar shi masa tabon a cikin kwayansa". Sai da na musguta kafin na ce"irin wannan kulawan da kuke ba wa junanku to me ye zai hana ku auri junanku?". Ta taɓe baki"ai aure lokaci ne kuma ni ban shirya yin aure a wannan shekarun nawan ba. Kin gan ni nan sai na gama cin duniyarta da tsinken sakacen sannan na yi aure, mu yi rayuwar farin ciki da shi mu farantawa juna rai da zaran
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98