Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 52

Chapter 52

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,217 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kala daban-daban suke ziyartar cikin kwanyanta a lokaci guda. Kyakykyawan ajiyar zuciya na sauƙe daidai lokacin da na ji an dafa kafaɗana na waigo a hanzarce don ganin wane ne, idanuna suka sauƙa akan fuskar Zinariya da yake ɗauke da maɗaukakin annuri fuskarta tamkar gonar auguda yayin da bakinta ya kai har kunne. "Kin dawo ke nan?". A jefa mata tambayar yayin da take haye wa kan tabarman ta zauna tana fuskan ta na. "Wai akan wannan abun kike kwana? Lalle ki na ƙoƙari kuma ki na rayuwar ƙunci. Wannan tabarman ai ba shi da maraba da kwanciyar ƙasa". Taƙaitaccen murmushi na yi kafin na ce"yaushe kika dawo? Akwai matsala fa". "Ƙarfe uku da wasu mintuna na shigo cikin gidan nan, na so na buga muku ƙofa ma sai kuma na fasa haka na yi kwanan farin ciki ina jin kamar garin Allah ba zai waye ba". "Me ya faru haka na farin ciki?". Ta ajiye mini wasu takardu akan cinyata kafin ta ce"kin ga wannan takardun da kike gani takardun tanƙamemen gida ne na beni a can cikin birnin tarayya". Na waro idanuna cike da mamaki ina juya takardar. "Ke kuwa waye ya ba ki wannan kyautar?". Ta yi fari da idanunta wanda izuwa yanzu na fahimci kamar hakan ɗabi'arta ne musamman a lokacin da take cikin farin ciki. "Fitan da na yi daren jiya ne aka ba ni shi kyauta, ko kuma na ce miki aka mallaka mini shi halak malak, na tabbatar yau wasu za su yi kwanan baƙin ciki a cikin gidan nan kuma da yardan Allah wannan shekarar ni ce wacce za ta lashe gasar zakaran gwajin dafin da Hajiya Babba take shiryawa a duk ƙarshen shekara". "Wacce gasa ke nan kike magana a kai?". "Wata gasa ce da Hajiya take shiryawa duk ƙarshen shekara, a cire wacce ta fi samun kyaututtuka, mu'amala da manyan mutane da kuma samun alkhairai. Wacce ta ciri tuta ita ce gwarzuwan wannan shekarar". Taɓe bakina na yi don wannan ba shi ba ne a gabana, wutar gabana ma kaɗai ta ishe ni ba sai na ƙara wa kaina wani nauyi da damuwar damuwa da waɗanda ba su san ina yi domin su ba. "Jiya Hajiya ta ƙira ta yi buƙac ta ji yanda ake ciki, na roƙe ta ta ba ni lokacin inda a ƙarshe ta ba ni watanni uku rak. Idan har wa'adin wannan lokacin ya cika ba tare da na cika alwashin da na yi to sai duk abin da ya faru ni na jaza wa kaina. Tun da daman an ce duk abin da ya sama shamuwa ta zargi watan bakwai". Ta ɗan yi jim alamar zantukan nawan ita ma ya caja mata kanta. Na riƙo hannunta na sanya cikin nawa kafin na ci gaba da cewa"yanzu ya ya kike ga za a yi?". "Gabaɗaya kaina ya kulle ban san abin da ya dace mu yi yanzu ba, amma ba ri na ƙira wanda na miki na sani a otel ɗin". "Yauwa don Allah ƙira shi mu yi". Ta ɗaga wayarta ta lallatsa kafin ta kara a kunnenta. "Mai gida kana wajen aiki ne?". Ban san wani amsa ya na ta ba na ji ta kuma ce wa"zan zo na same ke". Daga haka ta zare wayar daga kunnenta. "Tashi ku je?". "Ina za mu je?". "A gabanki fa na yi waya yanzu, otel ɗin za mu je mu same shi don ya fahimci mun ɗauki abin da muhimmanci sosai". Ta furzar da zazzafan iska daga bakina kana na ce"otel dai? Ki rufa mini asiri tun da uwata ta haife ni ban taɓa zuwa ko da cikin harabar otel ba kai ko wucewa ta gate din ban taɓa yi ba, balle har na shiga cikinsa". "Ke dalla! Ki kwantat da hankali mene ne a cikin zuwa otel ɗin?. Ke dai kawai ki tashi mu je ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba". Ta ƙare zancen tana riƙo hannuna maimakon na tashi sai na turje"kin san fa zan je wajen aiki". Ta galla mini wani uban harara tamkar idanunta za su faɗo ƙasa"idan ba za ki je ba ne ki fito fili ki faɗa min, ba sai kin tsaya ki na ta wani kewaye-kewaye ba Amatullah". Na ɗan yi shuru na wasu mintuna kafin na furta"shi kenan mu je mu amma don Allah kar mu daɗe". Ba amsa mini ba ta yi gaba ina bin ta a baya har muka fice daga cikin ɗakin. Muka fito bakin hanya ta tara mana abin hawa muka hau, tun da muka soma tafiyar ƙirjina yake bugawa da ƙarfi da ƙarfi ban sama sauƙi ba har sai da na ji an taka birki hakan ya ba ni damar cira kaina ina ƙarewa inda muka zo kallo. Sunan otel ɗin na karanta da aka rubuta da manyan baƙi, yana walƙiya da sauya kaloli daga shuɗi zuwa ruwan hoda. "Sarauta hotel". "Tabbas Saraute hotel ke nan fito mu je". Furucin Zinariya ke nan da ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na afka, sai da na dogon numfashi na fesar kafin na sama damar saƙalo ƙafafuna waje daga cikin napep ɗin kafin na fito da ragowar sauran gangar jikina. Na ƙare wa wajen kallo ganin yadda mutane suke ta hada-hada cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, maza da mata a cunkushe a waje guda manyan motoci ne suke da shige da fice a waje tamkar ana wani gagarumin taro. Duniya-duniya inji kwaɗo da ya ji shi a cikin ruwan zafi, tabbas Ubangiji shi kaɗai ya bar wa kansa ilmin sanin abin da gobe za ta iya haifar wa. Yau wai ni ce a cikin otel inda duk nake ban ta ko fa mafarki zuwa ba sai ga shi yau ƙaddara ta jawo ni idan tunanin bai taɓa tunanin kawo ni ba. Ganin yadda duk na rasa nutsuwata ya sanya Zinariya riƙo hannuna muka soma tafiya muka shiga ciki muka zauna a bisa wasu kujeru da aka tanada a wajen, ta ɗaga waya ta ƙira shi tare da sanar da shi cewar mun iso babu jima wa na hango wani mutum mai jiki ya nufo inda muke fari ne sol sannan yana da saje da kuma ƙasunba a bisa fuskarsa ya yi shigar ƙananan kaya ya sanya hular da ake wa laƙani da p-cap a kansa ya zo inda muke zaune ya zauna kusa da Zinariya, ya miƙa mata hannu suka tafa kafin ya ce"ina jinki don aiki nake yi na baro na zo na saurare abin da yake tafe da ke. Don kawai ke ɗin Zinariya ce". Da alama zantukansa sun yi tasiri a cikin zuciyarta da hakan ya sanya ta darawa sosai, har sai da sautin dariyar ya fita. "Ina miƙo dubun godiya ranka ya daɗe". Ya murmusa kafin ya ce"wannan cikar fa tare kuke da ita?". Ta gyaɗa kanta"e tare muke". Sai da ya musguta kafin ya ce"ina jinki gama maganarki don ni ma ina da nawa maganar da zan yi miki". Babu ɓata lokaci ta kwashe komai ta sanar da shi. "Mun zo ne mu ji idan a cikin kwanakin nan zai zo cikin garin ya sauƙa a otel ɗin. Na san kai kaɗai za ka iya yi min wannan abun

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});