Chapter 37
Chapter 37
yi zaman ƴan bori dirshan a ƙasa ba, na dulmiya cikin kogin tunanin da yake ƙoƙarin hautsina mini dukkan lissafin cikin kwanyata. Me ye haɗin Muhammad Taufik kuma da Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe? Na jefa wa kaina tambayar da take zuciyata ta ba ni amsa da faɗin wataƙila masoyansa ba ina ji a kaf cikin garin nan da kewayanta babu malamin addinin da take da yawan mabiya sama da Sheik Dawood. Na ja dogon numfashi na fesar ina jina gabaɗaya wani iri wacce ba ta da maraba da majinyaciyar da ta yi shekara tana jinya. Na mayar da hoton inda ya faɗo na ajiye takardan. Ban shiga musu cikin ɗakuna ba don ba na son na gane wa idanuna sbun fa bai halalta na gani ba, don na sha jun ana cewa ɗakin mutum sirrinsa ne musamman kuma su da suka kasance jinsin maza biyu kuma a matsayina na mace budurwa. Ina gama wa na fito na koma sashin Hajiya Muhibbat har yanzu tana tare da baƙin suna ta buga lissafi na durƙusa na yi mata sannu tare da sanar da ita cewar na gama aikin. "Ki zauna za mu yi magana idan na sallame su". "To". Na amsa mata da shi a taƙaice. Na zauna har duka gama lissafin suka ƙare na sinci wasu abubuwa a cikin hirarta sun duk da kuwa hirar kasuwanci ne, ƙoƙarin haɗa kayan lefe suke mai rai da motsi na fita kunyar jama'a kamar yanda na ji suna faɗi. Sai da suka gama ta ƙare tas ta sallame su suka tafi kana ta juyo gare ni. "Na bar ki kina ta jira ko? Kin ga kayan lefe ne muke ta ƙoƙarin haɗa wa na ɗaruruwan kuɗaɗe kayan na fita kunya. Don gidan manyan mutane za a kai kayan". Na jinjina kai kafin na furta"ai ku na ƙoƙari ma irin lissafi haka. In wasu ne ai komai sai ya sunce musu". Ta ɗan yi jim kafin ta ce"sai dai ba na son haɗa irin waɗannan kayan na kuɗaɗe masu yawa". Cike da mamaki na ɗago kai ina kallonta kafin na kai ga furta"Hajiya me yasa? Na ga ai ƙaruwarku ne tun da ciniki za a yi muku ko kayan miliyan ɗari za a haɗa ai ribarku ne". Ta sauƙe ajiyan zuciya wanda har sai da na ji sautinsa kafin ta sama lasisin faɗin"mafi yawancin masu haɗa irin wannan lefen na maƙudan kudaɗe bayan auren ba sa iya ba wa mata lokaci balle maganar kulawa. Daga zaran a kai ki ɗakinsa a matsayin mata to ke da ganinsa ma wataƙila sau ɗaya a cikin shekara guda shi ma ɗin sai kin yi sa'a kuma kin dage da addu'a. Amma duk wasu ababen buƙatann rayuwa ba za ki rasa su ba sai dai za ki yi rayuwa ne a zahiri kina raye amma a baɗili ruhinki ya daɗe da barin gangar jikinki". "Duk da hakan kuwa wasu ba su da burin da ya wuce su ha sun auri irin mjini da zai haɗa musu ko da kwatankwacin irin wannan lefen ne". "Ai kuwa kallon kitse suke yi wa rogo, da sun san tashin hankali da rashin samun nutsuwar da yake tattare da auren wani mai kuɗin da sun daɗe da dawowa hanyar gaskiya, sai dai ba dukka aka taru aka zama ɗaya akan sama na gari a cikinsu sai dai ƙalilan. Ni fa yanzu da ace ina da wata ƙanwa mace da ba ta yi aure ba ko kuma Allah ya ba n ƴaƴan mata da ba zan taɓa yi musu sha'awar su auri masu kuɗi ba sai dai masu rufin asiri. Don ina yaƙin sai sun fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa har ma da nutsuwar ruhi da salamar zuci". Ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauƙe kana na ce"Allah dai kawai ya da mu dace". Gabaɗaya jikina ya yi la'asar mussamman yanayin da na ga ta shiga, duk wani wanda zai gan ta a yadda take zai iya rantsuwa da girman zatin Allah cewar ba ta da wani sauran damuwa a cikin gidan duniya, mussamman idan aka yi la'akari da irin suturun da take sanya wa, muhallin da take zaune a cikinsa da kuma motar da take murza wa. "Za ki iya zuwa gida ki dawo idan ki na buƙatar hakan. Tun da na ga yanzu babu wani aiki sai zuws a kuma". Tana gama zancen ta tashi ta hau sama ta bar ni zaune a wajen ina bin ta da kallo. A ƙalla na ɓata mintuna ashirin zaune a wajen kafin na tashi na fita zan je na dawo kamar yadda ta lalince ministan.Tun da na fito idanuna suke kan sashin Saifullah haka kawai wata zuciyar mini na je na dauki hoton da na gani na Muhammad Taufik tare da Sheikh Dawood. Ba tare da na yi wani dogon tunanina na nufi sashin na tura ƙofan falon a hankali na shiga ina waige-waige. Da hanzari na je na buɗe takardan na ɗauko hoton na sama a cikin hijabina na fito na jawo ƙofar, ina fitowa na hango motarsa tana shigowa cikin gidan, na yi mutuwar tsaye a wajen na kasa gaba balle baya har ya gama daidaita parking. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________________ Page 5️⃣9️⃣ Sai da na ja dogon numfashi a fesar daga bakina kafin na iya sarrafa kaina. Har ya fito daga cikin motar na gaza matsawa daga inda nake tsaye tamkar wacce bishiya ko kuma sassaƙen gunkin indiya. Da sauri na ga ya nufo wajen sashinsa da alama wani abun ya mance ya zo ɗauka cikin gaggawa. Sai a lokacin na sama zarafin matsa wa daga wajen na ɓoye a bayan shuke-shuken da aka ƙawata wajen da su. Ina ganin sa ya zo ya wuce ba tare da ya lura da inda nake ba, ba a bi sakon talatin ba na ga ya fito riƙe da wasu takardu a wannan lokacin da ya murzawa ƙofar makulli ya rufe ta kirif kafin ya nufi inda ya ajiye motarsa ya shiga ya fiye da mungun gudu ya fice daga cikin gidan. Fitarsa ta yi daidai da sauƙe tagwayen ajiyan zuciyar da na yi wani yana bin wani tamkar wacce ta yi aikin fasa dutse. Na fito daga inda na ɓoye ina tafiya saɗaf-saɗaf tamkar ƙadangaruwar bayan tulu da hanzarina na nufi hanyar gate na ji an dakatar da ni. "Malama daga ina kike? Me ya kai ki hanyar sashin Saif?". Muryar Altine mai cike da isa gami da taƙama ya sauƙo a ƙofofin kunnuwana. Ban amsa mata ba har ta iso gabana ta tsaya riƙe da ƙugunta tana bi na da kallon tuhuma irin kallon da ma'aikacin ɗan sanda yake yi wa mutumin da aka kama bisa zargin ta'addanci. "Ban yarda da ke ba tabbas akwai abin da kike ɓoye wa. Kuma kawai abin da ya kai ki sashin Saifullah". Sai da na harhaɗo jarumta na yafawa wa kaina kafin na sama zarafin faɗin"Hajiya ce ta ce na je na gyara sashin". "Tun ɗazu kuma gyaran sashin kike yi? Uwar iya magana da iyayi". "Na riga da na faɗa miki iya gaskiyata, ya rage na ki ki yarda da abin da na faɗa ko akasin hakan". Ina dasa aya a zancen na raɓa ta gefenta na yi tafiyata,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98